Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yadda garin Aliero ya fito da Jihar Kebbi a idon duniya kan noman albasa

Wata kasuwar albasa
Wata kasuwar albasa

Garin Aliero da ke Jihar Kebbi ya yi suna kan noman albasa da harkokin kasuwanci, yayin da aka san Yawuri da noman shinkafa, Argungu da kamun kifi, Kamba ta yi suna kan kasuwancin kasa da kasa; saboda iyaka da Jamhuriyar Nijar da Benin.

Garin Aliero ya zama wata fitila a idon duniya kan noman albasa musamman kasashen Afirka. An san Aliero ne kan noman albasa da kasuwancinta a nan Najeriya da kasashen Afirka.

ADVERTISEMENT

Idan bako ya ziyarci garin  Aliero zai fahimci cewa babbar sana’ar mutanen garin Aliero ita ce noman albasa da sayar da ita a tsakanin matasa da dattawan gari.

Kasuwar albasa ta garin Aliero, kasuwa ce da a duk jihohin Arewa maso Yamma da sauran jihohin Najeriya babu irinta, ta fuskar hada-hadar albasa.

ADVERTISEMENT

Sakamakon haka ne dukkan ’yan kasuwa da manoman albasa na kananan hukumomin jihar da makwabtanta ke kai albasar da suka noma kasuwar garin Aliero; domin saye da sayarwa.

Mutanen garin Aliero na shuka iri daban-daban na albasa a watan nan na Agusta, bayan sun girbe gero a gonakinsu. Daga watan Disamba zuwa watan Janairun sabuwar shekara ne lokacin kakar cire albasar.

Gwamnatin Jihar Kebbi, karkashin tsohon Gwamnan Jihar Sanata Muhammadu Adamu Aliero, ta yi yunkurin gina Babbar Kasuwar Albasa ta Kasa da Kasa a garin Aliero. Ginin babbar kasuwar albasar an faro shi, amma daga baya sai aka yi wa aikin rikon sakainar kashi; bayan kare wa’adin gwamnatin Aliero.

Sai dai bayan wasu shekaru, gwamnatin Abubakar Atiku Bagudu ta gina wata karamar kasuwar albasa a Aliero,  don bunkasa kasuwancin albasar da nomanta a garin. Kafin gina karamar kasuwar,  ’yan kasuwar na sayar da albasar ce a kan wata babbar hanyar mota a cikin garin.

A cewar wani manomin albasa a Aliero, ayyukan manomin albasa, ba su tsaya ga aikin noma albasa ba kawai; har da cinikayyarta a kasuwar  Aliero, ya ce suna taruwa domin gudanar da cinikayyar buhunan albasa.

“Idan manomin albasa ya kawo buhunansa na albasa daga garin Yawuri, za mu saya a hannunsa, don mu sayar a kasuwar Aliero. Haka kuma kasuwancin albasa a Aliero, babban kasuwanci ne gare mu. Dalili shi ne kasuwa ce wadda mutane daga wurare daban-daban na kasar nan ke zuwa domin sayen albasa mai yawa a kullum. Haka daga jihohin Yarbawa da na Ibo sukan sayi buhunan albasa da ke cika manyan motoci zuwa Legas, Ibadan, Ebonyi, Imo da sauransu. Har ila yau, daga Jamhuriyar Benin da Nijar dukkansu na zuwa wannan babbar kasuwar albasa ta Aliero,” inji wani manomin albasa.

Kasuwar albasar kan fara ci ne da misalin karfe tara na safe zuwa karfe shida na yamma.

Wani dan kasuwar albasar da kuma nomanta, Malam Muhammadu Tukur ya ce, wannan shekarar ya noma buhun albasa fiye da 40 a gonarsa da ke garin Aliero. Ya kuma saye buhu 56 na albasar daga garin Yawuri, domin ya sayar a kasuwar ta garin Aliero.

Ya ce: ‘‘Gaskiya ce mutanen Aliero su ne suka fi kowa noman albasa a kasar nan; amma garin Yawuri da kuma Gada a Jihar Sakkwato su ma suna iya noma albasa fiye da garin na Aliero.”

Ya ce: ‘‘Mutanen garin Aliero sun riga kowa fara noman albasa da sayar da ita a kasuwa; kafin daga baya mutanen Yawuri da Gada a su gane cewa akwai arziki a cikin noman albasa.”

Farashin buhun albasa dai ya soma ne daga Naira 11,000 zuwa zuwa 15,000. Koda yake, a bara, farashin albasar ya fadi kasa warwas; har ya kai aka sayar da buhun albasa Naira 5,000. A shekarun baya da albasa ke da daraja har Naira 30,000 zuwa 35,000 an sayar da buhunta.

Manoman albasa, sukan iya noma buhu 10, 30, 50, 80 har zuwa buhu 200 a garin na Aliero. Haka kuma wadansu manoman albasa a wasu yankunan Jihar Kebbi da kuma ’yan kasuwar albasa suna kawo tasu albasa a garin na Aliero.

Malam Tukur ya ce ‘‘Ni dai na cire buhun albasa 40 a gonata na kuma na sayi buhu 56 daga hannun wani manomi daga Yawuri. Idan ka dubi kasuwar nan za ka ga tireloli tsaye ciki da wajen kasuwar, inda suka dauko buhunan albasa daga wasu yankunan Jihar Kebbi, za su wuce zuwa wasu jihohin Arewa da Kudu na kasar nan.  Wasu tirelolin za su dauki albasar ce zuwa kasashen Jamhuriyar Nijar da Benin. Dan kasuwa daya na iya sayar da buhun albasa 20 zuwa 60 a kowace rana.”

A yayin da wakilinmu ya kai ziyarar gani da ido a kasuwar albasar ta Aliero, ya tarar ana ta hidimar saye da sayar da buhunan albasar. Haka hanyoyi shida na shiga cikin kasuwar da wahalar gaske kafin mutum ya samu hanyar wucewa domin shiga cikinta; sakamakon yadda motocin tirela ke sauke buhunan albasa da daukarsu domin fita da su zuwa wasu jihohin kasar nan.

Daya daga cikin ’yan kasuwar albasa a kasuwar, Malam Suleiman Aliero, ya bayyana cewa: ‘‘Yadda ka ga yanayin kasuwar da ta cika da buhunan albasa da masu saye haka kasuwar ke ci a kullum.  Yawan motoci da kuma masu sayen buhunan albasa da manoma masu kawo albasa domin sayarwa suna shan wahala wurin shiga kasuwar saboda yawan motoci da mutanen da ke shiga kasuwar. Saboda haka babu wani abin da za mu iya yi domin rage yawan jama’a ko yawan motoci masu shiga kasuwar. Wannan ita ce babbar kasuwar albasa a Jihar Kebbi.”

“Haka kuma ban taba jin wata kasuwar albasa da ta yi yawa ko girman wannan ta garin Aliero ba a duk fadin Najeriya,” inji shi.