✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin Sallah ya gudana a Kalaba

Al’ummar Musulmi mazauna Kudu maso Kudu kamar takwarorinsu na sauran sassan kasar nan sun gudanar da Sallar Idin Layya lami lafiya tare da matakan tsaro…

Al’ummar Musulmi mazauna Kudu maso Kudu kamar takwarorinsu na sauran sassan kasar nan sun gudanar da Sallar Idin Layya lami lafiya tare da matakan tsaro da aka saba ba su idan bukukuwan Sallah suka taso.

A Jihar Kuros Riba dimbin  Musulmi ne a fadin jihar suka gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da kwanciyar hankali yayin da limamai da shugabannin addini da gwamnatin jihar suka bukaci Musulmi mazauna jihar su dukufa wajen yi wa kasa addu’a kuma su ci gaba da zama da kowa lafiya.

Sarkin Hausawa da Fulani na Jihar, Alhaji Salisu Abba Lawan, ya bukaci al’ummar Musulmi su zauna lafiya da sauran ’yan uwansu da masu masaukinsu ’yan asalin Jihar Kuros Riba kamar yadda suka saba shekara-da- shekaru.

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya gana da manema labarai a fadarsa a ranar Lahadi da ta gabata. Ya ce “Addinin  Musulunci addini ne na zaman lafiya ya kuma koya wa mabiyansa su zauna lafiya da sauran jama’a da ma wadanda ba Musulmi ba kamar yadda Manzon Tsira (SAW)ya zauna da wadanda ba su yi masa biyayya ba.”

Da ya juya kan halin da kasar nan take ciki na matsalar tsaro, Alhaji Abba Lawan ya bukaci gwamnati ta kara jan damara musamman yadda wadansu batagari ke haddasa fitintinu a kasar nan domin a bata sunan gwamnatin. Sarkin Hausawa da Fulanin ya ce “Jama’a suna da muhimmiyar gudunmawa da za su bayar wajen taimaka wa gwamnati ta inganta tsaro kamar yadda aka saba shekarun baya.”

A hudubarsa Malam Auwal Abdulkarim, Limamin Masallacin Mopol 11 da ke Kalaba, ya bukaci al’ummar Musulmi su jajirce wajen neman ilimi da kuma koyi da abin da addininsu ya karantar, kuma su rika yi wa shugabanni da’a da yi musu addu’a.

A tasa Hudubar Malam Bashir Salihu Abuga, Babban Limamin Masallacin Izala da ke Kalaba kira ya yi ga jama’a su yi koyi da halayen Manzon Tsira (SAW) da kuma yadda ya yi mu’amala  da mutane, kuma wajibi ne Musulmi ya yi riko da Sunnah .

Gwamnan Jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade ya taya al’ummar Musulmin jiharsa murnar bikin Sallar, kuma ya bukaci su zauna lafiya da kowa kamar yadda suka saba, kana su yi wa kasa addu’ar alheri.

Gwamnan ya furta haka ne a cikin sanarwar da Sakataren Watsa Labaransa Christian Ita, ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai a Kalaba.

An gudanar da bukukuwan salin alin ba tare da samun wata tangarda ba.