✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin Kirsimeti ya gudana a sassan Najeriya

A shekaranjiya Laraba ce aka gudanar da bikin Kirsimeti don murnar ranar haihuwar Annabi Isa (AS) a fadin duniya, inda mabiya addinin Kirista a Najeriya suka…

A shekaranjiya Laraba ce aka gudanar da bikin Kirsimeti don murnar ranar haihuwar Annabi Isa (AS) a fadin duniya, inda mabiya addinin Kirista a Najeriya suka yi bukukuwa tare da addu’o’in samun zaman lafiya ga kasa.

A sakonsa na Kirsimetin bana, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya al’ummar Kirista murnar zagayowar wannan rana, inda ya bukaci mutane su zauna lafiya da juna.

Ya ce, kasancewar bikin yana tuna haihuwar Annabi Isa (AS) ne, ya kamata mutane su yi koyi ne da rayuwar Annabin ta son juna ba tare da nuna kabilanci ba, tare da tsayawa kan abin da ya hada kasar baki daya, sannan ya bukaci masu bikin su guji aikata duk wani abu da ya saba wa ka’ida.

Shugaba Buhari ya ce murnar haihuwar Annabi Isa (AS) da koyi da halayensa bai kamata ta zama abin rana daya kawai ba, inda ya ce ya kamata ne ta zama an ci gaba da koyi da shi a kullum.

A jawabin Shugaban Cocin Assemblies of God na Gundumar Saminaka da ke Jihar Kaduna. Kuma wakilin Shugaban Cocin na Kasa a Arewa maso Yamma, Rabaran Haruna Tutu ya ce, “Muna kira ga shugabanni su lura cewa lokaci ya yi da za a dubi halin matsin da jama’ar kasar nan ke ciki.”

Ya ce, “Jagoranci mai kyau, shi ne shugabanni su dubi halin da jama’arsu ke ciki, idan talakawansu suna jin dadi, nan ne za su ji dadin yin mulki. Saboda haka wannan babban nauyi ne, kuma babban hakki ne, da ke kan shugabanni su dubi halin da jama’arsu ke ciki don daukar matakan gyara.”

Rebaran Tutu ya ce bikin Kirsimetin da ake yi ana tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu ne, wanda  ya kawo zaman lafiya da alheri da ci gaba a duniya. Ya ce saboda haka ya kamata dukkan al’umma a rungumi juna kuma a rungumi wannan zaman lafiya da ya kawo.

A Jihar Jigawa, ’yan kasuwa ne suka dara, inda masu kayan abinci da mahauta suka rika kai-koma saboda ayyukan ranar Kirsimeti.

’Yan kasuwa musamman mahauta sammako suka rika yi zuwa kasuwa domin saye da sayar da nama ga Kiristocin da ba su yi yanka ba, wadansu kuma suka je coc-coci, inda suka rika taya Kiristocin yanka tare da gyara musu nama.

Su ma ’yan acaba sai kaiwa suke suna komawa da yara da manya daga gidaje zuwa coci-coci.

Wakilinmu da ya zagaya birnin Dutse ya gane wa idonsa yadda jami’an tsaro dauke da bindigogi wadansu rike da sanduna a bakin tituna da harabobin coci suna  sinitiri domin bai wa Kiristocin da ke ibada tsaro.