Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yadda gobarar tanka ta kashe dan acabar da nake kai – Pamela Mamza

Pamela Mamza

Misis Abohre Pamela Mamza, wadda ta tsallake rijiya da baya lokacin da ake goye da ita a kan babur din da dan acabar da ya dauko ta ya kone kurmus a gobarar tankar man fetur a Unguwar Tumfure a Gombe ta bayyana yadda lamarin ya faru, inda ta ce a idonta dan acabar ya rasu.                                                                                                                                            Pamela Mamza ta ce ta hau babur din dan acabar ne daga shataletalen Daffon Kamfanin NNPC zuwa Tumfure kuma suna tafiya sa ta ji karar tankar mai a bayansu, sai ta ce da dan acabar ya tsaya kuma a kokarin tsayarwar da yake yi ne sai tankar man ta ci karo da wata babbar mota da aka ajiye a gefen hanya su kuma suka bugi bayan tankar suka fadi. Ta ce sai ta tashi da kyar ta fita da gudu, shi kuwa dan acabar ya kasa tashi har wuta ta cinye shi.

“Ku bar ni ba na cikin hankalina,” inji ta, lokacin da manema labarai suke son jin ta bakinta bayan da aka gano ita ce aka goya a babur din da ya kone.

ADVERTISEMENT

Daga baya ta ce, “Da ni ma na mutu ke nan ko? Na gode wa Allah!”

Wani da lamarin ya faru a kan idonsa, Usman Saleh ya ce sashen babbar mota da ke gefen hanya ne ya jawo wannan gobarar da har dan acabar da fasinjar da ya dauko suka fadi, sai Allah Ya kiyaye fasinjar mace  ba ta mutu ba, amma dan acabar ya rasu nan take duk da kokarin ceto shi da suka yi.

ADVERTISEMENT

Sakataren Kungiyar Bada Agajin Gaggawa ta Red Cross ta Jihar Gombe Malam UB Ahmed ya ce yana wani waje aka buga masa waya cewa ana gobara a Tumfure, inda nan take ya kamo hanya ya zo wajen suka ba da tasu gudumawar.

Malam UB Ahmed ya ce  mutum daya suka ciro da suka kai asibiti don likitoci su duba ko ya mutu ko yana da rai domin Red Cross ba ta iya tantance gawa sai likita ne kawai zai gane ya mutu ko bai mutu ba.

Sai dai wannan mutumi da Red Cross suka cire din gawar dan acabar ne da ya kone kurmus tare da babur dinsa, shi kuma direban tankar man ya tsira, amma da aka nemi ganinsa ba gane inda ya shiga ba.

Har zuwa aiko wannan labarin, wakilinmu bai samu jin ta bakin Hukumar Kare Hadura ta Kasa ba wato Road Safety, da Jami’an Kashe Gobara.