✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Coronavirus ta canja tsarin Tafsiri da Tarawih a azumin bana

Ga dukkan alamu bana al’ummar Musulmin Najeriya ba za su samu zuwa masallatai domin sauraren tafsirin Alkur’ani ko Sallar Tarawih ba, kamar yadda suka saba…

Ga dukkan alamu bana al’ummar Musulmin Najeriya ba za su samu zuwa masallatai domin sauraren tafsirin Alkur’ani ko Sallar Tarawih ba, kamar yadda suka saba saboda matakai daban-daban da hukumomi ke dauka domin dakile yaduwar cutar Kurona da ta gallabi duniya.

An samu rabuwar kai a Jos

A Jihar Filato, wadansu malamai sun goyi bayan dakatar da Sallar Tarawih, yayin da wadansu ba su goyi baya ba. Wannan na zuwa ne bayan da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bada umarnin a dakatar da sallolin na Tarawih da Tuhajjud, a watan azumin Ramadan bana a kokarin da ake yi na dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Ra’ayoyi

Ra’ayoyin malamai da kungiyoyin addinin Musulunci da limamai a Jos, fadar Jihar Filato, da wakilinmu ya zanta da su kan wannan al’amari sun bambanta.

Daraktan Makarantar Albayan da ke Jos kuma Shugaban Kwamitin da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam reshen Jihar Filato ta kafa, Dokta Muhammad Nazifi Yunus ya ce suna tare da sanarwar da Sarkin Musulmi ya bayar, na a dakatar da sallolin Tarawih da Tahajjud da taron Tafsiri a azumin bana.

Har ila yau ya ce sun yi matsaya cewa addinin Musulunci ya tsara yadda za a kare dukkan wata cuta da za ta cutar da al’umma, domin akwai ayoyin Alkura’ani da hadisai da dama da suka yi magana kan wannan al’amari. Ya ce a Musulunci, hatta hamma da atishawa akwai yadda ake yin su kuma addinin ne ya zo da rigakafi. “Muna kira ga al’umma, a daina yada labarai na tsoratarwa kan wannan annoba kuma mutane su zauna a gida, domin Manzon Allah (SAW) ne ya ce gidanka ya wadace ka, kada ka fita.

“Kowa ya koma ga Allah, domin barnar da ake yi a duniya ce ta sa Ya kawo mana wannan annoba. Don haka mu tuba mu koma ga Allah. Idan muka tuba muka koma ga Allah, zai yaye mana wannan annoba,” inji shi.

Shi ma Sakataren Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah ta Kasa reshen Karamar Hukumar Jos ta Arewa, karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau, Malam Rabi’u Ahmed Balarabe ya ce dama su tun kafin wannan lokaci, Shugaban Kungiyar Izala na Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ba su sakon su yi biyayya ga dukkan matakan da Gwamnatin Jihar da suke zaune ta dauka, kan dakile wannan annoba. Don haka ya ce tuni sun yi taro a karkashin jagorancin Kungiyar Jama’atu Nasril Islam a Babban Masallacin Juma’a na Jos, cewa duk hukuncin da shugabannin al’ummar Musulmi na kasa suka gabatar, suna tare da shi dari bisa dari.

Sai dai Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya ce za su gabatar da tafsiran Azumin watan Ramadan na bana, a masallatan kungiyar, bisa tsarin da gwamnati ta sanya, na kare yaduwar cutar Kurona.

Ya ce Musulunci yana tafiya ne da tsari na da’a da biyyayya ga shugabannin da suke tare da hukuncin Allah da ikonSa, amma ana kauce wa duk wani umarni da zai saba wa Allah da ManzonSa.

Ya ce, “Don haka ne za mu bi umarnin gwamnati da suka sanya, tunda bai saba wa Allah da ManzonSa ba. Don haka za mu yi tafsiri kuma za mu zauna wara- wara (nesa-nesa), sannan za mu zauna da mutanen da ba su fi 50 ba.”

Ya yi kira ga masu hali su taimaka wajen daukar nauyin sanya tafsiran a gidajen rediyo da talabijin da sauran kafofin yada labarai na zamani. Ya bukaci malamai masu tafsiri da al’ummar Musulmi su tashi su dauki azumi da sunan Allah kuma su roki Allah Ya yaye mana dukkan matsalolin da suke damunmu.

Yadda al’amarin yake a Kaduna

A Jihar Kaduna, alamu sun nuna cewa bana al’ummar Musulmi ba za su samu damar zuwa masallatai domin saurarar tafsirin Alkur’ani ko yin Sallar Tarawih ba, kamar yadda suka saba saboda matakan dakile cutar Coronavirus da ake dauka a jihar.

A bara kamar wannan lokaci, tuni an soma gudanar da tafsiri a manyan masallatan da ke babban birnin jihar, kamar Masallacin Tudun Wada, inda Sheikh Dahiru Usman Bauchi ke gudanarwa da Masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, inda Sheikh Ahmad Gumi ke gudanarwa.

Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, a kulle saboda cutar Coronavirus

A yanzu haka dukkan masallatan biyu da sauran masallatan da ke fadar jihar da ake aiwatar da tafsiri duk a rufe suke, wanda hakan ke nuna ba za a yi karatun ba cikinsu a bana.

Hatta Sallar Tarawih ko Asham da ake yi duk shakara a cikin watan Ramadan, a bana ba za a yi ba, domin gwamnatin jihar ta hana cinkoso a wuraren ibada, don dakile yaduwar cutar da ta addabi duniya ta Kurona.

Dokta Ahmad Gumi ya bayyana wa Aminiya cewa tuni ya fara Tafsirin bana a gidansa, ba kamar yadda ya saba yi a masallaci ba. Ya ce kuma jama’a ba za su taru ba, domin ta hanyar rediyo za a rika yadawa, don al’umma su rika saurare.

Ya ce daga shi sai masu daukar karatun, wato ma’aikatan gidan rediyon ne za su kasance, daga baya sai a yada saboda haka a bana babu taron jama’a kamar yadda aka saba. A kan ko yaya yake ji, kasancewar shekaru da yawa a masallaci ake taruwa, sai ya ce: “Da ma mafi yawan jama’a ta rediyo suke sauraran Tafsirin, don haka masu zuwa masallaci ai ba su fi dubu biyar ba. Saboda haka ba wani abu ba ne sabo.”

Game da Sallar Tarawih kuwa, sai ya ce “Ita ma ba za ta yiwu ba sai dai mutane su yi sallarsu a gidajensu. Mutum ya yi Sallar ko da matarsa ya yi sun samu jam’i. Da ma an fi son a yi Sallar Tarawih a gida.”

Ya ja hankalin jama’a su kwantar da hankalinsu. Ya ce, “Dole a damu, saboda jarrabawa ce daga Allah amma sai dai mu koma ga Allah, a kuma yi abin da ya kamata. A roki Allah kuma a bi abin da masana kiwon lafiya suka ce. Idan har mutum ya bi ka’ida kuma abin ya same shi, to, insha Allahu yana da ladar shahidi amma idan ya keta dokar, ba zai samu ladar shahidi ba. Domin ba za ka saba wa Manzon Allah ba, ka ce kana zama shahidi.” Shi ma Sheikh Haliru Maraya, wanda ya kwashe shekaru yana gudanar da Tafsiri a  Kaduna, ya bayyana ra’ayinsa kan rashin gudanar da Tafsiri da Sallar Tarawih a azumin bana.

“Da farko, ina jaje ga dukkan wadanda suka rasa wani a sanadiyyar wannan annoba, sannan wadanda suka kamu, Allah Ya warkar da su, wadanda kuma ba su kamu ba; Allah Ya kare mu. Addinin Musulunci ba ya bukatar mai yinsa ya samu kansa cikin wata wahala. Babu kunci a wannan addini. Sau da yawa dalilai kan sa abubuwan da aka haramta su zama halal. Wannan hali da aka samu kai a yanzu Sallar Juma’a ma da ta jam’i duk an dage su a wasu wurare kuma wannan ya yi daidai.

“Kuma shari’a ba ta ce dole sai mutum ya je masallaci ba Allah zai karba. Allah ba a masallaci kawai Yake ba kuma Allah ba sai a masallaci Yake karbar addu’a ko ibada ba.

Hadisin da aka samu daga Jabir dan Abdullahi, wanda Bukhari ya ruwaito Annabi (SAW) ya ce an sanya mana  kasa ta zamana masallaci, ta zamana mai tsarki. Ma’ana, duk duniya ko’ina ka samu wuri za ka iya yin Sallahýko babu lalura,” inji shi.

Mutane sun barke da kuka wajen Tafsirin Sheikh Dahiru Bauchi

Ba kamar Kaduna ba, a Jihar Bauchi al’ummar Musulmi ne suka barke da kuka lokacin da sanannen malamin nan Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bude karatun Tafsirin azumin bana a garin Bauchi.

Mahalarta karatun sun fashe da kuka ne saboda Shaihin ya shafe fiye da shekara 40 bai yi Tafsiri a Bauchi ba.

Alhaji Mahmuda Wunti dattijo mai shekara 78. Ya ce “A gaskiya da can muna zuwa wurin da Shaihi yake Tafsiri a Masallacin State Lowcost da ke nan Bauchi, lokacin babban almajirin Shaihin, marigayi Alaramma Muhammadu Bajoga ne yake ja masa baki. Gaskiya wannan abu ikon Allah ne, na ji farin ciki kwarai ganin cewa Shehu yana Tafsiri a gida; abin da na yi wajen shekara 40 ban gani ba.”

Ita kuwa Hajiya Addaji Muhammad, fashewa ta yi da kuka, ta ce a ce Shehi mutumin Bauchi ne amma duk karatun nasa sai a Kaduna za a je. “Gaskiya yin Tafsirin nasa a gida ya yi mini dadi. Shi ya sa na yi tattaki na zo har wajen don in shaida da idona.”

Mataimakin Shugaban Kwamitin Shirye-Shiryen Tafsirin, Sayyadi Tijjani Sheikh Dahiru, ya gode wa jama’a da kuma gwamnati saboda yadda ta turo jami’an kula da lafiya da suka nuna tsarin yadda jama’a za su zauna nesa da juna a wajen da ake gudanar da Tafsirin.

Ya ce a bana za a maida hankali ne wajen isar da Tafsirin ta kafofin watsa labarai, maimakon halartar dimbin jama’a.

Ya ce kwamitin ya tanadi duk abin da ake bukata ta fannin kiwon lafiya, kamar bokitan wanke hannu da abin rufe baki da hanci da kuma na’urar gwada zafin jiki, domin tantance wadanda za su shiga. Sai ya roki wadanda ba su samu wajen zama ba su hakura su koma gida, domin a samu hadin kai wajen bin dokokin gwamnati na kiyaye lafiya.

Da yake bude Tafsirin na bana, wanda ya fara karatu a cikin Suratu Ali Imrana, sura ta uku, aya na 148, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya roki jama’a su koma ga Allah kuma su guji aikata sabon Allah, wanda shi ne dalilin da Allah Ya jarrabe mu da wannan cuta ta coronavirus.

Ya ce, “an tsokani Allah da nufin wulakantar da addininsa, ta kai har a garuruwansa Masu tsarki na Makka da Madina, aka bude gidajen rawa da caca, sannan wadansu suna zagin waliyyai, wadansu suna zagin sahabbai, wadansu suna kafirta Musulmi. Duk an tsokani Allah ne, sai dai mu yi ta tuba, mu roki Allah Ya yaye mana wannan bala’i.”

Shaihin malamin ya kuma shawarci al’ummar Musulmi su yi kokari wajen bin dokokin da likitoci suke bayarwa don kariya daga kamuwa daga cutar, kamar yawan wanke hannu da rashin yin gaisuwa hannu da hannu da tsayuwa nesa da juna domin samun lafiya.

Tuni dai Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata  Bala  Abdulkadir   Muhammad a karshen taron da ya yi da limamai da sarakuna da malaman addini, ya ce bai zai rufe jihar gaba daya ba, amma ya kamata jama’a su kiyaye dokokin kiwon lafiya da likitoci suka bayar. Ya kuma kafa kwamiti da zai fito da tsarin yadda za a ba jama’a tallafi a karkashin jagorancin Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu, kafin a kai ga matakin killace jama’a idan ya zama dole.