✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin mawaki MD Anas ya wakana

A makon jiya ne aka yi bikin mawaki Muhammad Anas, wanda aka fi sani da MD Anas tare da amaryarsa Fatima Aminu. Wannan bikin ya wakana…

A makon jiya ne aka yi bikin mawaki Muhammad Anas, wanda aka fi sani da MD Anas tare da amaryarsa Fatima Aminu.

Wannan bikin ya wakana ne a garin Kwantagora na Jihar Neja, kuma bayan daura auren, aka dunguma tare da abokan ango da kawayen amarya zuwa Kaduna, inda aka gudanar da bikin taya su murna a dakin taron na Rich Bite da ke kan Layin Sakkwato, a Kaduna.

Daga manyan bakin da suka halarci taron akwai Abbas Sadik, da Shugabar Kamfanin Lamaj Proudctions, Hajiya Fatima Lamaj da daya daga cikin manyan jarumai masu fitowa a matsayin uwa Hajiya A’isha Mahuta wadda ake kira Mama a Masa’antar Kannywood da mai shirya fina-finai Hafsa Suleiman da Jarumi Isma’il Koli da sauran masu shirya fina-finai, mawaka da daraktoci daga Kaduna da Kano.

Da yake zantawa da wakilinmu a wajen bikin auren, MD Anas ya ce yana matukar farin cikin ganin wannan rana na auren masoyiyarsa Fatima, “Gaskiya ina cikin farin ciki sosai ta yadda zai yi wuya in iya kwatantawa. Amma dai ina godiya ga Allah da Ya nuna min rana da nake tsimaya. Ina addu’ar Allah Ya ba ni ikon kula da matata Fatima yadda ya dace. Sannan ina godiya da dukan ’yan uwa da abokan arziki da suka samu halartar wannan biki. Da fata Allah Ya mayar da kowa gida lafiya,” inji shi.

Ita ma amarya Fatima, ta nuna farin cikinta, inda ta ce, “Wannan ba karamar rana ba ce a wajena. Ina addu’ar Allah Ya ba ni ikon kasancewa mai biyayya ga angona.”

Fitaccen jarumi Abbas Sadik ya bayyana Anas a matsayin mutum mai mutunci da biyayya da son zumunci, wanda a cewarsa shi ya sa mutane suka amsa kiransa har suka zo taya shi murna.

A bikin dai an yi kada-kade da raye-raye, inda mawaka da dama suka baje kolinsu domin taya dan uwansu murna.