Da Dumi Dumi

Yadda jama’a ke rayuwa a karkashin ’yan bindiga a Katsina

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ’yan bindiga da suke yin fashi da satar shanu da garkuwa da mutane da kuma kisan ba gaira ba dalili. Matsalar ta fi kamarin a yanzu a yankunan kananan hukumomin Jibiya da Batsari da Danmusa da Safana, fiye da kananan hukumomin Kankara, Faskari, Dandume da Sabuwa.

Karamar Hukumar Batsari kuma ta fi sauran fuskantar hare-haren, domin kusan babu ranar da ba za a shiga wani yanki na karamar hukumar a yi barna ba. Hakan ya janyo tayar da wasu kauyukan baki daya har ma suna neman su fara zama kufai, yayin da wadansu kuma ke yin hijira zuwa manyan garuruwa makwabta, zuwa babban birnin jihar.

Wadannan hare-hare da farko an fi kai su kauyukan da ke makwabtaka da Dajin Rugu amma yanzu ya wuce haka. Garuruwa irinsu Mara, Zakka, Ummadau, Wurma, ’Yandaka, Kandawa Shimfida, Zandam da sauransu, suna cikin wadanda suke fuskantar wannan matsala.

A wata majiyar, a yanzu haka al’ummar garin Dankar, Garwa da sauransu duk suna ta hijra zuwa wurare daban-daban.

Alhaji Aminu Lawal Batsari ya yi wa Aminiya karin haske kan yanayin da garuruwan suke ciki inda ya ce:  “A zahirin gaskiya idan ka je wadannan wurare, ka ga halin da jama’ar suke ciki wallahi sai ka zubar da hawaye. Suna fama da karancin abinci, wadansu masu iyawa na baro kauyen su shigo inda suke ganin za su yi bara, domin su samu abinci. Wadansu bisa titi suke kwana domin babu muhalli, sannan babu wani tallafi da suke samu saboda ba su shigo cikin sansanin ’yan gudun hijra ba. Suna yawo ne kawai, duk inda ta fadi a sha.

ADVERTISEMENT

“Sannan hatta al’umma wadanda aka san a da in an samu wata matsala sukan taimaka, a yanzu wannan taimakon ya yi karanci. Batun noma a wajen ma tuni aka fita harkarsa tun farkon faduwar damina saboda wadannan hare-hare. Matasan da suka yi saura babu wata sana’ar yi domin babu jarin. Da ma noma da kiwo ne aka sani babbar sana’ar, to babu abin noman balle dabbobin. Hasali ma, mutum ya tsira da ransa – ga mata nan da kananan yara suna gararamba, wallahi abin sai wanda ya gani,” inji shi

Da ya juya a kan matakin da Gwamnatin Masari ke dauka na kawo karshen al’amarin, ya ce, “Shirin sulhu abu ne na maraba. Sai dai kada a sake yin wani kuskuren kamar yadda aka yi a baya. Kada a bari  wadannan mutane su yi tunanin ko suna da wani karfi ne fiye da gwamnati. Lallai a dauki duk matakin da ya dace.”

Shi kuwa Aminu Sada Dutsinma cewa ya yi tashin hankalin ba ga su wadanda aka kai wa harin ko ’yan gudun hijra yake ba. “Wadanda aka kai wa harin tamkar wadanda tarko ne ya kama, domin za a ce a hannu suke su da masu hijrar amma babbar matsalar da tashin hankalin da rashin sanin halin da ake ciki yana nan ga masu zaman dar-dar na tunanin ko za a kawo musu harin ko a a. Saboda ba su san ta inda abin zai fito musu ba balle silarsa. Kuma tsoron nasu ya shafi har ita gwamnati, domin ana zargin da masaniyarta kuma ta yi shiru. Lallai ne gwamnati ta fito ta nuna babu ruwanta ko sa hannunta a ciki tare da kwararan hujjojin da za su wanke ta a wuraren da abubuwan suka shafa, saboda gurbatattun labaran da ake ta samu,” inji shi.

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya fito fili ya nuna bacin ransa kan yadda wadannan hare-hare suke ta karuwa a jihar, maimakon su yi sauki, kamar yadda suka yi yarjejeniya da sasanci tsakaninsu da maharan da sauran gwamnonin jihohin da abin ya shafa har ma da makwabta.

Gwamna Masari ya nuna haka ne a taron da ya yi da wadansu shugabannin Fulani da ake zargi da kai wadannan hare-hare. Ya ce babu dalilin yin sulhu a tsakanin juna amma sai a bar kai hari wancan sashen a kuma dawo ana kaiwa wannan sashen, bayan kuma duk magana daya ce aka yi da juna kuma aka cimma matsaya.

Gwamnan ya ce yanzu ta fito fili cewa wadannan mahara ba su da amana saboda haka har in ba su bari ba, to gwamnati za ta dauki mataki a kansu a gwamnatance, inda ya ce tuni ya riga ya gama magana da duk wani sashe na tsaro. “Da ma ita wutar fetur in tana ci aka yi amfani da ruwa don kashewa ta ki mutuwa, to sai a yi amfani da sinadari. To muna da sinadarin kuma za mu yi amfani da shi,” inji Gwamna Masari.

Masari wanda ya yi dogon jawabi cikin bacin rai da nuna takaici ga taron shugabannin Fulanin, ya kuma dauki alkawarin shiga cikin dazuzzukan da ake fama da wadannan matsaloli shi da kansa don ganawa da su masu kai harin kai-tsaye ko shugabaninsu, domin samar da sahihiyar hanyar kawo karshen wannan matsala ta rashin tsaron da ta zama tamkar ruwan dare a jihar. Ya ce in hakar ba ta cimma ruwa ba, to gwamnati za ta yi amfani da karfinta don kawo karshen matsalar.

A shekaranjiya Laraba  Gwamna Masari ya fara shiga dajin, kamar yadda ya yi alkawari. Ya faro ziyarar shiga dajin ce daga Kudancin Jihar, inda daga wajen bangaren dajin Birnin Gwari Fulanin da ke kai hare-hare a yanki suka nemi su sasanta da gwamnati; kuma suka yi alkawarin ajiye makamansu, bisa ga rokon gwamnatin da suka yi na ta tsayar da ’yan banga daga kai masu hari.

Share