Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yadda bene mai hawa 3 ya rufta da ’yan makaranta sama da 100 a Legas

Akalla dalibai ’yan makarantar karama da babbar firamare sama da 100 ne suka makale a cikin buraguzan ginin nan mai hawan bene uku da ya rufta a Unguwar Itafaji a cikin garin Lagas a ranar Larabar da ta gabata da misalain karfe 10 da minti 20, lamarin da ya tada hankulan jama’ar yankin wadanda suka bazama domin ceton rayukan yara kananan da hatsarin ya rutsa da su.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton jami’an ba da agajin gaggawa na Jihar Legas da train jama’ar yankin na ci gaba da aikin ceton yaran da suka makale a cikin buraguzan ginin, inda aka ceto sama da dalibai hamsin.

ADVERTISEMENT

Mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Legas Mista Kehinde Adebayo ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce zuwa yanzu jami’an hukumar na ci gaba da kokarin ceton rayukan wadanda hatsarin ya rutsa da su, inda aka kai wadanda suka sami raunuka babban asibitin Gwamnatin Tarayya da ke yankin a Unguwar Marina. Kana har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a kai ga gano musababbin faruwar lamarin ba.

Gwamnan Jihar, Akinwumi Ambode ya isa wajen da lamarin ya faru, inda ya ba da tabbacin cewa an sami ikon ceto yara da dama da ransu a daidai lokacin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru, inda ya yi jawabin kwantar da hankalin al’ummar.

ADVERTISEMENT

“Ana kan shawo lamarin, mataimakina ya isa babban asibitin da aka kwantar da wadanda suka jikkata don ganin an ba su kulawa ta musanmman,” inji shi.

Ya yi kira ga masu mallakar gidaje a yankin da su tabbatar suna bin ka’idojin yin gini.

Wani mazaunin yankin mai suna Malam Sani Zarewa, shugaban kungiyar Arewa Gari Ya Waye, wanda ya shaida faruwar lamarin ya shaida wa Aminiya cewa abin takaici ne ganin yadda ake yawan samun rushewar gidaje a birnin na Legas, ya ce laifin hukumar da ke kula da tsarin gine-gine a birnin na Legas ne da ma gwamnatin jihar. “Domin da zarar ka fara gini za ka ga ma’aikatan wannan hukuma sun fara yo maka zarya kuma da zarar ka ba su ’yan kudin da suka bukata sai su tafi abinsu, ba za su zo su binciki yanayin da aka daura harsashin ginin ba. Babu ruwansu da yawan rodi ko simintin da aka saraffa a ginin, su dai fatansu su karbi kudi su zuba a aljihunsu, in ya so duk ranar da ginin ya rufta ko mutum nawa ya kashe babu abin da ya dame su,” inji shi.

Cikin garin Legas, inda lamarin ya faru yanki ne da ke da yawan gidaje masu hawan bene uku zuwa hudu ko biyar, wadanda asalinsu ba gidajen bene ba ne, sai aka mayar da su na bene, inda ake samun cukoson irin wadannan gidaje cike da jama’a da ke amfani da gidajen a matsayin rumfunan kasuwa ko ajujuwan makaranta; domin karatun ’ya’yansu ko kuma dakunan kwana, inda akan sami akalla mutum 4 zuwa biyar a dakin kwana guda, duk a dalilan karancin muhalli tare da tsadarsa a wannan yanki na Jihar Legas.