✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake yin fanke

Assalamu alaikum uwargida tare da fatan alheri kuma kina cikin koshin lafiya. Mata da dama ba su damu su ko yi yadda ake girka fanke…

Assalamu alaikum uwargida tare da fatan alheri kuma kina cikin koshin lafiya. Mata da dama ba su damu su ko yi yadda ake girka fanke ba, saboda daga zarar maigida ya bukata sai dai kawai a je waje a sayo a bakin titi. Hakan bai dace ba.

Yana da kyau a nuna wa maigida cewa, an iya girki iri-iri ba tare da an je an sayo a wani wuri ba. Ya kamata ana tausaya wa maigida domin yana sayen kayan cefane bai kamata kuma ya rika sayan abinci a waje ba.

 

Abubuwan da za a bukata

•        Bota

•        Kwai

•        Madarar fulawa

•        Fulawa

•        Sukari

•        Bakar hoda/ Yeast

•        Gishiri kadan

•        Filebo

 

Hadi

A samu fulawa a tankade ta sannan a jika sukari a dama da ruwa kadan a kofi a yi ta gaurayawa har sai ya narke. A zuba fulawa a kwano, a zuba bota kamar cokali 2, a dirza ta da fulawa har sai ta bata a cikin fulawa. Sannan a zuba yeast kamar cokalin shan shayi biyu a ruwan dumi a jira na kamar minti 5, bayan minti 5 za a ga ya dan yi kumfa a saman kofin. Sannan a zuba madarar fulawa da gishiri rubu’in cokalin shan shayi da filebo, a fasa kwai kamar biyu. Sannan a ci gaba da murzawa. A zuba ruwan yeast a kwaba sannan, a dauko ruwan sukarin nan a zuba ana kwabawa har sai yadan yi kauri haka daidai kwabin fanke. Bayan sun kwabu sosai. Sai a rufe na tsawon yini guda. Wadansu kuma za su iya jiransa sai ya tashi kafin tuya.

Bayan kwabin ya tashi, sai a dora man gyada a tukunyar tuya a yanka albasa. Bayan ya yi zafi sai a rika yankawa daidai girman fanken da ake so. Har sai sun toyu sannan a kwashe a sanya wa maigida a kwanon karyawarsa.

Za a iya cin wannan fanken da shayi kuma ya fi dacewa da karyawa.