✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda direba ya hada baki aka yi garkuwa da fasinjojinsa a hanyar Kaduna

Wasu da aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun bayyana yadda suka fada hannun masu garkuwa da mutane don karbar kudin…

Wasu da aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun bayyana yadda suka fada hannun masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa a kan hanyar, inda suka zargi dereban da ya dauke su a motar haya daga gareji, cewa yana da hannu a lamarin.

Biyu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, wadanda suka zanta da wakilinmu a Abuja, sun ce lamarin wanda ya faru a kwanakin baya ya ritsa da su ne ’yan mintoci kaliilan bayan sun baro garejin da ke kusa da gadar sama, a wani waje da aka fi sani da suna “Abuja Junction” da misalin karfe 6 na yammacin ranar da lamarin ya faru, da niyyar zuwa Abuja.

Sun yi bayanin cewa akwai mutum hudu a cikin motar tasu baya ga direban. “Sai dai bayan tafiya ta dan lokaci kadan daga garejin, sai muka cin ma shingen masu garkuwa da mutane a kan hanyar suna ta harba bindiga. Bayan mun tsaya sai suka bukaci da mu fito tare da wasu mutum hudu daga wata motar, suka karbe wayoyinmu tare da sauran abin da ke aljihunmu sannan suka yi ta tafiya da mu ta cikin jeji har zuwa kamar karfe 12 na dare kafin mu ka iso wani sansani. A can ne muka yi ta zama na tsawon kwana uku kafin suka sako mu bayan sun karbi kudin fansa,” inji su.

Daya daga cikin wadanda suka yi zantawar da wakilinmu ya ce macen da aka dauke su tare daga mota guda, ba a karbi komi daga wajen mutanenta ba a matsayin kudin fansa kasancewar ta rasa wayarta tun a lokacin da ta shiga rudewar kai bayan haduwa da barayin kuma a dalilin hakan ba su samu zarafin zantawa da danginta ba bare a yi batun kudin fansa har zuwa lokacin da aka sake su tare.

Ya ce asirin dereban nasu ya tonu ne kasancewar wani dan uwan matar da ya rakata zuwa gareji a lokacin tafiyar, ya dauki lambar motar direban tare da shaida fuskarsa, sannan bayan da aka sako su sai ’yan uwan matar suka shigar da kara a ofishin ’yan sanda kan zargin ba su gamsu da yadda direban ya tafiyar da lamarin fasinjansa ba a lokacin tafiyar.

“Yan sanda sun kai samame a garejin, inda suka yi sa’ar samun direban sannan suka bukaci takardan sunayen fasinjan motar da suka yi tafiyar tare daga hannun ’yan yuniyan gabanin suka garzayo da shi zuwa ofishinsu. “Bayan an kai shi ofishin ’yan sanda, da farko an tambaye shi a kan yadda tafiyar ta kasance. Da farko ya yi ikirarin cewa ya sauke fasinjan a garejin motoci na Zuba a daren ba tare da fuskantar wata matsala ba, sai dai bayan ’yan sanda sun shigo da matar a gabansa, sai ya ce sun fada hannun ’ya fashi a lokacin tafiyar sai dai shi ya kubuta sannan ya sake komawa ya dauki motarsa daga wajen.

“Sun sake tambayarsa ko ya kai maganar gaban wani ofishinsu, nan take ya ce bai kai ba, kuma a dalilin hakan aka tsare shi.”

Malam Kasim Shu’aibu wanda ke matsayin limami a garin Gwagwa Abuja, inda daya daga cikin wadanda suka fada hannun masu garkuwa da mutanen ke da zama, shi ne ya kai kudin fansar da aka bukata kafin aka saki mutumin. Ya ce bayanin da suka samu shi ne, daga bisani ’yan uwar matar sun janye karar a gaban ’yan sanda don gudun fadawa wata rigimar kuma a dalilin hakan aka saki dereban.

Ya ce bayan kwana guda da faruwan lamarin masu garkuwa da mutanen sun buga waya ga wani da ke gida daya da mutumin da aka sacen, inda suka fara maganar kudin fansa, kafin daga bisani aka mika ragamar tattaunawar a hannunsa.

“Da farko sun nemi Naira miliyan daya tare da kashedin cewa sun ba mu zuwa washegari da mu gabatar da kudin ko su dauki mummunan mataki a kansa. Sai dai bayan na yi masu bayani a kan matsayin mutumin na kasancewa mara abin hannu, sun amince za su karbi Naira dubu dari shida, kuma abin da muka kai masu ke nan.

“Na isa inda suka bukaci a kai masu kudin tare da wani dan uwa a wani waje da ake kira Sabon-Gayan, a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Na bar abokin tafiyar tawa a wani masallaci da ke kusa da wani gidan mai, sannan na sanar da su isowa ta ta waya.

“Sun bukaci da na kara tafiya zuwa wani kauye da ke gaba kuma a can ne suka nemi sanin irin launin kayan da na saka sannan suka umarce ni da na ketara hanya da misalin karfe daya na rana. Sun bukaci da na tsaya na dan lokaci za su turo wani dan acaba ya zo ya dauke ni. Kuma ba a jima ba sai ga shi ya iso ya tinkaro inda nake tsaye, tare da tambayar ko ni ne wanda ke jiransa, na ce masa ni ne, sai ya dauke ni muka shiga cikin jejin.

“Mun yi ta tafiya kamar ta kilomita 10 kafin muka tsaya a wani waje mai gada da ta raba hanyar jirgi da ta mota. Mun bi ta kan gadar tare da tafiya kadan sai dan acaban ya tsayar da babur dinsa ya yi musu waya. A nan ma sai suka bukaci da mu kara yin gaba kadan sannan muka tsaya. Bayan kamar minti 5 sai ga mutum uku sun fito daga jeji, kowannensu dauke da bindiga da kuma safar fuska, daya ya tsaya ta hagu da mu daya ta dama sai kuma gudan ya tinkare mu ya karbi kudin.

Ya ci gaba da cewa, “da farko ya nemi sanin ko kudin ya cika cif, na tabbatar masa cewa sun cika. Mai mashin ya juya zai koma sai suka tsayar da shi tare da bukatar ya koma da ni. Sun bukaci da ya nemo karin wasu masu acaba 2 su dawo wajen da misalin karfe 6 na almuru don daukar mutum 6 da za su saka, ciki har da dan uwan namu, tare da umurtarsa da ya kira su ta waya kafin su taso.

“Bayan dawowa ta bakin hanya na samu wasu da su ma suka kai kudin fansar wasu daga cikin wadanda aka kaman, kuma suna jiran lokacin almurun ya yi a je a dauko ’yan uwan nasu. Sai dai koda lokacin ya yi bayan mai babur ya dawo sai ya ce ya yi ta neman su ta waya amma bai same su ba kuma koda na duba lambar sai na gane cewa iri daya ce da ta wa.

“Da misalin karfe 11 na dare ne na samu nasarar samun su a waya, sai suka ce a yanzu babu batun sai masu babura sun zo, kasancewar sun riga sun hannunta dan uwan namu tare da sauran wadanda suke rike ga wasu mutanensu da za su rako su zuwa bakin hanya. Daga baya sai ga kiran waya ta dan uwan nawa, inda ya yi amfani da layinsa na waya da suka mika masa, ya ari wayar ’yan banga na kauyen ya kira ni da misalin karfe daya na dare,” inji Malam Kasim.

Ya ce bayan sun hadu a daren sun kwana a kauyen, inda daya daga cikin ’yan banga na kauyen ya kai su gidansa sannan bayan wayewar gari suka kama hanya suka dawo Abuja.

Yunkurn jin ta bakin dan uwan nasa da aka yi garkuwa da shi mai suna Tanko Dako bai samu nasara ba, kasancewar ya ce har yanzu yana fama da matsalar rudewar tunani da ya samu kansa a ciki tun bayan faruwar lamarin kuma ba zai so ya yi wani bayani a kai ba.