✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake tururuwa zuwa gidan Abba Kyari a Maiduguri

Daruruwan jama’a ne ke ta zuwa gidan Malam Abba Kyari, Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Kasa da ya riga mu gidan gaskiya, domin mika sakon…

Daruruwan jama’a ne ke ta zuwa gidan Malam Abba Kyari, Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Kasa da ya riga mu gidan gaskiya, domin mika sakon ta’aziya game da rasuwarsa.

Da wakilin Aminiya ya kai ziyara gidan wanda ke Unguwar GRA a birnin Maiduguri, ya ga yadda ake ci gaba da karbar baki masu zuwa don yin ta’aziya ga ’yan uwansa.

Dr Babakura Kaigama, wanda aboki ne na kusa ga marigayin ya bayyana kaduwarsa da jin labarin rasuwar amma, a cewarsa “ba mu da wani abin yi – haka Allah Ya so, domin duk mai rai mamaci ne” .

Kaigama ya kuma ce hakika Malam Abba Kyari mutum ne mai gaskiya, wanda rashinsa ba karamin gibi ya bari ba wanda cike shi zai yi wahala.

Shi kuwa Chiroma Abba, wanda ya bayyana marigayi Abba Kyari a matsayin yayansa, cewa ya yi marigayin “mutum ne mai gaskiya da rikon amana, wanda mutane da dama ba su fahimce shi ba”.

Ya kuma ce hakika jihar Borno da ma Najeriya an yi babban rashi.

Sakataren Kungiyar Dattawan Borno, Bulama Mali Gubio, bayyana marigayi Abba Kyari ya yi da hazikin mutum mai dattako da sanin ya kamata.

“Wadannan abubuwa ne ma da Buhari ya gani tare da shi suka sa ya nada shi a matsayin Shugaban Ma’aikata a Fadarsa”, inji sakataren na dattawan Borno.

Ya kara da cewa marigayin “mutum ne kaifi daya, kuma ba shi da munafunci, mun tashi tare duk da dai ya girme mu. Abba ba ya fadar abin da ba haka ba, gaskiya an yi babban rashi, sai dai muna fatan Allah ya karbi shahadarsa, kuma ya kyautata abin da ya bari”.

Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa marigari Abba Kyari na gudanar da ayyukan alherinsa a boye, domin ya dauki nauyin yara marayu fiye da 200 ana ba su ilimi, kuma yana wannan aiki sama da shekara 10, sannan yana taimaka wa masu karamin karfi a tsakanin al’umma.

Marigayin dai ya rasu ne da daren Juma’a sakamakon kamuwa da ya yi da cutar coronavirus yayin wata tafiya da ya yi zuwa kasar Jamus a watan jiya, aka kuma yi jana’izarsa ranar Asabar a Abuja.