✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gidan Abba Kyari na Kaduna ya kasance

’Yan aikin gidan Abba Kyari na Kaduna da makwabtansa sun bayyana matukar kaduwa da jin labarin rasuwar Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasar, wanda ya rasu ranar…

’Yan aikin gidan Abba Kyari na Kaduna da makwabtansa sun bayyana matukar kaduwa da jin labarin rasuwar Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasar, wanda ya rasu ranar Juma’a bayan ya yi fama da COVID-19.

Da wakiliyar Daily Trust ta ziyarci gidan wanda ke Raba Road ta samu babbar kofar shiga harabarsa a kulle, kuma ba kowa a ciki sai ’yan aiki.

Daga bisani wani maigadi da fuska a murtuke ya shaida mata cewa gaba daya iyalan marigayin suna Abuja, kuma ba shi da tabbas a kan ko za su dawo Kaduna, kuma yaushe.

Makwabtan marigayin dai sun bayyana kaduwa da samun labarin rasuwarsa, suna cewa sun yi ta yi masa addu’ar neman sauki tun bayan da aka kai shi Legas kusan makwanni uku da suka wuce don a yi masa karin gwaje-gwaje a kuma yi jinyar shi.

Daya daga cikin makwabtan, Sadiq Ibrahim, ya ce marigayin mutumin kirki ne kuma mutuwarsa babbar asara ce ga jihar Kaduna, inda yake zaune da iyalinsa shekara da shekaru.

“Mun yi ta yi masa addu’ar samun sauki, kuma mutane da yawa sun yi farin ciki lokacin da ya fitar da wata sanarwa yana cewa ba ya nuna wasu alamu [na kamuwa da cutar]. Amma sai Allah Ya yi ikonSa. Muna addu’a Allah Ya jikan shi”, inji Sadiq.

Hajiya Asabe Uwa ma a unguwar take kuma a cewarta ta saba da iyalan marigayin, wanda ta ce mutuwarsa ta haifar da wani wawakeken gibi.

“Galibin mutane ba su san [Malam Abba Kyari] ba don haka suke yarda da karairayin da ake yi game da shi a kafofin yada labarai. Magidanci ne mai kauna da kulawa sosai da iyalinsa, kuma yana damuwa da matsalolin jama’a kuma a ko da yaushe yana kokarin taimaka wa mabukata”, inji ta.

A watan Maris ne dai aka tabbatar marigayin, wanda aka binne a makabartar Gudu da ke Abuja, ya kamu da cutar coronavirus jim kadan bayan dawowarsa daga Jamus.