Search
Subscribe
Yadda gobara ta hallaka matan aure 2 da yara 5 a Katsina

Malam Shu’aibu a bakin gidansa da gobara ta cinye

Yadda gobara ta hallaka matan aure 2 da yara 5 a Katsina

A makon jiya ne wata gobara ta hallaka matan aure biyu, cikinsu har da mai ciki dan wata bakwai a garin Danmusa da ke Jihar Katsina.

Malam Shu’aibu Ahmad, wanda gidansa ne gobarar ta tashi da yammaci ranar, ya shaida wa Aminiya cewa “Mun zo gida Danmusa ne wajen hidimar bikin ’yan uwa tare da matata Maryam Lawal mai shekara 27 da ’ya’yaana biyu, Abdurrahman mai shekara 4 da Muhammad mai shekara 2. Bikin da ba zan manta da shi ba, domin daga murna ne abin ya zame mini bakin cikin da ba zan manta ba. Bayan an gama hidimar biki na koma Abuja, inda nake harkokina, na bar su gida don su kara hutawa tare da gaisawa da sauran ’yan uwa da abokan arziki.

 

Da misalin karfe 2:30 na ranar Asabar din makon jiya, mun yi waya da matata, mun yi hira da ita sosai a cikin raha da nishadi, ta gaya mini cewa suna cikin koshin lafiya, ba su kuma tare da kowace irin matsala. Bayan mun gama wayar ba da jimawa ba, sai na rika jin jikina babu dadi, wani abu haka wanda ban iya tantacewa na damuna amma na gaza gane ko mene ne. Hakan ya faru kafin wancan bakin labari ya riske ni,” inji magidancin.

Ya ci gaba da cewa, “Sai na sake buga wayarta, bayan kamar minti 30 da wadda muka yi. Amma sai na ji shiru babu wayar. Sai na buga ta kanwarta, ita ma shiru. Sai fa damuwar tawa ta karu. Can sai na ga kira daga kawuna cewa maza in dawo gida amma bai gaya mini abin da ya faru ba. Sai na kira wayar wani dan uwa amma sai ya tambaye ni ko na yi waya da matata? Amma muryarsa na rawa. Na ce, eh, kimanin minti 30 da suka wuce amma kuma na sake kira na ji shiru. Nan ne ya shaida mini cewa wuta ta kone gidana. Nan take jikina ya yi sanyi, ban iya yin komai, hatta da makullan motar da ke hannuna na gaza rike su na yi.”

Malam Shu’aibu ya ce wani abokinsa ne ya tuka motar suka je Danmusa. “Lokacin da muka zo na tarar da Maryam da kawarta da yara 5 duk sun rasu sanadiyyar wannan wuta wadda ta tashi da misalin karfe 3:00 na yamma. Babu abin da aka fitar daga cikin gidan, domin duk sun kone a nan Unguwar Kukoki. Sannan babu wanda zai iya cewa ga sanadiyyar wannan wuta. Kamar yadda wadansu ke cewa wai ta faru ne ta murhun iskar Gas Cooker, ni kuma ba na amfani da shi, domin da itace ko risho ake yi mini girki. Labarin da ake bayarwa kan sanadin wutar duk shaci-fadi ne. Allah ne kadai Ya san yadda abin ya faru. Akwai yarana 2 da suka tsira daga wannan wuta,” inji shi.

“Shi Abdurrahman wani dan uwana ya dauke shi zuwa wata makaranta a nan kusa domin ya yi ganawar shiga makarantar. Shi kuma Muhammad yana gidan kakarsa, inda ya je taya ta kwana.”

Aminiya ta gano cewa, Malam Shu’aibu mai shekara 33 ya auri Maryam ce shekara bakwai da suka gabata. Kuma sun haihu sau uku, inda daya ya rasu. Dukkansu suna zaune a Abuja, sai dai zuwa ganin gida, wanda hakan ne ya kawo su a wannan karon tare da halartar biki. Malam Shu’aibu ya bayyana marigayiyar da “Macen kirki mai hali nagari, wadda kowane lokaci take kula da yaranta ta fuskar tarbiyya da iliminsu. Tana yi mini ladabi da biyayya. Mukan zauna mu tsara abubuwa da yawa ta fuskar zamanmu. Gaskiya Maryam…ina cikin jimami matuka har ban san me zan yi ba. Har yanzu ina ganin kamar tana nan raye. Allah Ya jikanta da rahama tare da wadanda suka rasu.”

Kalaman da suka fito daga bakin Malam Shu’aibu ke nan da ke zaune a Unguwar Arewa wajen danginsa a  garin Danmusa, bayan ya gaza komawa Abuja a  yanzu.

Aminiya ta gano, wutar ta tashi a yammacin Asabar ce bayan Maryam ta dawo daga gidan kawarta da suka tashi tare mai suna Jamila, wadda kuma take dauke da cikin wata bakwai.

Mijin Jamila Malam Sama’ila ya ce, “Maryam ta zo gidana wajen matata da suke kawaye tun daga yarinta, ta nemi Jamila ta je gidanta, domin ta taya ta yin kunun aya. Jamila da yaran sun tafi gidanta. Wannan ne kuma ganina na karshe da su.”

Wani mai suna Muhammadu, daya daga cikin wadanda suka kai dauki lokacin da wutar ke ci ya ce, “Hayaki ya turnuke gidan baki dayansa bayan an rufe kofar shiga daga ciki, wanda hakan ya sa muka gaza shiga ciki lokacin da suke kuwwar neman taimako. Mun yi kokarin fasa bango domin isa dakin da suke ciki. Maryam na miko hannu ta taga wadda kofar take rufe don neman ceto amma lokacin da muka isa har Mai ikon komai Ya gama ikonSa. Babu wanda muka samu a raye.”

Kakakin Rundunar’Yan sandan  Jihar Katsina SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce duk da ba a gano abin da ya haddasa gobarar ba, ana zargin an ajiye man fetur ne kusa da wutar da ta haddasa gobarar.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin