✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Hawan Daushe ya fama tsohon miki a Kano

A ranar Litinin da ta gabata ce Masarautar Kano ta gabatar da Hawan Daushe a cikin jerin bukukuwan Babbar Sallah da masarautar ta saba shiryawa.…

A ranar Litinin da ta gabata ce Masarautar Kano ta gabatar da Hawan Daushe a cikin jerin bukukuwan Babbar Sallah da masarautar ta saba shiryawa.

Shi dai Hawan Daushen, masarautar tana gudanar da shi ne a washegarin Sallah da yamma inda Sarki da jama’arsa ke fita ta Kofar Arewa ya zagaya ta Unguwar Mandawari da Galadanci da Tudun Wazirci zuwa Unguwar Gwangwazo inda yake kai gaisuwa ga mahaifiyarsa wato Mai Babban Daki kafin ya karasa fadarsa  don karbar gaisuwa daga hakimai da sauran jama’a.

Sai dai wannan hawa ya zama na musamman saboda an kara kawata shi domin tarbar Shugaban Kasar Guinea Conakry Alpha Conde wanda ya zo jihar don yin bikin Salla tare da sauran Musulmin jihar.

Bakon ya zo fadar ce tare da Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje  inda suka zauna a benen Fadar Sarki inda manyan mutane ke zama don kallon yadda abubuwa suke kasancewa.

An fara Hawan Daushen ne bayan Sarki Muhammadu Sanusi II ya fito daga gida ta Kofar Arewa a kan farar taguwarsa inda  ya bi Unguwar Kabara zuwa Asibitin Hasiya Bayero sannan ya karasa gidan mahaifiyarsa. Daga nan sauran hakimansa suka karasa fadarsa da ke Kofar Kudu suka jeru don jiran zuwansa don su kai gaisuwarsu wato abin da ake kira ‘Jahi’.

Bayan da Sarkin ya gama gaisawa da mahaifiyarsa sai ya wuce fadarsa inda isarsa ke da wuya ya sauka daga kan taguwar ya hau farin dokinsa wanda ya sha kwalliya daga nan ya samu wuri daidai kofar fadarsa ya tsaya.

Bayan ya tsaya a wurin ne hakimansa da ’yan kwalkwali da ’yan sulke da ’yan bindinga da sauran mahaya dawaki suka rika kai gaisuwa ga Sarkin.  Haka aka ci gaba da kai gaisuwa har zuwa lokacin da aka kammala hawan.

Aminiya ta kalato cewa duk da irin matakan tsaron da jami’an tsaro suka dauka na samar da tsaro a wurin an samu matasa da suka rika nuna kin amincewarsu ga sababbin masarautun da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro suna daga yatsansu daidaya suna cewa “Sarki daya ne a Kano.”

Hawan Daushen na bana ya fama mikin rashin jituwar da ke tsakanin Sarki da Gwamnan, bayan da wadansu hakimai a Jihar Kano suka sa kafa suka shure umarnin da Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayar cewa kowane hakimi ya zauna ya gudanar da bikin Sallah a sabuwar masarautarsa.

Sanarwar ta Gwamnatin Kano ta fito ne jim kadan bayan gayyatar da Masarautar Kano ta yi wa dukkan hakimai da suke a kananan hukumomi 44 na jihar don halartar Hawan Daushe a Birnin Kano.

Takardar da Kakakin Gwamnan, Abba Anwar ya sanya wa hannu ta bayyana cewa hakiman da suke karkashin Masarautar Kano ne kawai za su halarci hawan a Kano  yayin da sauran hakiman da suka samu kansu a sababbin masarautun hudu da Gwamnan ya kirkiro za su yi nasu hawan a masarautunsu.

Rahotanni sun ce hakimai 11 da bincike ya gano gundumominsu na karkashin sababbin masarautun  ne suka halarci hawan na Kano.

Hakiman sun hada da na Tofa Yusuf Nabahani da Sarkin Ban Kano Hakimin Dambatta Mukhtari Adnan da Dan Ammar Hakimin Doguwa Aliyu Harazumi Umar da Yarima Hakimin Takai Lamido Abubakar da  Dan Isa Kabiru Hashim Hakimin Warawa da Dan Madami Hakimin Kiru Ibrahim Hamza Bayero.

Sauran sun hada da Sarkin Dawaki Mai Tuta Hakimin Gabasawa Bello Abubakar da Dokaji Hakimin Garko Muhammad Aliyu da Makaman Kano Hakimin Wudil Sarki Ibrahim da Sarkin Fulanin Ja’idnawa Hakimin Garun Malam Buhari Muhammad da Barden Kano Hakimin Bichi Idris Bayero.

Duk kokarin Aminiya na jin dalilin da Masarautar Kano ta gayyaci hakiman da ke karkashin sababbin masarautun ya ci tura, saboda wadanda ya kamata su yi magana sun ja bakinsu sun tsuke.

Sai dai wata majiya a Masarautar Kano wadda ta nemi a boye sunanta ta bayyana wa Aminiya cewa, “Masarautar Kano har yanzu tana ganin wadancan hakimai a matsyain hakimanta lura da cewa kotu ta bayar da umarnin cewa ‘a tsaya a matsayin da ake a da’ Ga fahimtar Masarautar Kano dukkan hakiman na masarautarta ce har zuwa lokacin da kotu za ta yanke hukunci.”

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Gwamnan Malam Abba Anwar kan batun ya yi alkawarin zai kira don bayar da matsayin gwamnati a kan bijire wa umarnin nata da hakiman suka yi, sai dai har zuwa lokacin hada wanann rahoto bai kira ba, kuma bai amsa kiran wayarsa da aka yi masa ba.

Amma daga baya gwamnatin ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci yi mata kafar ungulu kan batun na sababbin masarautun ba daga hakiman.