✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Buhari da Shugaban Guinea suka yi bikin Babbar Sallah a Daura

Garin Daura, wanda yake mahaifar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne, an yi gagarumin biki Hawan Babbar Sallah don karrama Shugaban Kasar Guinea, Alpha Conde; wanda…

Garin Daura, wanda yake mahaifar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne, an yi gagarumin biki Hawan Babbar Sallah don karrama Shugaban Kasar Guinea, Alpha Conde; wanda ya kawo ziyara ta musamman ga Shugaban Kasa  Muhammadu Buhari.

Dukkan shugabannin biyu sun gabatar da Sallah a Masallacin Idi da ke Kofar Arewa a garin Daura da misalin ƙarfe 9:37 na safe, bayan minti biyu da isowarsu masallacin. Shugaba Buhari da bakonsa sun baro gidansa da ke Unguwar GRA da misalin karfe 9 da rabi.

Daga cikin ’yan rakiyar da suka zo masallacin tare da Shugaba Buhari, akwai dattijo daga cikin masu fada-a-ji, kuma dan uwansa Alhaji Mamman Daura sai kuma Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da sauransu.

Babban Limamin Daura, Alhaji Safiyanu Yusuf Dansawwai ne ya jagoranci Sallar mai raka’a biyu. Bayan sallamewa sai Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk ya jinjina wa Shugaba Buhari, inda ya ce suna alfahari da shi matuka tare kuma da ci gaba da yi masa addu’a.

“Za mu ci gaba yi maka addu’a kuma in Allah Ya yarda za ka ci gaba da yin nasara a kan makiya kuma sai Allah Ya kunyata su,” inji Sarkin Daura.

Daga nan sai Shugaba Buhari tare da bakonsa Alpha Conde suka yanka ragunansu na layya, wadanda aka kiyasta kudinsu a tsakanin Naira dubu 35 zuwa Naira dubu 40 kowannensu.

Shugaban ya sake komawa gidansa kafin sake fitowa don kallon Hawan Sallah a Fadar Sarki, wanda hakan shi ne na farko a wajensa. A cikin wata ’yar gajeruwar hira da aka yi da shi, Shugaba Buhari ya nuna farin cikinsa a kan irin yadda ake gudanar da bikin Sallah a cikin kwanciyar hankali da lumana. Kazalika ya sake nanata kudirinsa na yaki da cin hanci.

Har ila yau, Shugaban Kasar ya karbi bakuncin masu yi wa kasa hidima da ke yankin Daura. Shugaba Buhari tare da bakonsa Shugaba Alpha Conde sun bai wa masu yi wa kasar hidimar kyautar raguna biyu da kuma buhun shinkafa 10 tare da Naira dubu 250 domin su ma su yi hidimar abincin Sallah.

Jagoran masu yi wa kasar hidima, Aliyu Abdullahi ya yi wa Shugaban godiya bayan yi masa addu’a da kuma kasar baki daya. Sannan ya sake jinjina wa Shugaba Buhari kan yadda yake yaki da cin hanci da kuma abin da ya shafi matsalar tsaro.

Ya ce, “Daura da Katsina wurare ne na zaman lafiya, inda masu yi wa kasa hidima suka kara zama tsintsiya madaurinki daya.”

A lokacin da yake mayar da jawabi bayan ya yi godiya, Shugaba Buhari ya ce shirin tura masu yi wa kasa hidima da ake yi, ba karamin hadin kan ’yan kasa ne ba. “Wanda ya fito daga Legas ko Fatakwal da sauran wasu wurare na sassan kasar yau duk ga ku a karshen kasar kuma a hade. Hakan kuma ya ba ku damar sanin wurin kuma ya fitar da shakku daga zukatan marasa ilimi, wanda hakan ya sa suke yin batanci a kai. Sha’anin hidimar kasa ne kadai da na ’yan sanda da sojoji ke hada mu waje daya,” inji Shugaba Buhari.

Shi kuwa babban bako ta hanyar yi masa tafinta, Shugaban Guinea Alpha Conde kira ya yi ga masu yi wa kasa hidima da su ci gaba da hadaka kai a tsakanin ’yan kasa.

“Farko ku fara sanin cewa ku ’yan Najeriya ne kafin sanin cewa na fito daga wani yanki ko kabila,” inji Conde.

Bikin Hawan Sallar dai wanda aka yi a Kofar Fadar Sarkin Daura aka shirya wa Shugaba Conde ya kayatar sosai.

A lokacin hawan, hakimai da dagatai da  sauran masu rike da sarautun gargajiya da ayarinsu sun rika fitowa daya bayan daya domin nuna farin ciki da kuma irin shirin da suka yi don wannan rana. Wannan bikin ya bai wa hakimai wadanda ke bisa dawaki kai gaisuwar girmamawa ga Sarkin wanda yake tsaye a bisa doki.

Daga cikin hakiman da suka kai gaisuwar har da Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba wanda masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da shi a kwanakin baya.

A jawabinsa a lokacin  bikin, Mai martaba Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, wanda Sakataren Majalisar Masarautar Alhaji Abdulmumini Salisu ya karanta, ya yaba wa Shugaba Buhari bisa ga hakuri da kuma jajircewar da yake da ita a wajen tafiyar da jagorancin kasar nan.

 Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Faruq Umar Faruq na musabaha da Shugaba Conde, yayin da Buhari ke kallo
Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Faruq Umar Faruq na musabaha da Shugaba Conde, yayin da Buhari ke kallo

“Muna godiya ga bakonmu Shugaba Conde a kan wannan ziyara da ya kawo wa kasar kuma har ya zo garin Daura domin ya yi bikin Babbar Sallah ta bana tare da Shugaba Buhari,” inji Sarkin.

Sarkin ya sake yin kira ga Daurawa cewa su tabbata suna bai wa ’ya’yansu ilimin addini da na zamani. Su kuma ci gaba da bayar da hadin kai a kan abin da ya shafi sha’anin tsaro.

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce an shirya wannan Hawan Sallah ne domin girmama bakon tare da nuna masa kyawawan al’adunmu.

“Zamowar Daura kan gaba a wajen ci gaban Hausa, ina da tabbaci kan cewa akwai abubuwa da yawa da za su nuna wadanda muna iya kai karfe 4:00 na yamma ba tare da an gama hawan ba,” inji Masari.

An dai nada Shugaba Alpha Conde a sarautar Talban Daura, daya daga cikin manyan sarautun da ake da su a masarautar. Kamar yadda Sarkin ya ce, an nada Conde a sarautar ce saboda irin soyayyar da ya nuna wa dansu Shugaba Buhari.

Sabon Talban Daurar kuma Shugaban Guinea ya ce farkon alakarsa da Shugaba Buhari ita ce lokacin da za a rantsar da shi a 2015. “Ban san Buhari ba a baya, na san shi a lokacin bikin rantsar da shi a 2015. A da na san Shugaban Kasa na Soja wanda nake yi wa dariya idan na ji an ce ya daure mutum har na tsawon shekara 50 a gidan yari. A zatona ma, wancan dalilin ne ya sa mutane suka ki zabensa har sau uku,” inji Conde.

Shugaba Conde ya ce lokacin da wadansu mutane suka mayar da hankalinsu a kan tara dukiya, shi kuwa Shugaba Buhari ciyar da kasa da jama’arta ya sa gaba.

Shugaba Alpha Cande ya ce da farko Sarkin Saudiyya ne ya gayyace zuwa Aikin Hajjin bana amma sai ya zabi ya zo Najeriya don ganin yadda ake bukukuwan Sallah.

“Abubuwan da na gani sun wuce abin da na rika hasashe. An karrama ni, an girmama ni, abubuwan da ba zan taba mantawa da su ba. Fatata ita ce, ni ma in gayyaci Shugaba Buhari zuwa Guinea domin ya ga irin al’adunmu,” inji shi.

Shugaba Conde ya shawarci ’yan siyasa su bai wa Shugaba Buhari goyon baya domin ganin ya maido da martabar Najeriya a idon duniya.