✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dalibai ke sayen jarabawar kammala sakandare su kasa karatu a makarantun gaba

Yayin da ake kukan ilimi ya tabarbare a kasar nan tun daga firamare zuwa sakandare, inda nan ne tushen karatu, lamarain na kara lalacewa duk…

Yayin da ake kukan ilimi ya tabarbare a kasar nan tun daga firamare zuwa sakandare, inda nan ne tushen karatu, lamarain na kara lalacewa duk da kokarin da ake yi na kawo gyara.

Kukan da ake yi yanzu  shi ne na yadda ba sai dalibai sun zauna a aji ko sun koyi karatun ba za su samu takardun kammala sakandare sakamakon yadda suke sayen jarrabawar kammala sakandare ba tare da sun tsaya neman ilimi ba.

A makarantu da dama yanzu, Aminiya ta gano akan biya kudin jarrabawar WAEC da NECO a cibiyoyin jarrabawa da ake kira ‘Miracle Centers,’inda ake biyan kudi masu yawa bisa tabbacin cewa za a samu sakamako mai kyau. Yanzu abi ya kai za a iya a ba ka zabin ko ka zo ka zauna a rika ba ka amsa, ko ka yi zamanka a gida kawai, idan sakamako ya fito ka zo ka karba.

Wannan lamari na sayen jarrabawa ya taimaka wajen kara lalata ilimi, inda za a ga dalibi ya je jami’a ko makarantar gaba da sakandare ya kasa tabuka komai. Kuma hakan ke sa wadansu shiga mugun hali don neman mafita, inda dalibai mata ke bayar da kansu ga malamai ko dalibai ’yan uwansu domin su tsallake jarrabawa a manyan cibiyoyin ilimi.

Malamai da masu ruwa-da- tsaki a makarantun sakandare sun danganta matsalar kan yawan dalibai. Sun ce makarantu da dama ba su kiyaye ka’idar daukar dalibai.

A bangaren dalibai da iyayen kuwa, wadanda aka zanta da su sun ce sau da dama yaro na kaurace wa zaman aji, musamman lokacin gama makaranta saboda kawai yana da yakinin cewa iyayensa za su yi masa rajista a wuraren da ake magudin jarrabawar.

Wani malami a Makarantar Sakandaren GSS Raga da ke Kafanchan, Malam Shafi’i Jume ya ce: “Idan muka duba irin kallon da mutane ke yi wa harkar malanta a wannan lokaci da irin kirarin da ake mata na ’yar autar sana’a, za mu fahimci cewa babu kima da girmamawa a yanzu; sabanin da da ake bai wa harkar koyarwa girma da martaba. Yawancin masu shiga harkar koyarwa a yanzu ba kwararrun malamai ba ne. Da yawa ma sukan fara aikin ne a matsayin zabi na karshe saboda sun rasa aikin da suke nema kuma da zarar sun samu wani aikin a kamfani ko ma’aikata, nan da nan za ka ga sun yi watsi da koyarwar. Su ma ’yan kadan daga cikin kwararrun malaman za ka ga suna hada koyarwar da wasu sana’o’i inda hankalinsu zai rabu biyu,” inji shi.

Wata mai makaranta mai zaman kanta da ta bukaci a sakaye sunanta ta ce batun amfani da cibiyoyin cin jarrabawar WAEC ko NECO a yanzu ba ya tsaya ne kawai ga makarantu masu zaman kansu ba.

“Wannan ko a makarantun gwamnati yanzu akwai masu taimaka wa dalibai bayan sun amshi kudinsu, don haka in har gyaran ake so a yi, to gaba dayan makarantun za a tantance na gwamnati da na masu zaman kansu kuma kowa ya san lamari ne da ba boyayye ba,” inji ta.

Wani malami a Abuja cewa ya yi, “Wadansu malaman sun fi dacewa da a kira su da  “Cheaters (macuta) maimakon Teachers (malamai)” saboda suna cutar da dalibansu ne kawai ba karantar da su ba, kuma su kansu sun samu aikin ne ta bayan fage, ba don sun cancanci aikin ba.”

Malam Mubarak Muhammad, malamin wata makarantar gwamnati a Abuja ya ce sha’anin makaranta a yanzu ya fi kama da a kira shi “zuwa makaranta ba karatun ba.” Ya ce ita kanta gwamnati ba da gaske take yi ba, idan aka yi la’akari da kudin da take ware wa sashin, inda ya yi misali da Naira biliyan 46 da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a matsayin kasafin kudin badi (2020) ga bangaren ilimi, alhali ya ware wa bangaren Majalisar Dokoki ta Kasa sama da Naira biliyan 100, duk da cewa mambobinta ba su wuce 400 ba.

Ya zargi bangaren sa ido a makarantun sakandaren gwamnati “Education Kuality Assurance” da cewa ba ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata, inda ya yi zargin cewa da yawa daga cikin jami’an bangaren suna nuna kwadayi kan na-goro lokacin da suka kai ziyarar sa-ido a makarantun, maimakon ladabtar da su.

A martanin da suka mayar, sashin kula da makarantun sakandare na Shiyyar Suleja a Jihar Neja da ba su bayyana sunansu ba, saboda ba su samu sahalewar hedikwatarsu da ke Minna a kan haka ba, sun musanta zargin da ake yi wa sashen kan amsar na goro.

Wani jami’i a bangaren ya ce, matsalar da ke faruwa a makarantu a yanzu matsala ce da ta shafi dukkan fannonin rayuwa a kasa baki daya. “Muna kai rangadi a makarantun a koyaushe kuma muna gabatar da  korafi gare su tare da ba su lokaci don su cika ka’ida.

Dokta Abu Abubakar shi ne Daraktan Sashin Guraben Ci gaba da Karatu a Kwalejin Ilimi ta Abuja da ke Zuba, a zantawarsa da Aminiya kan yadda manyan makarantu ke fama da dalibai marasa inganci, ya ce lamarin na mayar da hannun agogo baya a sha’anin makarantun, saboda wadansu daliban ba sa ma gane abin da ake yi musu.

Ya ce matsalar tana faruwa ce duk da cewa takardun da daliban suka gabatar kafin a ba su gurbin karatu, na dauke da kyakkyawan sakamako na akalla darusa 5, kamar yadda ka’ida ta bukata. Ya ce hakan na nuni da cewa akwai matsala a kan sahihancin takardun.

Ya ce idan lamarin ya ci gaba, akwai yiwuwar kasar nan za ta fuskanci matsalar rashin kwararrun malamai da na sauran bangarorin aiki a nan gaba.

Malam Mustafa Kabiru da ya kammala makarantar nakasassu ta Rashid Adisa Raji da ke Sakkwato, ya ce ya je makarantar ce domin ya samu jarrabawa mai kyau duk da cewa yana da lafiya, saboda ana samun sakamako mai kyau a makarantar.

Wani shugaban makarantar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “A dukkan makarantun da muke da su a Jihar Sakkwato na gwamnati da masu zaman kansu ba wadda ba a biyan kudi a samu sakamako mai kyau, wato “Miracle Centres,” ana ware daliban da iyayensu suka biya kudi kamar Naira dubu 15 zuwa dubu 20. Akwai wadanda ke fita wajen makaranta su rubuta jarrabawa a dawo da su, akwai wadanda sai mai kula da jarrabawa ya gama aikinsa ma sannan su kuma za a sanya nasu.”

Malamin ya ce lokacin jarrabawa kaka ce ta samun kudi ga shugaban makaranta da malamai masu kula da jarrabawar da aka turo a cibiyoyin shirya jarrabawar. “Yanzu yaran talakawa ne kawai ba su iya cin jarrabawar kammala sakandare,” inji shi.

Dokta A’isha Bawa malama a Sashen Tarihi na Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato. Ta bayyana takaicinta kan yadda ake samun daliban da ke shigowa jami’a ba su san komai ba, su dai muradinsu su mallaki shaidar digiri kamar yadda suka mallaki ta sakandare, babu ruwansu da kare shaidar karatun.

Wadansu dalibai sun bayyana wa Aminiya cewa a wasu makarantun, akan ce musu matukar ba su ba da na kati ba ko sun ci jarrabawar ma ba za a ba su ba.

Wani dalibin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce wata makaranta ce ya je a Jihar Akwa Ibom rubuta jarrabawa sai aka ware su aka ce wadanda ba ’yan asalin jihar ba ce, su kawo Naira 5,000 kowannensu, wanda bai bayar ba kuma zai ga sakamakon da zai samu. Ita ma wata dalibar cewa ta yi “Na gano take-taken malaminmu ne a makarantar sakandaren da nake yi, na yana son sai ya cimma burinsa a kaina sannan ya taimaka in samu sakamako mai kyau. Sai na hada baki da kawayena muka yi masa kofar rago muka kama shi bayan na nuna masa a shirye nake in yi duk abin da yake so. Haka muka kai shi kara gaban shugaban makarantar, aka ladabtar da shi sannan Kungiyar Iyaye da Malamai ta ce dole sai an kore shi. Haka kuwa aka yi aka samu lafiya.”

A Jami’ar Kalaba, Tsangayar Ilimi akwai malamin da idan jarrabawa ta zo yana umartar shugaban daliban aji cewa ya rubuta sunayen dalibai ya karbi Naira 3,000 hannun kowa, wanda ya bayar ya ci jarrabawa wanda bai bayar ba kuwa ya fadi.

Wani dalibi da ya gama a Jami’ar Kalaba ya ce, “Sai da na biya Naira dubu 40 a asusun ajiyar malaminmu bayan an hada karya da gaskiya aka ce ban ci ba, ko in sake ko in ba da wani abu. Muka yi ciniki na biya.”

Akwai laifin iyaye a lamarin – Hukumar JAMB

Da Aminiya ta tuntubi Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu  (JAMB), ta ce akwai laifin iyaye a lamarin, inda suke ba ’ya’yansu kudi domin su biya a irin wadannan makarantu ko cibiyoyin jarrabawa ba tare da sun damu da bincikar karatun yaran ba.

Kakakin Hukumar, Dokta Fabian Benjamin ya ce su a wajensu, babu wata cibiyar magudi da ake kira ‘Miracle Center.’

“Mu a tsarinmu babu irin wadannan cibiyoyi. Kawai dai mun san akwai masu kokarin yin magudin jarrabawa, amma duk makaranta ko cibiya da muka kama da laifin magudi ko taimakon magudi, mukan kulle cibiyar daga tsawon watanni zuwa shekara biyu. Ko kuma mu rike wannan jarrabawa.

“Idan kuma muka kama iyaye ko dalibai da suke zuwa irin wadannan makarantu suna hada baki da makarantun, muna gurfanar da su a kotu ne. Yanzu haka akwai da yawa da muka kama da suke kotu, wadansu ma mun kama su ne da laifin yin rajistar jarrabawa biyu,” inji shi.

Dokta Fabian ya kara da cewa a hukumance ba sa jin dadin yadda wadansu ke amfani da magudi wajen cin jarrabawa, “Amma yanzu mun yi tsare-tsare masu kyau da zai yi wuya a yi magudi ba tare da mun kama mutum ko makarantar ba. Don haka muke ba iyaye da dalibai shawara da su malaman maimakon su rika kashe kudinsu wajen neman hanyar magudin jarrabawa, kamata ya yi iyaye su lura da karatun yaransu, su goya musu baya su samu ilimi mai inganci,” inji shi.