✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda hakar Kuza ya hada kan kabilun Masarautar Godogodo a Kaduna

Yankin Karamar Hukumar Jama’a da ke Kudancin Jihar Kaduna na daya daga cikin yankunan da Allah Ya azurta su da albarkatun ma’adinai da suka hada…

Yankin Karamar Hukumar Jama’a da ke Kudancin Jihar Kaduna na daya daga cikin yankunan da Allah Ya azurta su da albarkatun ma’adinai da suka hada da Kwaranda da Kuza da Tantalaye da Wolfromite da Feldspar da sauransu. Wadannan ma’adinai an kwashe akalla shekara 40 ana hakarsu tare da yin kasuwancinsu a garuruwan Antang da Nisama da Unguwar Mailafiya da Godogodo da Kafanchan da Gidan Waya da Gwal-Kofa (wanda aka ce ya samo sunansa ne daga Gold & Copper) da Dalle da Kariyo da Jagindi da Dangoma da sauran garuruwan da dukkansu ke karkashin Karamar Hukumar Jama’a.

Yayin da Aminiya ta ziyarci Dajin ’Yar Kurciya da ke hanyar Gidan Waya zuwa Godogodo, inda Turawa suka zauna tare da yin gidajensu don dibar Kuza fiye da shekara 40 da ta gabata, kamar yadda wani dillali ya shaida wa wakilinmu, kafin daga baya abin ya ja baya inda suka bar yankin a kwanan nan an sake gano ma’adinin Kuza shake a karkashin kasar yankin.

Yayin da Aminiya ta ziyarci dajin ta zanta da ma’aikatan da suka hada da leburori da dillalai da masu sayar da kayan abinci, inda suka nuna farin cikinsu da samuwar wannan abin alheri da yadda ya taimaka musu wajen samar da hadin kai a tsakanin kabilun yankin da suka hada da Ninzo da Gwandara da Fulani da Numana da Kaninkon da Hausawa, mabiya addinai daban-daban da suka dade ba sa ga maciji da juna a shekarun baya.

Yunusa Yakubu, daya ne daga cikin shugabannin leburori a dajin, ya bayyana wa Aminiya cewa idan ramin Kuza ya yi musu kyau, sukan samu waya ashirin a rami daya, wanda kowane waya ake sayar da shi kan Naira 1,700.

“Mutum biyu ko uku ko fiye da haka ke hada kansu su yi aikin rami, idan ya yi kyau su samu waya 20 zuwa sama, idan bai yi kyau ba kuma su samu waya biyar zuwa bakwai,” inji shi

Yunusa, ya bayyana kadan daga cikin alheran da aikin ma’adinin ya samar a yankin da ya shahara da rikice-rikice a shekarun baya, inda ya ce a yanzu kabilu daban-daban kuma mabiya addinai daban-daban ne kan hadu a rami daya suna aiki tare, babu tsangwamar juna.

“Baya ga babban nasarar da muka samu na hadin kai, akwai kuma ci gaban sababbin gine-gine da sababbin ababen hawa da mutanenmu ke yi albarkacin fara wannan aikin da bai wuce wata uku zuwa hudu ba,” inji shi.

Y bayyana shirin da suke da shi na yi wa kungiyarsu ta leburori rajista domin magance matsalolin da ka iya tasowa na baragurbi ko wani rikici a tsakanin leburori ko tsakaninsu da dillalai ko ’yan fashi da makami domin inganta sana’ar tasu da kuma samun taimako daga karamar hukuma da jiha da kuma tarayya.

Wani lebura, Yahaya Abubakar ya ce a yanzu haka suna kokarin hada kungiya ce don yi mata rajista, inda ya yi kira ga gwamnati ta taimaka musu da injuna, maimakon amfani da karfinsu da suke yi don saukaka musu aikin don ci gaba da dogaro da kansu.

Ya ce da farko sukan yi jinga ne da masu gona. inda sukan ba su gona a kan Naira dubu 10 ko 15 kafin kuma a kira su su fara aikin tono Kuza ta hanyar la’akari da wuraren da za a iya samu.

Da yake yi wa Aminiya karin haske, Shugaban Kungiyar Dillalan Kuza a dajin, Mista Joshua Danladi, ya ce sukan bai wa leburori masu hakar ma’adinin wasu ’yan kudi domin ci gaba da aikin neman Kuza ta hanyar lura da wuraren da Turawa suka yi aiki a baya suka tsaya. A cewarsa, su Turawan bayan sun gama dibar arzikin, sun raina abin da ke wajen daga baya wanda hakan ya sa suka kwashe kayansu suka bar wurin tun da dadewa.

“Sai dai duk da cewa abin bai kai kamar na da yawa ba, amma kuma abin ba zai yanke a wurin ba saboda wajen zamansa ne,” inji shi.

Bayan tono da fitarwa da yin jido da wankewa sannan a ware yashi da laka daga jikin Kuza, sai konawa domin busarwa sannan su tankade, kamar yadda Joshua ya bayyana, sannan sai su auna su saya kafin su kai garin Jos, hedkwatar Jihar Filato don sayarwa bayan su ma sun auna.

LidiYa James, wata mai sayar da abinci a dajin ta shaida wa Aminiya cewa akalla takan yi cinikin Naira dubu takwas zuwa dubu goma a kowace rana idan ma’aikata sun zo da yawa, sabanin cinikin da take yi a gida na Naira dubu biyu zuwa uku kafin fara hakar ma’adinin.

Ta yi kira ga gwamnati ta taimaka wajen bunkasa aikin ta hanyar samar wa ma’aikatan da na’urar da za ta taimaka wajen gano ma’adinin a wuraren kamar yadda ta sani ana amfani da su a baya.

Ta ce, “Idan gwamnati ta taimaka ta taimaki kanta ne ta hanyar karuwar hanyoyin kudin shiga. Ka ga gwamnati za ta samu, leburori da dillalai za su samu, hatta mu masu sayar da abinci za mu samu kudin shiga, ka ga hakan zai taimaka wa matasanmu wajen magance zaman banza da sauransu.”