✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda farashin kayan abinci ya yi tashin gauron zabi a Taraba

Farashin buhun shinkafa da na masara ya karu na N5,000 a cikin mako daya

Farashin kayan abinci na ci gaba da hauhawa a Jihar Taraba duk da cewa manoma na samun karin yabanya da kuma albarka ta amfanin gona da suke girbewa.

Binciken da wakilanmu suka gudanar ya gano cewa, a halin yanzu ana sayar da buhun masara a kan farashin N22,000 sabanin N17,000 da aka sayar a makon jiya.

Ana kuma sayar da buhun shinkafa ’yar gida tsohuwar ajiya a kan N42,000 sabanin yadda aka rika cin kasuwarta a kan N37,000 a makon da ya gabata.

Haka kuma ana sayar da buhun masara sabuwar girbi a kan N16,000 sabanin N6,000 da aka sayar a bara daidai wannan lokaci.

Binciken ya kuma gano cewa, farashin wake, gero, doya da kuma garin Fulawa, ya yi tashin gauron zabi da kimanin kaso 25 cikin 100.

Karuwar farashin kayan hatsin na zuwa ne a yayin da manoma a fadin jihar suke ci gaba da samun yabanyar amfanin gona.

Sai dai wakilanmu sun gano cewa tsadar farashin na da nasaba ne da yadda manoma a fadin jihar suka tsiri boye sabbin amfanin gonar da suka girba musamman duba da yadda ake jidar amfanin daga kasuwanni irin su Mutum Biyu, Iware, Garba, Chede Tella da Sabongida zuwa wasu garuruwa.