✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Aliero ta sauya jihar Kebbi a idon duniya kan noman albasa

Garin Aliero a Jihar Kebbi ya yi suna  a noman albasa da harkokin kasuwanci. Yayin da garin Yawuri ya shahara a noman shinkafa, sai Argungu…

Garin Aliero a Jihar Kebbi ya yi suna  a noman albasa da harkokin kasuwanci. Yayin da garin Yawuri ya shahara a noman shinkafa, sai Argungu kuma da aka san shi a harkar kamun kifi da Kamba wanda ya yi suna ne a kasuwanci tsakanin kasashe saboda ya yi iyaka da Jamhuriyar Nijar da ta Benin.

Garin Aliero ya zama wata fitila a idon duniya kan noman albasa musamman kasashen Afirka. Garin sananne ne a noman albasa da kasuwancinta a nan  Najeriya da  kasashen Afirka.

Idan bako ya ziyarci garin Aliero zai iske matasa da kuma dattijan garin aikinsu ke nan noman albasa da kasuwancinta a  koyaushe.

Kasuwar albasa ta garin Aliero, kasuwa ce wadda a duk jihohin Arewa maso Yamma babu kasuwar albasa irinta kai hatta a sauran jihohin Najeriya.

Bisa ga haka ne ’yan kasuwa da manoman albasa na wasu kananan hukumomin jihar ke kai albasar da suka noma kasuwar  Aliero domin sayarwa ko su je domin sayowa domin amfani ko su sayar a wasu kasuwannin wasu kananan hukumomin jihar ta Kebbi.

Jama’ar garin Aliero na shuka nau’o’in albasa ne a cikin watan Agustan kowace shekara, bayan sun sare gero a gonakinsu. Har ila yau, daga watan Disamba zuwa watan Janairun kowace shekara ne lokacin kakar cire albasa.

Domin habaka noman albasa; Gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Sanata Muhammadu Adamu Aliero ta yi yunkurin gina babbar kasuwar albasa ta kasa da kasa a garin Aliero. An fara ginin babbar kasuwar albasar amma daga baya sai aka yi wa aikin ginin rikon sakainiyar kashi bayan Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya kammala wa’adin mulkinsa na Gwamnan Jihar.

Bayan wasu shekaru gwamnatin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta gina wata karamar kasuwar sayar da albasa a garin Aliero don ganin cewa ya zama wajibi a bunkasa kasuwancin albasa da nomanta a garin Aliero da ke Jihar Kebbi. Saboda kafin gina karamar kasuwar ’yan kasuwar na sayar da albasar ce a kan babbar hanyar mota da ta tashi daga Jihar Sakkwato zuwa Legas, inda a lokacin kakar albasa  manoman albasa da masu saye  sukan hadu a bakin babban titin mota don gudanar da cinikaiya.

Wani manomin albasa a garin Aliero, ya ce ‘‘Ayyukan manomin albasa bai tsaya dga noman albasa ba kawai, har da harkar sayar da albasa a kasuwar ta garin suna taruwa ne domin gudanar da cinikayyar buhuhunan albasa.”

“Idan manomin albasa ya kawo buhuhuna albasa daga garin Yawuri za mu saya a hannunsa, don mu sayar a kasuwar Aliero. Kuma kasuwancin albasa a garin Aliero babban kasuwanci ne gare mu. Dalili shi ne kasuwa ce wadda mutane daga wurare daban-daban na kasar nan suna zuwa domin sayen albasa mai yawan gaske a kullum. Haka daga jihohin Yarbawa da na Ibo sukan saye buhuhunan albasa da ke cika motocin tirela zuwa Legas, Ibadan, Ebonyi, Imo da sauransu.

Sauran sun hada da Maiduguri, Kano da sauran jihohin Arewacin kasar nan. Har ila yau, daga Jamhuriyar Benin da Nijar dukansu na zuwa wannan babbar kasuwar albasa ta garin Aliero da ke cikin Jihar Kebbi,” inji shi.

Kasuwar albasar takan fara ci ne daga misalin karfe 9 na safe har zuwa karfe 6 na yamma.

Haka wani dan kasuwar albasa da nomanta Malam Muhammadu Tukur ya ce, a bana ya noma buhun albasa fiye da 40 a gonarsa da ke garin Aliero, kuma ya sayi buhu 56 na albasa daga wadansu manoman Yawuri domin ya sayar a kasuwar ta Aliero.

‘‘Gaskiya ne cewa mutanen Aliero su ne suka fi kowa noman albasa a kasar nan, amma garin Yawuri da kuma Gada su ma suna iya noman albasa fiye da garin na Aliero,” inji shi.

Haka kuma ya ce, ‘‘Mutanen garin Aliero sun riga kowa fara noman albasa da kuma sayar da ita a kasuwa kafin daga baya mutanen Yawuri da Gada a Jihar Sakkwato su gane cewa akwai arziki a cikin noman albasa. Saboda haka shi ya sa muke shiga gaban kowa har aka sanmu a kan noman albasa. Wannan dalili ne ya sanya sauran manoman albasa idan suka noma albasa suke kawo ta kasuwar garin Aliero domin su sayar da ita. Farashin buhun albasa wanda irin daban-daban da ke akwai ya soma ne daga Naira dubu 11 zuwa Naira dubu 12 har dubu 13 zuwa dubu 15. A bara farashin albasa ya fadi kasa warwas har inda aka kai ana sayar da buhun albasa a ka Naira dubu 5. Wanda a shekarun baya da albasa ke da daraja har Naira dubu 30 zuwa dubu 35, mun sayar da buhun albasa. Ya danganta daga lokaci. Domin Allah ne Yake sanya albarka a cikin kasuwancin. Don a shekaru baya kasuwar albasa ta fadi har ana sayar da buhun albasa kan Naira dubu 2, zuwa 2,500.”

Ya kara da cewa: “Wani lokaci za ka ga ana sayar da buhun albasa a kan Naira dubu 23 zuwa dubu 24.”

Wadansu manoman albasa a garin Aliero sukan iya noma albasar da ke iya kaiwa buhu 10, 30, 50, 80 har zuwa buhu 200. Wannan yana faruwa ne a nan garin Aliero yayin da lokacin kakar cire albasa ya kama. Kuma wadansu manoman albasa na wasu yankunan Jihar Kebbi da ’yan kasuwarta ma suna kawo tasu albasa a garin Aliero idan lokacin kakar cire albasa ta kama.

Ya ce ‘‘Idan ka dubi kasuwar nan za ka ga tireloli A tsaye a ciki da wajenta, inda suka dauko buhuhunan albasa daga wasu yankunan Jihar Kebbi, za su wuce da ita zuwa jihohin Arewa da Kudu na kasar nan. Har ila yau, wasu tirelolin za su dauki buhuhunan albasa ne zuwa Jamhuriyar Nijar da ta Benin. A wannan kasuwar ta albasa da ke garin Aliero, dan kasuwa daya na iya sayar da buhuhunan albasa 20 zuwa 60 a kowace rana.”

A yayin da wakilinmu ya kai ziyarar gani da ido a kasuwar albasa ta garin Aliero ya tarar ana ta hidimar saye da sayar da buhuhunan albasa a kasuwar. Haka hanyoyi shida na shiga cikin kasuwar sun toshe, ta yadda yake da wahalar gaske kafin a samu hanyar wucewa domin shiga kasuwar, saboda za a ga tireloli suna sauke buhuhunan albasa da loda su cikin tirelolin domin fita da su zuwa wasu jihohin kasar nan da kasashe makwabta. Daya daga cikin ’yan kasuwar albasa da ya kasa buhuhunanta a wajen daya daga cikin kofofin shiga kasuwar, Malam Suleiman Aliero, ya ce, ‘‘Yadda ka ga yanayin kasuwar da ta cika da buhunan albasa da masu saye haka kasuwar ke ci a kullum. Bugu da kari yawan motoci da masu sayen buhuhunan albasa da manoma masu kawo albasa domin masu sayarwa na shan wahala wurin shiga kasuwar saboda yawan motoci da mutanen da ke shiga cikinta. Kowa na kokarin samun wurin da zai sauke albasarsa domin ya sayar ko ya saya domin kai ta wasu kasuwanni na wasu jihohin kasar nan. Saboda haka babu wani abin da za mu iya yi domin rage yawan jama’a ko yawan motocin tireloli masu shiga kasuwar. Wannan ita ce babbar kasuwar albasa a Jihar Kebbi.”

Ban taba jin wata kasuwar albasa da ta yi yawa ko girman wannan ta garin Aliero ba a duk fadin Najeriya.