✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gobara ta ci mata da ’ya’yanta hudu a Kebbi

A farkon wannan mako ne wata gobara ta tashi a gidan Malam Umaru Argungu wanda ma’aikaci ne a kamfanin casar shinkafa na WACOT na garin Argungu…

A farkon wannan mako ne wata gobara ta tashi a gidan Malam Umaru Argungu wanda ma’aikaci ne a kamfanin casar shinkafa na WACOT na garin Argungu a Jihar Kebbi. Gobarar ta tashi ne da misalin karfe daya na rana, inda ta lashe rayukan matar gidan da ’ya’yata uku da wata yarinyar makwabtansu.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa matar gidan ta sanya hita ce domin tafasa ruwan zafi, sai ta manta har ruwan ya kone hitar ta kama da wuta daga nan ne sai gidan ya kama da wuta bakin daya. Majiyarmu ta ce a lokacin da jama’a suka fahimci wuta ta tashi a gidan Malam Umaru Argungu kafin a kai musu dauki matar da ’ya’yan nata sun rasu.

Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kebbi, (SEMA), Alhaji Sani Dododo ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, inda ya ce “Wata mata da ’ya’yanta uku sun rasu sanadiyyar tashin gobarar a gidan wani ma’aikacin Kamfanin WACOT da ke garin Argungu.”

Ya ci gaba da cewa wutar ta lashe rayukan matar da ’ya’yanta ne sakamakon sanyar hita a wutar lantarki, sai ta shiga yin wani aiki har ta manta cewa ta sanya hita a wuta. Sakamakon haka gidan ya kama da wuta kuma ya zama sanadiyar rasuwarsu. “Ofishinmu ya kai kayan agajin gaggawa ga ’yan uwan wadanda gobarar ta shafa a garin Argungu,” inji shugaban hukumar.

Ya mika ta’aziyya a madadin Gwamnatin Jihar Kebbi da kuma hukumarsa ga mai gidan da sauran ’yan uwan marigayan. Ya ce “Ku dauki wannan bala’in gobarar a matsayin abin da Allah Ya kawo. Allah Ya gafarta wa wadanda suka rigamu gidan gaskiya.”

Ya yi kira ga jama’ar Jihar Kebbi su rika kashe kaya masu amfani da wutar lantarki a duk lokacin da suka gama amfani da su ko za su shiga wata hidima ta daban.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin mai gidan da abin ya shafa, amma abin ya ci tura. Wata majiya ta ce  a lokacin da mai gidan ya samu labarin abin da ya faru sai ya yanke jiki ya fadi, inda aka dauke shi zuwa asibiti, kuma a cewar majiyar har zuwa lokacin hada wannan rahoto ana ci gaba da duba lafiyarsa.