✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Amitabh Bachchan ya yi shekara 50 yana fim

A watan jiya ne, fitaccen jarumin fina-finan Indiya Amitabh Bachchan ya cika shekara 50 cif da fara yin fim. Jarumin wanda har yanzu tauraruwarsa na haskawa…

A watan jiya ne, fitaccen jarumin fina-finan Indiya Amitabh Bachchan ya cika shekara 50 cif da fara yin fim.

Jarumin wanda har yanzu tauraruwarsa na haskawa a fina-finan Indiya, ya taka muhimmiyar rawa a harkar fim.

Kafin Amitabh ya kai matsayin da yake a yanzu, ya sha gwagwarmaya da fama a lokacin da yake tasowa a harkar.

Da farko dai a rayuwarsa ya so ya zamo mai aiki a gidan rediyo, wato mai gabatar da shirye-shirye, amma lokacin da ya je wani gidan rediyo domin aiki sai aka ki daukarsa saboda babbar muryar da yake da ita.

Amitabh Bachchan, saboda tsabar neman abin yi a lokacin, ya kasance har kwana yake a benci a wajen da yakan je neman aiki.

Haka ya yi ta gwagwarmaya, har daga karshe ya samu da kyar aka gwada shi a fim kamar yadda gidan rediyon BBC ya rawaito.

Daga cikin fina-finansa akwai, Amar Akbar Anthony da Mard da The Great Gambler da Coolie da Silsila da Khabhi Khabhi da Kaalia da Toofan da Shahensha da Sholay da Naseeb da Zanjeer da Deewar da Don da kuma sauransu.

Babu irin rawar da Amitabh ba ya takawa a fim, kama daga jarumin fim ko mai taimaka wa jarumi ko uba da sauransu.

Wani abu da ya sa Amitabh ya kara shiga ran mutane shi ne shi mutum ne mai son barkwanci a fim.

Amitabh dattijo ne mai tausayi a yanzu, domin yakan cire makudan kudi ya bayar tallafi ga mabukata ko wadanda wata masifa ta auka musu a kasarsa.

A tsawon shekara 50 din da ya yi a harkar fina-finai, Amitabh ya ce ‘ Ni a yanzu babu abin da zan ce wa Bollywood sai dai godiya wadda ba ta misaltuwa, domin kuwa duk abin da na zama a yanzu ita ce sanadi, haka duk a bin da na tara, Bollywood ce sanadi.”

An haifi Amitabh ne a ranar 11 ga Oktoban 1942, shekararsa 76 ke nan a yanzu.

Jarumi ne kuma da ya taba shiga harkar siyasa a baya.

Yakan gabatar da manyan shirye-shirye a gidajen talabijin din kasarsa wadanda mutane ke son kalla, ba a kasar ba kawai har ma da wasu kasashen duniya.

Ya auri jaruma Jaya Bachchan, inda suka haifi ’ya’ya biyu mace da namiji, namijin Abhishek Bachchan, shi ma jarumi ne, kuma ya auri jaruma Aishwarya Rai.

Yana da jikoki uku.

Ya yi suna ne a shekarun 1970, sakamakon fitattun fina-finan da ya yi kamar Zanjeer da Deewaar da kuma Sholay.