Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Yadda Buhari ya sa hannu a sabon kasafin 2020

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan sabon kasafin kudin shekarar 2020.

Yadda Buhari ya sa hannu a sabon kasafin 2020

A ranar Juma’a 10 ga Yuli ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan sabon kasafin kudin 2020 na Naira tiriliyan 10 da miliyan 800, da majalisar dokoki ta amince da shi.

Shugaban ya ce mummunar illar da annobar coronavirus ta yi wa tattalin arziki ce ta tilasta sake yin kwaskwarima a rage kasafin kudin na bana.

Ma’aikatu da hukumomin gwamnati za su karbi rabin kudaden manyan ayyukansu kafin karshen watan Yuli don tabbatar da an ci gaba da tafiyar da kasafin daga watannin Janairu zuwa Disambar kowacce shekara, inji shi.

Bikin sa hannun wanda ya gudana a dakin taro na fadar shugaban kasa ya sami halarcin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Ibrahim Gambari, shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan da kuma kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Kazalika, ministar kudi kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmed, karamin ministan kudi Clement Agba, gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele da kuma babban daraktan kasafin kudi Ben Akabueze sun halarci bikin.

Da misalin karfe 11:03 ne dai manyan hadiman shugaban kasa kan majalisun tarayya, Sanata Babajide Omoworare da Hon. Umar El-Yakub suka mika masa kasafin shi kuma ya rattaba hannun da misalin karfe 11:06 a gaban Osinbajo, Lawan da Gbajabiamila.

A watan Disambar shekarar da ta gabata ne dai shugaba Buharin ya rattaba hannu a kasafin da ya haura Naira tiriliyan 10 da biliyan 500.

Daga bisani kuma majalisa ta amince da shi a harsashen Dala 57 kan kowacce gangar danyen mai.

Sai dai daga baya faduwar da farashin danyen man ya yi a kasuwar duniya sakamakon annobar COVID-19 ta tilastawa gwamnatin sake duba kasafin

A ranar 13 ga watan Mayu gwamnatin tarayya ta amince da Naira tiriliyan 10 da biliyan 523 a matsayin sabon kasafin kudin bayan wata wasika da ma’aikatar kasafin kudi, kasafi da tsare-tsare ta aike wa majalisar zartarwa ta kasa don amincewa da sabon tsarin kashe kudade na matsakaicin zango daga shekarar 2020 zuwa 2022.

Hakan dai na nufin an samu banbancin Naira biliyan 71 da miliyan 500 kan adadin da aka amince da shi tun da farko.

A ranar 11 ga watan Yuni, majalisar dattawa ta kara kasafin da Naira biliyan biyar wanda ya daga shi zuwa Naira tiriliyan 10 da biliyan 810.

Ministar kudi ta ce an yi gyaran fuskar ne domin kasafin ya dace da yawan gangar danyen man da ake haka daga ganga miliyan biyu da dubu dari daya zuwa ganga miliyan daya da dubu dari tara a kullum.