✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda guguwa ta yi kisa, ta lalata gidaje 100 a Yobe

Akalla mutum daya ya rasa ransa, wasu 45 kuma sun jikkata sakamakon wata guguwa mai karfi da ta lalata kusan gidaje 100 a jihar Yobe.…

Akalla mutum daya ya rasa ransa, wasu 45 kuma sun jikkata sakamakon wata guguwa mai karfi da ta lalata kusan gidaje 100 a jihar Yobe.

Guguwar wadda ta taso bayan wani ruwan sama mai karfi da almurun ranar Litinin ta kuma barnata mai tarin yawa.

Iftila’in guguwar ya yi barna ne a kananan hukumomin Damaturu, Tarmuwa, da kuma Potiskum a jihar ta Yobe.

Modu Ali, matashin da iftila’in ya yi sanadiyyar rasuwar mahaifinsa dan kimanin shekaru 60 ya ce guguwar ta yaye rufin gidansu gaba daya.

Hakan ta sa ginin ruftawa a kan mahaifin nasa, daga bisani kuma ya ce ga garinku.


Wani shugaban al’umma a yankin Pompomari Sabon Kwalta a Damaturu Bulama Isa, ya shaida wa wakilinmu cewa guguwar ta raba akalla magidanta 20 da muhallansu a yankin.

Isa ya ce iftila’in ya tilasta wa mutanen neman mafaka a gidajen ‘yan uwa da abokan arziki.

Ko da yake ba a kai ga tantance hakikanin yawan gidajen da guguwar ta yi wa barna a wajen babban brinin jihar na Damaturu ba, rahotanni sun tabbatar da cewa mafi yawansu a yankunan Tarmuwa da Potiskum suke.

Wadanda iftila’in ya shafa, wanda yawancinsu talakawa ne sun yi kira ga gwamnati da ta kai musu dauki.

Da yake tsokaci a kan lamarin, gwamnan jihar Mai Mala Buni ya jajanta wa alu’ummar tare umartar Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta jihar da ta kai musu tallafi.

Gwamnan cikin wata sanarwa ta bakin kakakinsa ya umarci a kai duk wadanda suka jikkata asibiti tare da duba girman barnar don gano irin tallafin da suke bukata.

Shugaban hukumar Dr Muhammad Goje ya ce an yi nasarar ceto mutum 45 tare da kai su asibiti.

Ya kara da cewa an kammala tattara bayanai kan mutanen da suke bukatar tallafin gaggawa na abinci, magunguna da kuma matsuguni.