✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake samun nasarar noman tafarnuwa

Noman tafarnuwa na da matukar tasiri ga manoma, kuma ana iya noma shi a matsakaicin yanayi sannan a waje mai sarari. A nan Najeriya ana…

Noman tafarnuwa na da matukar tasiri ga manoma, kuma ana iya noma shi a matsakaicin yanayi sannan a waje mai sarari. A nan Najeriya ana noma shi ne galibi a wuraren fadamu a lokacin rani, kamar daga Watan Nuwamba har zuwa Maris a daidai lokacin da zafi ya tsagaita.

Kodayake tafarnuwa na bukatar ruwan sama, amma ba da yawa ba, masana sun kiyasta cewa yana bukatar ruwan saman da bai wuce karfin ma’aunin mm 600 zuwa 1, 200mm ba, sannan da kuma mafi karancin zafin rana gwargwadon 5oC zuwa 25oC sannan ya zarce har zuwa mafi zafin 25oC zuwa 40oC.

Ana iya samar da curin tafarnuwar da ta kai nauyin kilo-garam 475 a kowane hecta guda. Haka kuma tafarnuwa na bukatar turbaya ce, ba ta son kasar tabo da kuma kasar dauke da duwatsu. Sannan busasshiyar kasa ta fi dacewa da noman tafarnuwa.

Masana na bada shawarar game da dacewar zuba taki ga noman tafarnuwa don karin samun tagomashin ta yadda ya kamata. Haka kuma noman nata na bukatar yin kaftu da kuma tsara kunyaki kamar sauran shuke-shuke. Bugu da kari kyakkyawan iri na shuka yana taka rawa wajen samun yabanya ko amfani mai yawa.

Haka zalika masana na ganin dacewar jika irin cikin ruwa na tsawon akalla awa shida kafin a kai ga shukawa, domin hakan zai bada damar a yade sosan da ya dabaibaye ’ya’yan tafarnuwan, sannan sai a busar da su da kuma yin feshin maganin kwari duk gabanin a shuka. 

Akwai bukatar manomin tafarnuwa ya san cewa bada ’yar tazara tsakanin shuka da shuka kimanin inci 8 ko kuma santi-mita 200. Kamar kuma yadda ake son shuka irin cikin kasa akalla zurfin santi-mita 3 zuwa 6 sannan a binne.

 

Haka zalika daga lokacin da aka shuka irin tafarnuwa, zai dauki tsawon watanni hudu zuwa biyar ko kuma a lokaci da aka ga ya ganyayen sun koma ruwan dorawa ko ruwan kasa kafin ya kai ga kwarin da ake bukata. Sannan akwai bukatar kulawa wajen ciran tafarnuwa bayan kosawarsa don gudun lalata ’ya’yan da aka samun.