✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin gasar City People Entertainment Award ya gudana a Legas

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka gudanar da bikin gasar City People Entertainment Award a wurin taro na Heaben Ebent Centre da ke…

Zaharaddeen Sani rike da kyautarsaA ranar Lahadin da ta gabata ne aka gudanar da bikin gasar City People Entertainment Award a wurin taro na Heaben Ebent Centre da ke garin Legas.
Masu kallo ne suka zabi wadanda suka samu nasara ta hanyar turo sakon waya, ba wai an dauko fina-finan jaruman sannan alkalai suka tantance ba.
Rukunin wadanda suka samu nasarar sun hada da ‘yan fim din Yarabanci da Hausa (Kannywood) da Turanci (Nollywood) da gidan talabijin da rediyo da kuma mawaka.  
Wadanda suka samu nasara sun nuna farin cikinsu, inda wadansu kuma suka sadaukar da nasarar da suka samu ga masoyansu.
Ga jerin jadawalin wadanda suka samu nasara a bangaren Kannywood:
Fuskar Kannywood:
Ali Nuhu
Gwarzon Jarumi:
Sani Danja
Gwarzuwar Jaruma:
Rahama Hassan
Mai Tallafa wa Gwarzon Jarumi:
Zaharaddeen Sani
Mai Tallafa wa Gwarzuwar Jaruma:
Nafisa Abdullahi
Gwarzon Sabuwar Fuska bangaren maza:
Yakubu Mohammed
Gwarzuwar Sabuwar fuska bangaren mata:
Halima Atete
Gwarzon Darakta:
Aminu Saira
Gwarzon Furodusa:
Sani Danja
Gwarzon fim:
‘Oga Abuja’
An kuma karrama Hajara Usman da Bashir Nayaya da Ibrahim Mandawari da kuma Hauwa Maina.