Da Dumi Dumi

Yadda garkuwa da mutane ke sa jama’a sayen bindigogi don kare kai

Gwamna Aminu Masari da marigayi Buharin Daji lokacin shelanta afuwa ga ’yan bindiga a Katsina

Ta’azzarar ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a sassan Jihar Katsina tana daukar sabon salo inda a ’yan kwanakin nan neman makamai da suka hada bindigogi hadin gida da adduna da takubba da kuma maganin bindiga dona kauce harbin kisan harbin bindigar.

Aminiya ta gano bewa sakamakon tsoron abin da ka iya zuwa ya zo, mutane na yin doguwar tafiya don nemo makaman wadanda ake sayar da su a boye ga masu sha’awar saya. Yayin da suke dada zage damtse don sayen maganin bindiga.

Game da bindigogi kuwa binciken Aminiya ya gano bindiga kirar gida ana sayar da ita kan Naira dubu hudu, yayin da wadda aka inganta ta take kaiwa Naira dubu bakwai zuwa dubu tara. Galibin wadannan bindigogi ana amfani da fulogin babura ne ko janareta ko kuma ’ya’yan borus, kuma bayanai sun nuna suna da matukar bata wanda aka harba fiye da bindiga kirar AK 47. Kuma irin wadannan bindigogi ne ’yan sintiri ko ’yan banga suke amfani, kafin yanzu mutane su kama sayensu don kare kawunansu.

Duk inda aka samu labarin mai sayar da maganin harbin bindiga yanzu za a ga mutane suna tururwar zuwa don saye tare da gwada aikinsa. Magungunan bindigar wadanda akasari layu ne suna matukar cin kasuwa inda mutane suke haba-haba su ji labarin inda ake sayar da su. Su kuma masu sayar da layu ko maganin bindigar akasari suna yawo ne a kan babura ko cikin motpci suna tallata kayayyakinsu a ranakun kasuwanni ko a kan tituna.

Wadannan layu ko magani ana sayar da su ne tsakanin Naira 1,500 zuwa 2,500 kamar yadda wakilinmu ya samu bayani.

ADVERTISEMENT

Kuma ana amfani da wadannan layu ne bisa yakinin mutum da fahimtarsa, inda a wasu lokuta suke haifar da kokwanto, saboda wadansu sukan samu nasara, wadansu kuma ba su samun nasararsu.

A kwanan nan ma sai da wadansu suka rasa rayukansu a lokacin da suke kokarin gwada karfin wannan maganin bindiga a kauyen Kwari da ke yankin Farafara a Karamar Hukumar Jibiya da ke jihar.

Daya daga cikinsu mai suna Abu Sadara ya rasa ransa ne a lokacin da yake gwada maganin bindigar da ya saya, yayin da Mani Dogo-Dogo ya jefa rayuwarsa cikin hadari bayan bindigar ta yi masa illa inda aka kwantar da shi a asibiti. Marigayin da kuma Dogo-Dogo da wadansu mutum biyu, sun tafi har Karamar Hukumar Kankara ce domin su sayo maganin bindigar, kuma bayan da suka dawo kauyensu sai takaddama ta kaure ka maganin da aka sayo inda wajen gwaji aka kai ga rasa rai da kuma samun mummunan rauni.

Shi kuwa Rufa’i Batsari, wanda a kwanakin baya ya sayo maganin bindigar, ya ce dalilinsa na sayen maganin shi ne yak are kansa daga masu kai musu hari, inda ya ce “Na saye shi ne saboda yawan harin da ake kai wa kauyenmu, kuma ina da yakinin maganin zai yi aiki.”

Game da abin yake da wannan yakini duk da cewa wadansu suna mutuwa, Rufa’i Batsari ya ce, “Mutuwa tana kan kowa kuma amfani da maganin ba yana nufin ba za ka mutu ba ne, amma muna da tabbacin kariya ce.”

Da Aminiya ta tuntubi Dokta Musa Ahmed Jibrin, na Sashin Nazarin Tarihi da Tsaro a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa (UMYU) da ke Katsina, ya ce an fara amfani da dokar takaita bazuwar bindigogi ne bayan Yakin Basasa, inda aka kyale mutane su yi amfani da bindigar gida wato harbi-ruga don yi farauta, kuma kalilan din mutane ne suke neman lasisi a kansu daga hukumar ko a wancan lokaci.

Ya ce, gwamnati ta fadi balo-balo cewa irin wadancan bindigogi kirar gida an amince ne kawai a yi amfani da su don farauta amma ba da sunan kare kai ba, inda ya ce daga lokacin Yakin Basasa zuwa yanzu an rika samun sauye-sauye kan fasalin tsaro.

Ya dora alhakin yaduwar bindigogi a hannun jama’a kan rikicin kasar Libya da ayyukan ’yan ta’adda a yankin Afirka ta Arewa da kuma rashin tsaro a kan iyakokinmu, wanda hakan ya sa mutane suke samun sauki shigowa da bindigogi cikin kasar nan ta hanyoyi daban-daban da ba a kula da su yadda ya kamata, yana mai cewa iyakokin kasar nan a wangale suke kuma hakan ba abu ne mai kyau ba, domin idan ba a kula da iyakoki komai zai iya faruwa.

 Gwamna Aminu Masari da marigayi Buharin Daji lokacin shelanta afuwa ga ’yan bindiga a Katsina
Gwamna Aminu Masari da marigayi Buharin Daji lokacin shelanta afuwa ga ’yan bindiga a Katsina

Dokta Musa Jibrin ya ce, a Katsina ko’ina mashiga ce, kuma mutane suna kai da kawo ba wata matsala dauke da kayayyaki ba tare da ana bincikarsu ba inda ya ce, “Wannan gazawa ce babba daga bangaren gwamnati da jami’an tsaro da suka kasa magance matsalar da kuma barazanar ’yan bindigar.”

Dokta Jibrin ya ce “Sakamakon karuwar ta’asar ’yan bindigar, mutane sun fahimci cewa sai yaushe za su farka su fuskanci barazanar da wadannan ’yan bindiga suke yi musu ta neman shafe su daga bayan kasa, don haka a fakaice saboda harkokin kasuwanci da kusancinsu da Jamhuriyyar Nijar da Libya sai mutane suka fara sayen bindigogi da sunan kare kai.”

Ya ce, “Gaskiyar magana mutane a kashin kansu ba su iya magance kalubalen rashin tsaro ba, hatta jami’an tsaro ba za su iya su kadai ba, domin ka kawo soja ko dan sanda daga Benuwai ka nemi ya shiga dajin Batsari ya yi yaki, tilas ne ka hada da masu leken asiri ’yan yanki a hada hannu da mazauna yankin.”

A cewarsa babban abin da damuwa shi ne abin da zai biyo baya bayan an kawo lamarin ya kwanta alhali ga bindigogi a hannun mutane da dama, “abin zai kasance ne kamar Libya, kashe-kashen mutane zai ci gaba a tsakaninmu,” inji shi.

Ya ce “Mallakar wadannan bindigogi zai kara jawo cutarwa fiye da amfaninsu ga masu tasowa. Don haka gwamnati ta hanzarta mikewa tsaye ta sauke nauyin da ke kanta don fuskantar wannan matsala, domin idan aka magance wannan matsala abin da zai biyo baya yana iya fin na yanzu muni.”

“Mutane su daina yaudarar kansu cewa za su iya fuskantar wadannan ’yan bindiga gaba da gaba, ba za su iya ba, yanayin bindigoginsu da adadinsu ba za su iya fuskantar wadannan ’yan bindiga ba, suna kawo hari ne cikin jerin gwano, sukan zo ne mutum uku a kan babur daya tare da babura fiye da 50, akalla mutum 150 ke nan dauke da isassun makamai, bindiga kirar AK47, yayin da ’yan banga ke da harba-ka-ruga,” inji shi.

Wani malamin jami’a, Magaji Saleh na Sashin Nazarin Halayyar dan Adam na Jami’ar Tarayya da ke Dutse, ya ce akwai alfanu da rashin alfanu game da batun na mallakar bindigogi don kare kai. Ya ce, alfanun hakan zai ba jama’a damar ji a jika cewa za su iya kare iylalan gidansu, kuma hakan zai tallafa wa kokarin jami’an tsaro kuma ya hana ’yan bindigar kai wa jama’a da dama hare-hare. “A wannan bangare hatta wadanda ba su da bindigogin za su samu kariya, saboda ’yan bindigar ba su san wane ne yake da ita da wanda bai da ita ba. Kuma da ’yan bindigar da wadanda suka mallaki bindigogi bisa doka ba wanda ya samu cikakken horo kan yadda ake amfani da ita. Dukansu ’yan dagaji ne don haka za su ji tsoron kai wa juna hari,” inji shi.

Sai dai ya ce, inda rashin alfanu zai bayyana shi ne hakan zai kawo karuwar aikata miyagun ayyuka, saboda mallakar bindigogi yana nufin karuwar miyagun ayyuka ne, musamman idan suka fada hannun, marasa kan gado, kuma wadanda ba su mallaki bindigogin ba, za su iya samunsu cikin sauki, tunda mutane da na iya neman a ba su lasisinta wanda hakan zai ba wadanda bas u cancanta ba damar su mallake ta.

“Hakan zai raunata dokar takaita mallakar bindiga a Najeriya, wanda shi ne babban dalilin da ya sa kashe-kashe da kisan gilla ke karuwa a Yammacin Duniya. Bilhasali ma sassauukar dokar mallakar bindiga ce silar kai harin ta’addancin da ya gudana a New Zealand na baya-bayan nan, wanda hakan ya sa kasar take shirin tsaurara dokar mallakar bindiga,” inji shi.

Ya ce karuwar bindigogi a hannu jama’a zai bayar da damar kashe-kashe hatta a cikin dangi tare da musguna wa jama’a, inda ya kawo misali da batun wani mai suna Muhammaed na Zoo Road a Kano, wanda ya kashe iyayensa da dan uwansa. “Kada a manta wadansu mutane suna raye ne saboda kisa zunubi ne, yayin da wadansu suke raye saboda tsaurara dokar hana kisan kai,” inji shi.

Shi kuwa Sani Sa’adu babban mai bayar da shawarwari da lallashi a Sashin Harkokin Dalibai na Jami’ar UMYU da ke Katsina ya ce, tururuwar da jama’a ke yi don neman maganin bindiga akwai bukatar masu ruwa-da-tsaki su dauki mataki don dakile abin da zai shafi tunanin jama’a. Ya ce akwai bukatar a kara fadakar da jama’a su guji irin wannan, domin ya saba wa hankali da tunani kuma ba shi ne mafita ba

“Wannan barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar shi kansa mutumin, kuma ya wajaba hukumomi su shigo cikin lamarain, domin daga abin da na lura, yadda ake tururuwa ana zuwa neman maganin bindigar abin ya wuce hankali,” inji shi.

A bangaren gwamnatin jihar kuwa, yarda da wadannan layu ko magungunan bindiga abu ne mai tayar da hankali kuma zai dada jefa jama’a cikin matsala. Shugaban Kwamitin Yaki da Satar Shanu kuma Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Mustapha Inuwa ya ce, a baya-bayan nan mutane sun bullo da wasu halaye na neman layu da magungunan bindiga, kuma abu kadan sais u tashi su ce za su shiga daji su tunkari ’yan bindigar, sai kuma ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne, layun ko maganin ba ya aiki, inda za a hallaka mutane kawai.

Ko a kwanankin baya a kauyen Wagina da ke Karamar Hukumar Batsari, karamar takaddama kan wani karamin dam ya sa mutane sun fada daji, inda aka kashe mutum 10 aka raunata wadansu da dama.

Kididdigar da aka samu daga sashin hulda da jama’a na Hedkwatar ’Yan sandan Katsina ta nuna cewa a wata biyu da suka gabata, akalla mutum 8 aka kama daga cikin wadanda ake zargin ’yan bindiga ne kuma an kwato bidigogi uku kirar AK 47 da bindigogi kirar gida guda 6 da harsasai masu rai 41.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya