✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Ali Jita ya shirya

kalankuwa da kaddamar da albam a Abuja Fitaccen mawakin nan Ali Isa wanda aka fi sani da Ali Jita ya shirya taron kalankuwa na musamman…

kalankuwa da kaddamar da albam a Abuja

Fitaccen mawakin nan Ali Isa wanda aka fi sani da Ali Jita ya shirya taron kalankuwa na musamman a garin Abuja.

Taron kalankuwar wanda ya kayatar da mahalarta an gudanar da shi ne a dakin taro na Lagos Hall da ke otal din Transcorp Hiton a Birnin Tarayya, Abuja  a ranar Asabar da ta gabata.

A lokacin taron Ali Jita wanda haifaffen birnin Kano ne, ya kuma kaddamar da albam din wakokinsa guda biyu masu suna ‘Lobe, inda daya na bidiyo ne mai dauke da wakoki bakwai, daya kuma na murya ne wanda yake dauke da wakoki 12.

A albam din wakokin na bidiyo a lokacin da aka nuna shi a dakin taron, fitattun jarumai irin su Hadiza Aliyu Gabon da Maryam Booth da Baba Ari sun fito a ciki, sannan daraktoci irin su J.K Omobo da Hassan Giggs suka ba da umarnin wasu daga cikin wakokin.

Mawaki Ali Jita ya yi hadaka da mawaka irin su Nazifi Asnanic da Morrel da kuma mawakin Kudu da ake kira Faze wajen rera wasu wakoki na albam dinsa mai murya.

Dakin taron ya cika da ’yan fim da mawaka da kuma daruruwan mutane da a cikinsu wadansu suka biya Naira dubu 250 ga teburi mai dauke da mutum 10 ko Naira dubu 150 ga teburi mai dauke da mutum biyar ko suka biya Naira dubu biyar zuwa dubu 10 duk da sun kalli taron kalankuwar.

Wadannan albam biyu su ne na 10 da kuma na 11 da mawakin ya fitar tun da ya fara harkar waka fiye da shekara 15 da ta gabata.

A yayin taron mawakin ya rera wakokin cikin kundin nasa mai suna ‘Lobe’, inda ya rera wakokin da harshen Hausa da kuma Ingilishi.

Sauran mawakan da suka nishadantar da masu kallo sun hada da Ahmad Musa Danja da Tagwayen Asali da Aminu Ladan Abubakar (ALA) da wata mawakiya ’yar Jihar Kogi mai suna Fenah da mawaki Abdul S. Thinking (mai gashi) da sauransu.

A lokacin da yake jawabi, mawaki Ali Isa Jita ya bayyana cewa ya samu karsashin yin wakokin albam din ne sakamakon mu’amala ta yau da kullum da ya rika yi da mutane.

Ya ce, “Mu’amalar da nake yi yau da kullum ta sanya na samu karsashin rubutawa da kuma rera wakokin cikin wadannan albam din, wasu daga cikin wakokin suna dauke da jigon soyayya da kuma jarumta.”

Jita wanda ya fitar da albam da suka hada da ‘Bakandamiya’ da ‘Zakin Maza’  ya ce kashi 10 cikin 100 na adadin kudin da ya samu a taron kalankuwar da kuma kaddamar da albam din nasa zai tafi ne wajen yaki da Cutar Sankara.

A lokacin da yake jawabi a wurin taron, jarumi kuma darakta, Bello Muhammad Bello (BMB) ya yaba wa Ali Jita bisa babban aikin da ya yi wajen samar da albam din ‘Lobe’ na murya da kuma na bidiyo.

Ya ce, “Wannan ba karamin namijin kokari ya yi ba, domin wannan ne karo na farko da wani mawaki a Kannywood ya shirya taron kalankuwa da kuma kadammar da albam a Abuja.”

Jarumi BMB ya kuma yi kira ga sauran mawaka su yi koyi da mawaki Ali Jita don ganin sana’ar waka a yankin Arewa ta samu babban tagomashi da kuma bunkasa.

Shi ma lokacin da yake jawabi, fitaccen mawaki, Nazir M. Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya bukaci mawaka su hada kai wajen ciyar da harkar waka a Arewacin Najeriya gaba har ta kai ga ta yi shahara a sauran kasashen duniya.

A cikin manyan mutane da suka halarci taron akwai Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Bagudu da matar Gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya A’isha Muhammad Abubakar da matar Gwamnan Jihar Kogi, Misis Rashida Bello da kuma matar Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya A’isha Ummi El-Rufa’i.

Sauran manyan jami’ai sun hada da matar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Halima Ibrahim Shekarau da tsohon Babban Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka da Alhaji Abdullahi Shu’aibu Maje da hamshakin dan kasuwa, Alhaji Alhassan Fatuhu  wanda ya sayi kwafi biyu na albam din a kan Naira miliyan biyu.

A cikin ’yan fim da suka halarci taron akwai fitaccen jarumi, Adam A. Zango da Yakubu Muhammad da Sadik Sani Sadik da Hadiza Aliyu Gabon da darakta Aminu Saira da mawaki Nazir M. Ahmad  da kuma Nazifi Asnanic. Sauran sun hada da fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara da jarumi kuma darakta, Bello Muhammad Bello (BMB) da jarumin barkwanci, Baban Chinedu da Babban Daraktan Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’Abba Afakallah.