✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dokar kulle ta tayar da kura tsakanin Kano da Kaduna

Matakin da gwamnatocin jihohin Najeriya suka ɗauka na rufe iyakokinsu domin hana yaduwar cutar coronavirus ya kara tayar da kura. Cacar baki ta kaure tsakanin…

Matakin da gwamnatocin jihohin Najeriya suka ɗauka na rufe iyakokinsu domin hana yaduwar cutar coronavirus ya kara tayar da kura.

Cacar baki ta kaure tsakanin ‘yan jihohin Kano da Kaduna, a shafukan zumunta bayan gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufa’i ya ce ranar jajibirin karamar Sallah zai tare a iyakar jihar da makwabciyarta Kano da nufin hana shigo da cutar daga Kano.

Ko kafin nan, gwamnatin Kaduna ta yi zargin cewa yawancin masu cutar COVID-19 da aka samu a jihar na da tarihin tafiye-tafiye zuwa jihar Kano.

Batun zuwan El-Rufa’i iyakar jiharsa da Kano ya haifar da mahawara da zolayar juna tsakanin ‘yan jihohin biyu da magoya bayansu, musamman a Twitter.

Mahawarar mai taken #KadunaVsKano ta yi tashe matuƙa inda ‘yan kowanne daga cikin jihohin masu makwabtaka da juna ke ganin jiharsu ce ta fi.

Ga wasu kalubalen da @Sirtopshadow ya yi wa ‘yan Kaduna, wanda ya  aka yi ta mahawa a kai:

“An ba ‘yan Kaduna sa’a 12 su ba da amsa.

“A bincika a Kachia da Birnin Gwari da Chikun ko akwai kamar wadannan.

@adamdanfadal ya ce:

“Ciniki ya kaya bayan Aliko Dangote ya sayi Kaduna da mutanen cikinta sannan ya umarci hukumomi da kar su bari kowa ya fice daga garin.

“Barka da samun karin wata karamar hukuma a Kano.”

“Ga yadda ‘yan Kaduna ke yi sadda suka fara zuwa Kano”, inji @BayeroHydar

 

A martanin ‘yan Kaduna, @harmees__ ya ce:

Ku zaba cikin hikima.

DJ AB – yi liking

Nomisgee – yi retweeting.

“Ga bambancin tsakanin Government House (Kaduna) da Gidan Gwamnati (Kano)”, inji @ahmad_abulqadir:

@SirTopSadow ya ce wa Kanawa, “Shin kuna da kamar wadannan?”