Da Dumi Dumi

Yadda ake yin miyar ‘Afang’

Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. A kullum muna kawo muku girke-girke irin namu na Arewa, amma a yau mun koma girke-girke irin na mutanen Akwa-Ibom. Yana da kyau a rinka gwadawa maigida nau’ukan girki daban-daban domin kada ya fara tunanin cin abinci a waje. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da za a bukata
• Ganyen ‘water leabe’
•Kifin crayfish
•Ganyen ukazi
• Magi
• Busashen kifi
• Ganda
• Man ja
• Nama
•Dodon kodi (ba dole)

Hadi
A wanke dodon kodi da ruwan lemun tsami. Sannana sulala naman da magi da albasa har sai ya nuna. A yanke ganyen ‘water leabe’ sannan a wanke da ruwan gishiri sannan a saka a rariya yadda ruwan jikin ganyen zai tsiyaya bakidaya.
A jika busashen kifi a ruwan dumi sannan a cire kashin jikin kifin sannan a zuba a cikin tukunyar naman har sai ya yi laushi, har ruwan miyar ya kusan shanyewa, sannan a zuba man ja da kifin nau’in “cray fish” sannan a juya su. A saka magi da nikakken barkono da dodon kodi  sannan a rufe ya turara na tsawon mintuna uku zuwa biyar.
Sannan a zuba ganyen water leabes sai kuma a zuba ganyen ukazi, sannan a juya su sai a rufe tukunya su turara na tsawon mintuna biyar bayan haka, sai a sauke.
Za a iya cin wannan miyar da sakwara ko fufu ko kuma da tuwon alkama.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya