✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake yin Wainar Dankali

Kayan hadi: . Dankalin Hausa . Kwai . Hoda da yis . Attarugu da albasa . Kayan kanshi . Man gyada Yadda ake yi Da…

Kayan hadi:

. Dankalin Hausa

. Kwai

. Hoda da yis

. Attarugu da albasa

. Kayan kanshi

. Man gyada

Yadda ake yi

Da farko uwargida za ki dafa dankalinki na Turawa ko na Hausa sai ki

sami kwano ki juye shi sai ki sa cokali ki farfasa shi yadda zai yi

laushi. Sai ki kawo kwai ki fasa a kai, sannan ki kawo kayan kanshi da

suka hada da citta da kirfa da tafarnuwa da sauran kayan kanshi. Sai

ki kawo sinadarin dandano ki zuba a ciki sannan ki kawo jajjagaggen

attarugu da yankakkiyar albasa mai yawa ki zuba a ciki sai ki juya,

yadda zai hadu sosai. Idan ya hadu sai ki kawo bakar hoda da yis ki

zuba a ciki domin ya  tashi. Sa ki rufe. Sannan sai ki dauko tandarki,

ki dora akan wuta ki zuba mai a ciki. Sai ki rika diban wanann hadin

dankalin kina zubawa a ciki. Ki lura idan kwabin ya yi kauri sai ki

dan kara ruwa amma kada yayi yawa. Daga nan sai ki fara soyawa kamar

yadda ake soya wainarki.

Ana iya cin wannan dankali da miyar nikakken nama ko a ci ta da lemo ko shayi.

Kwalliya