✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake zaben Sarki a Masarautar Wukari

A ci gaba da kawo muku tarihi da al’adun al’ummar Jukun a wannan mako Aminiya ta kawo muku yadda ake zaben Sarki ne a Masarautar…

A ci gaba da kawo muku tarihi da al’adun al’ummar Jukun a wannan mako Aminiya ta kawo muku yadda ake zaben Sarki ne a Masarautar Wukari. A al’adance idan aka samu gurbi a fadar Jukunawa, sakamakon mutuwa ko wani dalili na daban, dattawa masu zaɓen Sarki za su bayar da umarni ga gidajen sarautar Jukunawa guda biyu; wato zuriyar Bagya da Bama cewa su fitar da sunayen waɗanda suke ganin su suka cancanci wannan kujera ta sarautar Jukunawa. Idan suka samu waɗannan sunaye, sai kuma su bi matakan da aka saba da su wajen zaɓe da kuma naɗin sabon Sarki kamar yadda za mu gani a kasa:

 

Daren Litinin

Matakin farko daga cikin jerin matakan da dattawan Jukunawa ke dauka wajen zaɓen sabon Sarki shi ne kwana a garin Adi Bakundi a ranar Litinin da su masu neman kujerar suke yi. A wannan mataki ana umartar dukkan masu sha’awar wannan kujera ta Aku-Uka su fita daga garin Wukari zuwa garin Adi Bakundi cikin dare ranar Litinin, su kwana a can.

Zaɓe

Bayan an kwana ɗaya a Adi Bakundi, sai kuma a ayyana wata rana da za a yi zaɓen Sarki a cikinta. Idan ranar ta zo, sai waɗannan ’yan takara da suka kwana a Adi Bakundi su rankaya zuwa wani wuri da ake kira Abi.

A wannan wuri dukkan ’yan takarar za su yi shigar fararen kaya (zane da hula). Wannan shiga ana kiranta da Nbufyo a harshen Jukunanci. Bayan sun yi wannan shiga sai kuma a zaɓi ɗaya daga cikinsu bisa la’akari da waɗannan siffofi masu zuwa da za a zayyana:

Babban abin da dattawa masu zaɓen Sarkin Jukun suke lura da shi, shi ne halaye nagari waɗanda dama tun samartakar ’ya’yan Sarki ake lura da waɗannan halaye tare da su. Daga ciki akwai:

  1. Kawo arziki da wadata a dukkan faɗin ƙasar Jukun: Dattawan suna lura da cewa, duk ɗan sarki da za a zaɓa zai kawo ƙaruwar arziki da wadata ta hanyar samun damina mai yawan ruwan da za ta samar da kaka mai albarka da zaman lafiya da haɗin kai da kuma kwanciyar hankali.
  2. Sannan ɗan Sarkin ya zamo mai guje wa aikata laifuffuka.
  3. Ya zamo mai girmama na gaba da shi.
  4. Ya zamo mai tattali da kuma kiyaye shigar al’ada ta sarauta.
  5. Ya zamo mai kyawawan halayen da za su zama abin koyi a rayuwarsa ta sarauta da kuma ɗaiɗaiku.

Idan suka laluba suka tabbatar da waɗannan halaye a tare da ɗaya daga cikinsu, wanda dama kamar yadda na ambata tun samartakarsu ake lura da su, to sai a ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen Aku-Uka. Daga nan kuma sai abubuwa su ci gaba kamar haka:

Ziyarar Ɗakin Bauta

Bayan an zaɓi sabon Aku-Uka, sai kuma ya yi shigar baƙaƙen kaya shi kaɗai. Zai ɗaura baƙin zane sannan ya saka baƙar hula. Sai kuma ya shiga ɗaki mai tsarki da ake kira Kunbyi a Jukunanci.

Zaɓen Suna

Bayan zaman sabon Aku-Uka a ɗaki mai tsarki, sai kuma ya hau farin doki daga garin Abyi ya tafi Kuntsa. A wannan gari na Kuntsa ne zai zauna a kan fatar damisa, a kawo masa sunayen da sai Aku-Uka ne kaɗai yake amsa su, ya zaɓi guda ɗaya daga ciki. Sunayen su ne: Agbumanu, Awudumanu, Ahumanu, da kuma Kubyon.

Kuntsa, suna ne na babban shugaba mai tsarki, wanda yake bai wa Aku-Uka waɗancan sunaye ya zaɓi ɗaya daga ciki, sannan kuma bayan ya zaɓa ya damƙa masa kayayyakin sirrin sarauta (kamar a ce tagwayen masu da ake bayarwa a Kano), waɗanda mai riƙe da su shi ne Sarki.

Zaɓen Mata

A bisa al’adar Jukunawa, zaɓaɓɓen sabon Sarki yana gadar ɗaya daga cikin matan Sarkin da ya gada idan har mutuwa ya yi. Wannan al’ada kuma ana gudanar da ita a garin Puje. Wannan mata ita ake kira Wakuku.

Saboda haka bayan an kammala dukkan ayyukan al’ada da suka kamata a yi a Kuntsa, sai kuma Sarki da ayarinsa su zarce zuwa Puje, a nan za a fito masa da matan tsohon Sarki ya zaɓi guda ɗaya daga ciki wacce za ta zamar masa uwargida.

Hikimarsu ta yin wannan al’ada ita ce cewa, ita wannan mata ta tsohon Sarki ta riga ta zauna a gidan sarauta tare da tsohon Sarki, saboda haka ta koyi zama da Sarki, su kuma matan sabon Sarkin da za su shigo ba su da wannan gogayya, saboda haka ita sai ta koyar da su yadda ake kula da Sarki da kuma zaman gidan sarauta.

Shiga Fada

Mataki na ƙarshe a jerin abubuwan da ake yi a zaɓen Sarkin Jukunawa shi ne shigar Sarki fada. Bayan Sarki ya zaɓi mace daga cikin matan tsohon Sarki, sai matar ta kintsa kayanta ta baro Puje zuwa Wukari, idan ta zo ita za ta tarbi Sarki tare da sauran masu riƙe da sarautun gargajiya na Jukunawa a wani bigire (fili) da ake kira Afyin Acio.

Daga nan kuma sai sabon Aku-Uka ya zarce zuwa wani wajen bauta domin gudanar da ziyarar girmamawa ga abin bautarsu mai suna Yaku. Shi Yaku, shi ne ubangijin da yake bai wa Jukunawa kariya a lokutan yunwa da kuma annoba.

Bayan an kammala wannan ziyara, sai kuma sabon Aku-Uka ya shiga fadarsa ta mulki da take a babban birnin Jukunawa wato Wukari.

Wannan shi ne abin da aka saba da shi a tsarin naɗin sarautar Jukanawa a bisa turbar kaka-da-kakanni.

Majalisar Sarki

Wato Majalisar Aku-Uka, majalisa ce da take ƙunshe da mutum biyar; shi Aku-Uka (Sarki) kansa da Abon Acio (Waziri) da Abon Ziken (Galadima) DA Kinda Acio (Sarkin Gida) da kuma Kinda Ziken (Sarkin Bai).

Aku-Uka: Shi ne kankat a Masarautar Jukun. Matsayinsa ne sama da kowane matsayi. Shi ne mai shiga tsakanin abubuwan bautar Jukunawa da kuma al’ummar Jukunawa. Shi kaɗai yake iya magana da abubuwan bautar Jukunawa sannan ya sanar da mabiya abin da ya dace.

Abon Acio (Waziri): Shi yake da ikon gudanar da duk wani aiki da Aku-Uka zai yi matuƙar Aku-Uka ɗin ba ya nan ko yana halin rashin lafiyar da za ta hana shi gudanar da fada. Sannan shi ke bai wa Sarki shawara a harkokin al’adu da al’amuran yau-da-kullum. Yana da damar gudanar da shari’ar da ta shafi auratayya kai-tsaye ba tare da ya tuntuɓi Sarki ba. Amma kuma duk da haka, Waziri ba ya gadon kujerar Aku-Uka.

Abon Ziken (Galadima): Galadima shi ne Mataimakin Waziri, kuma mai gadon kujerarsa da zarar babu kowa a kanta. Yana taimaka wa Waziri wajen gudanar da ayyukan da suka shafi sarauta.

Kinda Acio (Sarkin Gida): Shi ne mai kula da al’amuran cikin gidan Aku-Uka. Yana kuma aiwatar da wasu ayyukan na fannin sarauta, sannan yana da mataimaka masu  riƙe da ƙananan muƙaman sarauta.

Kinda Ziken (Sarkin Bai): Shi ne shugaban masu riƙe da ƙananan muƙaman sarauta.

Bayan Zuwan Turawa

Da Bature ya zo ya kafa mulkinsa na mallaka a wannan ƙasa Najeriya, sai yanayi da tsarin yadda ake gudanar da zaɓe da naɗin sarakuna ya sauya. Wannan sauyi ya shafi Jukunawa. Kundin tsarin mulkin Najeriya yanzu ya bai wa Gwamnan Jiha damar amincewa ko watsi da sunan Sarkin da masu zaɓen sabon Sarki suka miƙa masa. Saboda haka sai aka samu ƙarin matakai guda biyu bisa yadda aka saba. Da farko akwai miƙa sunan Sarkin ga gwamnatin jiha domin tantancewa da zarar an zaɓa, sai kuma naɗi bayan an kammala gudanar da waɗancan al’adu da aka ambata a sama.

Idan masu zaɓen sabon Uka-Uka suka zaɓe shi, to za su tura sunan zuwa ga Gwamnan Jihar Taraba  a yanzu. Idan Gwamnan ya karɓi  sunan, shi ke nan sai a ci gaba da gudanar da waɗancan al’adu da na ambata a sama.

Sai kuma, mataƙi na ƙarshe da ya taɓa wancan tsohon tsari wanda shi ne na naɗi. Bayan an kammala dukkan waɗancan shagulgula, sai kuma Gwamna ya zo ya rantsar da Sarki a fadarsa.

Waɗannan su ne abubuwa biyu da suka shigo cikin sabgar zaɓe da naɗin sabon Sarki wato Aku-Uka a ƙasar Jukunawa.

Mun ciro wannan rubutu ne daga shafin Rumbun Ilimi na Intanet.