✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda da za a san na’o’in man da suka dace da fatarmu

Mata da dama na son kulawa da fatarsu domin kawata kwalliya da adonsu. Koda mace ta ja shekaru za a ga ta dage tana kula…

Mata da dama na son kulawa da fatarsu domin kawata kwalliya da adonsu. Koda mace ta ja shekaru za a ga ta dage tana kula da fatarta domin kada tsufarta ta bayyana. A koyaushe mace na son a ce da ita yarinya. Babbar hanya mafi sauki da za mu kula da fatarmu ita ce amfani da man da ya dace da fatarmu (moisturizer). Wannan irin mai na dauke da sinadarai masu gyaran fata kuma yana kula da ruwan da ke cikin fatarmu. Kuma man na taimakawa wajen kare fuskarmu daga kunar rana (sun screen). Idan za a sayi nau’in man sai a karanta ko man na dauke da sinadarin (sun screen) kuma ya kasance (moisturizer) ne. Bambancin mai (cream da lotion) shi ne, ana amfani da man (cream) a fuska (lotion ) kuma a jiki.

•        A shafa man moisturizer a fuska kafin yin kwalliya.

•        Kada sunan kamfanin mai ya rude ku, domin akwai wanda mai ya fi ruwa yawa a cikin man shafawa. In ko kina da fata mai yawan gumi bai kamata ki yi amfani da wanda mai ya fi ruwa yawa a ciki ba.

•        In ke mai gautsin fata ce, sai ki yi amfani da man moisturizer wanda ke dauke da sinadarin mai domin samun fata mai santsi da laushi.

•        A sayi man da sinadaransu ba masu illa ga fata ba ne.

•        Kuma a sayi wanda ba kanshi sosai. Saboda nau’in mai  mai kanshi na janyo kurarrajin fata.

•        Kada a sayi nau’in mai mai kanshi, saboda kanshin na janyo kurarrajin fata.