✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin Ranar Hausawa ya gudana a wata sakandaren Jigawa

A shekaranjiya Laraba ce aka gudanar da bikin Ranar Hausawa a Makarantar Sakandare ta Model da ke garin Dutse, Jihar Jigawa. A yayin bikin wanda…

A shekaranjiya Laraba ce aka gudanar da bikin Ranar Hausawa a Makarantar Sakandare ta Model da ke garin Dutse, Jihar Jigawa.

A yayin bikin wanda aka gudanar da nufin raya al’adun Hausawa, an nuna wa yara yadda ake yin bikin saukar karatun Alkur’ani a tsarin gargajiyar Bahaushe. Yayin da kuma a gefe daya aka gabatar da wasan kwaikwayo a kan yadda al’adar Malam Bahaushe take da ta shafi rayuwar yau da kullum.

Haka kuma ’yan mata sun gabatar da kidan kwarya da rawa irin ta gargajiya, yayin da dalibai maza suka yi da’ira ana yi masu kidan kalangu suna taka rawar Malaja, wadda ake wa kirari da “Haujiya rawar mai wando, wanda ba ya da wando ya je gida ya yi kuka.”

A yayin bikin saukar karatun Alkur’ani kuwa, wani dalibi ne mai suna Lawan Ahmed ne ya zama zakara.

Shugaban makarantar Malam Lawan Yusuf ya ce sun bullo da bikin Ranar Hausa ce da nufin zaburar da dalibai su san al’adunsu. Ya kara da cewa irin wadannan bukukuwa suna sa wa yara sha’awa a zuciyarsu, su ji suna kaunar zama cikin makaranta saboda abubuwan da suke koya daga darasin al’adar Hausawa. “Kuma hakan yana kara debe wa dalibai kewa, ba za su rika samun damuwa ba yayin zaman makaranta, duk da cewa abubuwan da aka baje kolinsu a ranar sun san su a karance,” inji shi.