✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Alhaji Bello Ahmed ya rasu a kokarin hana dan kunar bakin wake kai hari a Jos

A yayin da ake ci gaba da zaman zullumi a garin Jos fadar Jihar Filato sakamakon tagwayen hare-haren bama-bamai da aka kai garin da suka…

A yayin da ake ci gaba da zaman zullumi a garin Jos fadar Jihar Filato sakamakon tagwayen hare-haren bama-bamai da aka kai garin da suka yi sanadin asarar rayukan sama da mutum 120 a Talatar makon jiya. Wani dan kunar bakin wake ya yi kokarin kai hari ga wani gidan kallon kwallon da ke dauke da mutum 700 a ranar Asabar da ta gabata, a titin Bauchi Road da ke kusa da Unguwar Rogo, sai dai bai samu nasara ba, bam din da yake dauke da shi, ya tashi sakamakon dakatar da shi da wani mai suna Alhaji Bello Ahmed Ali ya yi.
Alhaji Bello Ahmed Ali ya rasa ransa tare da dan kunar bakin waken da kuma wasu mutum biyu da suke wurin a kusa da gidan kallon kwallon.
Mutune da dama a garin Jos, suna ta juyayi tare da yabawa kan yadda marigayi Alhaji Bello Ali rasu a kokarinsa na hana dan kunar bakin waken kaiwa ga daruruwan mutanen da suke kallon.
Da yake yi wa wakilinmu karin bayani kan yadda lamarin ya faru, wani makwabcin marigayin kuma amininsa tun suna kanana mai suna Alhaji Sadik Ibrahim Musalla. Ya ce tunda rana dan kunar bakin waken ya kai motar cikin garejin da yake bayan gidan marigayi Alhaji Bello Ahmed da ke kusa da gidan kallon kwallon ya yi karyar a gyara masa birkinta ya lalace.
Ya ce kowa ya yi mamaki a garejin domin motar sabuwa ce, ya ce bayan da aka gyara ya fita da sunan yaje ya gwada, sai ya sake dawowa ya ajiye motar.
Alhaji Sadik Musalla ya ce da marigayi Alhaji Bello ya dawo kamar Allah ya sanar da shi cewa akwai sharri a cikin motar, sai ya ce bai yarda da motar ba, a dauke ta daga wurin. Ya ce ya rike dan kunar bakin waken suka yi ta jayayya a gaban yaran da suka zo kallon kwallon kan sai ya wuce zuwa gidan kallon amma ya ki yarda.
Ya ce sun yi ta jayayya da mutumin har zuwa karfe 8:30 na dare inda wani abokins Alhaji Auwalu Yusi da ke wajen ya dauko darduma zai yi Sallah nan take, sai bam ya tashi a motar ya hallaka su tare da dan harin da wasu yara biyu da suke cikin garejin.
Musallah ya ce tsakanin wajen da Alhaji Bello ya tsare motar dan kunar bakin waken zuwa gidan kallon wanda na wani kanensa ne bai fi mita 10 ba. Ya ce, da dan kunar bakin wake ya kai ga gidan kallon da ya kashe yara 700 zuwa 1000 da suke kallo a lokacin. “Alhaji Bello ya nuna shi gwarzon ne da ya kamata
al’umma ta yi masa godiya kan kokarin da ya yi, kuma su roki Allah ya gafarta masa, kan wannan abu da ya yi, na kubutar da daruruwan yara da maharin ya so ya halaka,” inji shi.
Ya ce hankalinsu ya tashi dangane da faruwar lamarin kuma wannan ya nuna cewa Najeriya tana cikin bala’i. Ya ce ya kamata kowa da kowa Musulmi da Kirista a kama addu’o’in Allah ya kawo karshen wannan bala’i.
Ya bukaci al’umma su taimaka wa iyalan marigayin wadanda a yanzu suke cikin mummunan hali
saboda rushewar gidansa sakamakon faruwar lamarin. “Akwai bukatar a hada hannu a sake gina gidan wannan bawan Allah, ba daidai ba ne a bar iyalansa a cikin wannan hali da suka shiga ba, inji shi.
daya daga cikin matan marigayin Khadija Adam Bello ta shaida wa wakilinmu cewa, “Muna cikin gida da ni da shi da sauran yaranmu, bayan da ya dawo. Sai muka ga ya tashi ya zagaya bayan gida, bayan ya fita sai ya ce wa daya daga cikin ’ya’yanmu ya zo ya gaya mana mu fita daga cikin gidan. Kafin yarona ya kara so, na dauki tukunya zan dora a risho in dafa abinci, sai na ji bam din ya tashi. Shi ne sai na ji
ya kwala mani kira.”
Ta ce daga nan ba ta sake jin muryarsa ba, silin din rufin gidan ya fado mata da ’ya’yanta Allah Ya taimake su muka samu suka fita.
Ta ce motar tunda Azahar take wajen ya yi ta magana, kan a dauke ta amma mai motar ya ki daukewa.
Ta ce ya rasu yabar mu biyu matansa da ’ya’ya tara.
Ana bayyana marigayi Alhaji Bello da mutumin kirki mai haba-haba da kowa kuma mutumin da bai da
abokin fada.
Harin ya lalata gilasan gidagen da ke kusa, kuma babban jami’in tsare-tsare na Hukumar Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) na shiyyar Arewa Muhammad Sulaiman ya shaida wa manema labarai cewa sun gano gawarwakin mutum hudu a harin.