Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yadda goyon bayan kungiyoyin kabilu ga Atiku ya jawo cece-ku-ce 

Buhari and Atiku

Ayyana dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a matsayin wanda kungiyoyin kabilu da na shiyya irin su Afenifere da Ohanaeze da ta Dattawan Arewa (NEF) da ta kabilun Tsakiyar Najeriya (MBF) da ta Kudu maso Kudu (PANDEF) cewa shi za su mara wa baya ta jawo cece-ku-ce, bayan da wadansu ’ya’yan kungiyoyin suka ce ba da yawunsu aka yi ba.

Takardar bayan taron da kungiyoyin suka gudanar a Abuja a karshen makon jiya wadda Yinka Odumakin ya karanta dauke da sanya jagororin kungiyoyin da suka hada da Cif Ayo Adebanjo na Afeniferi da Cif Nnia Nwodo na Ohanaezi da Farfesa Ango Abdullahi na NEF da Cif Edwin Clark na PANDEF da kuma Dokta Bitrus Pogu na MBF, ta bukaci ’yan Nijeriya su zabi Jami’iyyar PDP a zaben da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

ADVERTISEMENT

Sai dai tun a watannin baya kan ’ya’yan Kungiyar NEF ya rabu lokacin da Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana goyon bayan kungiyar ga takarar Atiku. Fitattu daga cikin wadanda suka barranta da matsayinsa su ne Alhaji Sani Zangon Daura da Kanar Sodangi da Solomon Dalung da sauransu da dama.

Sannan babbar kungiya al’ummar Arewa ta ACF ta bayyana cewa ba wani dan takara a tsakanin Buhari da Atiku da za ta ce shi mutanen Arewa za su zaba.

ADVERTISEMENT

Takardar bayan taron kungiyoyin kabilun ta ce, “Bayan kammala auna dukan ’yan takarar da suke neman shugabancin kasar nan don ficewa daga cikin matsalolin da take ciki tare da jagorantarta zuwa ga sake fasalinta, sun lura cewa: “Matasa da dama da suka fito takarar Shugaban Kasa sun nuna hobbasa da alkawarin kai kasar nan tudun mun tsira a fannin rayuwa da tattalin arziki. Sai dai akasarinsu a yanzu ba su kama kasa da za su iya samun nasara a zaben Shugaban Najeriya a wannan yanayi ba. Don haka mun amince da dan takarar PDP, Atiku Abubakar a matsayin dan takarar da muka yi muwafaka ya zama Shugaban Kasa saboda ya nuna cikakkiyar fahimta kan muhimman abubuwan da kasa taje bukata a wannan lokaci kuma zai iya kawo mafita a wannan bangare.”

Sauran wadanda suka halarci taron mai taken: “Nemo Gamsasshe, Ingantacce kuma Karbabben Zabe” ya samu halartat Alhaji Tanko Yakasai (Jagoran Kungiyar Northern Leaders and Stakeholders Assembly) da Dokta Junaid Mohammed da Farfesa ABC Nwosu da Sanata Femi Okunrounmu da kuma Alhaji Buba Galadima da sauransu.

Lokacin da yake mayar da jawabi a wata sanarwa Alhaji Atiku Abubakar ya ce, ya zubar da hawayen murna bayan da wadannan kungiyoyi suka bayyana goyon baya gare shi, inda ya ce bayyana goyon bayan babban kalubale ne gare shi.

“Na zubar da hawaye ganin cewa a wannan lokaci da muke fama da rarrabuwar kawuna da yadda ake amfani da cibiyoyin gwamnati don gwara kan mutanenmu suna fada da juna a shekara uku da rabi da suka gabata, shugabanni masu mutunci da ake girmamawa daga sassan kasar nan su yi ittifakin hada kai domin amincewa da takarata a zaben Shugaban Kasa na 16 ga Fabrairu,” inji shi.