✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Jami’ar Bayero ta gudanar da Taron Duniya kan Mamman Shata

A wannan mako ne Cibiyar Bincike kan Harsunan Najeriya da Tatsuniyoyi da Fassara ta shirya taro na Duniya a kan marigayi Dokta Mamman Shata Katsina…

A wannan mako ne Cibiyar Bincike kan Harsunan Najeriya da Tatsuniyoyi da Fassara ta shirya taro na Duniya a kan marigayi Dokta Mamman Shata Katsina a duniyar waka.

Taron wanda shi ne irinsa na farko, an yi wuni biyu ana gudanar da shi, inda aka gabatar da makaloli a kan abin da ya shafi nazarin harshen Hausa da kuma al’adun Huasawa.

A jawabin maraba, Shugaban Jami’ar Bayero Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya ce, “Duk da cewa Shata ya yi wa dimbin mutane waka da suka fito daga garuruwa daban-dabam na kasar nan, amma idan za a kirga za a ga cewar Jihar Kano ce za ta zo ta daya. Haka kuma a Jami’ar Bayero aka fara gudanar da bincike a kan rayuwar marigayi mawakin inda Farfesa dandatti Abdulkadir ya gabatar da kundin digirinsa na uku a kan rayuwar Shata.”

Ya kara da cewa jami’ar ta dauki niyyar ganin harshen Hausa ya ci gaba ta hanyar ba wa kowane bangare na koyar da harshen muhimmanci. “Idan aka dauki canja tsarin Cibiyar Nazarin Harshunan Najeriya, inda za ta hada da wasu bangarori na nazartar harshen da suka hada da tatsuniyoyi da fassara mataki ne babba da aka dauka don ganin an yi wa bangaren nazarin harshen kwaskwarima tare da bunkasa shi a jami’ar,” inji shi.

A jawabin, Daraktan Cibiyar Farfesa Aliyu Mu’azu ya bayyana cewa duk da cewa akwai jami’oi da a baya suka yi kokarin shirya makamancin wannan taro, hakarsu ba ta kai ga ruwa ba, hakan bai sa sun ajiye ba,“Duk da cewa muna sane da cewa wasu jami’o’in sun yi kokarin shirya irin wannan taro a kan marigayi Shata, ba tare da cin nasara ba, amma hakan bai sa mun sare ba, inda muka ci gaba da yunkuri wajen ganin tabbatuwar wannan taro wanda kuma Allah Ya taimaka mana muke gabatar da shi a yau. Wannan ba karamin abin alfahari ba ne ga Jami’ar Bayero,” inji shi.

Ya bayyana dalilin zabar Shata da cibiyar ta yi a wannan karon da cewa duk ire-iren tarurrukan da cibiyar kan shirya tana shirawa ne a kan abin da ya shafi kimiyyar harshe, hakan ya sa suka ga dacewar a wannan karon a duba sauran bangarori biyu na nazarin harshen Hausa da suka hada da rubuce-rubucen harshen da kuma al’adunsa.

Daraktan ya kara da cewa duk da irin kalubalen da harshen Hausa ke fuskanta, harshen yana kara samun bunkasa a ciki da wajen jami’a.

“A yanzu haka wannan cibiya ta yi nisa wajen hadin gwiwa da wasu sassan jami’ar don fassara kalmomin da suka shafi darussan da ake koyarwa a sassan. Misali cibiyar ta yi nisa wajen fassara kalmomi a sashen kimiyya musamman bangaren da ya shafi rassan kwayoyin halitta (anatomy), ta kuma fassara kalmomi masu yawa a bangaren shari’a. Kuma cibiyar da hadin gwiwar masana a banagren ilimin koyarwa ta samar da littattafan firamare daga aji daya zuwa aji shida wadanda suka kawo karshen karancin littattafan koyarwa a harshen Hausa,” inji shi.

Yayin gabatar da kasidarsa a kan rayuwar Mamman Shata, Farfesa dandatti Abdulkadir wanda shi ne ya fara rubuta tarihin rayuwar Shata a 1975 kuma ya sami wakilcin Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, Farfesa Mustapha Ahmad Isa ya ce duk da cewa an sha yin rubuce-rubuce a kan rayuwar Mamman Shata da ayyukansa da nasarorin da ya samu, shirya taro na musamman a kan rayuwar mawakin da ake ganin babu kamarsa abu ne da aka dade ana jira,” inji shi.

Da ya tabo tarihin rayuwar marigayin, ya ce “Shata ya fada min cewa ya samu Shata ne a lokacin da yake tallar goro. A wancan lokaci masu sayar da goron suna sayar da shi ne a bisa tsarin kirga, misali wadansu sukan kirga hamsin sai a ce ’yan hamsin da sauransu. Amma shi Shata idan ya zo sayarwawa sai ya rika diba yana cika hannunsa yana sayar wa mutane, “Daga nan sai ake kirana da Shata wato wanda ke sayar da goro ba tare da kirgawa ba,” inji shi.

A cewar Farfesan, marigayi Mamman Shata ya fara harkar waka ne daga wasannin dandali inda ya ci gaba har zuwa kasuwanni da lokutan wasannin al’adun gargajiya, “Kasancewar Shata yana da murya mai dadi sai ya kasance shi yake yin waka a dandalin kasuwa. Hakan ya sa ya zama sanannen mawaki tun yana yaro. A wancan lokacin yana yin wakar ce don nishadi ba don kudi ba. Haka yana yin wasa a duk  lokacin da ake gudanar da wasannin al’ada misali Shadi da Langa da Kokawa da sauransu,” inji shi.

Farfesan ya kara da cewa “Bayan da sunan Shata ya kada, sai mawaka da suke neman kudi da waka suka rika nemansa yana yin waka a madadinsu a duk lokacin bukukuwa. Sai shi ma a hankali marigayi Shata ya bi layinsu inda suke waka suna samun kudi musamman a lokacin da iyayensa suka juya masa baya suna ganin aibin roko inda suka so ya mayar da hankalinsa ga sana’ar da ya gada ta kiwon shanu. Tun yana dan shekara 20 ya fara samun daukaka a harkar waka inda ya zama fitacce a cikin ’yan uwansa mawakan baka, kasancewar babu abin da ba ya yi wa waka daga kan mashahuran mutane da talakawa da sarakuna da malamai da sauransu. Kafin rasuwarsa Shata ya yi wakokin da ba za su kirgu ba.”

A tasa makalar, marubuci Malam Ibrahim Sheme dubi ya yi game da kirarin da Tsangaya wanda aka fi sani da danliti ke yi wa Shata inda ya danganta kirarin da addini Musulunci “Idan an duba ire-iren kirarin da danliti Tsangaya ke yi wa ubangidansa, za ka tarar cewa kusan dukan abin akwai tasirin addini a ciki.”

Shi ma wani malami a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, Dokta Aliyu Ibrahim kankara ya ce adadin wakokin Shata za su kai dubu goma “Shi da kansa Shata ya fada min cewa yana da wakoki dubu takwas. Ya ce yana da kundin waka dubu 200 kuma a cikin kowane kundi akwai waka 40. Ni kuma da na tashi aikina sai na bar lissafin gaba dayan wakokin a dubu goma saboda kowacce waka Shata ya yi to yana yi mata kanwa,” inji shi.

Kuma ya bayyana hatsabibancin da ake fadi cewa Shata yana da shi a matsayin gado daga mahaifinsa, “Duk wani hatsabibanci da ake tunanin Shata yana da shi, to a wurin mahaifinsa ya gada, domin tarihi ya nuna cewa mahaifinsa Ibrahim Yaro ya yi abubuwa na ban mamaki a rayuwarsa. Misali yakan je wuri ba tare da an ga ta inda ya bi ba, haka idan aka ba shi sarar itaciya to sai dai a ga itace yana faduwa daga saman itaciya, da sauran abubuwa na ban mamaki. Don haka idan Shata ya yi wani hatsabibancin, ba abin mamaki ba ne.

Dokta kankara ya yi kira ga mawaka da su yi koyi da halin Shata na kamewa da kuma hakuri, “duk da cewa shi mawaki ne, ba shi da halin maroka, domin shi ba ya zuwa sai an gayyace shi. Haka kuma Bello Katagum ya fada min cewa tunda yake da Shata tsawon shekara 50, bai taba tambayarsa kudi ba. Ko wasa ya je Azare sai ya nade kayansa ya yi tafiyarsa. Idan da mawaka za su dauki halinsa to da roko ya yi daraja.”

Shi ma Magajin Shata, wato daya daga cikin ’ya’yansa, Mansur Mamman Shata ya ce duk da cewa yana yin waka a halin yanzu, amma ya tabbatar ba zai yi kamar mahaifinsa ba, saboda mahifinsa daban ne a cikin mutane “A fannin waka babu abin da za a fadi wanda Shata bai fadi ba, ko ni da nake waka a halin yanzu sai dai in maimaita abin da ya fada, domin yawanci kalmomin da nake amfani da su a waka mahaifina ya riga ya fade su a wakokinsa na baya. Shi mutum ne na daban da Allah Ya yi masa baiwa, wanda har yanzu ba a samu kwatankwacinsa a fagen waka ba,” inji shi.

Mansur Shata ya mika godiya ga Jami’ar Bayero da ta shirya wannan taro don tunawa da rayuwa da ayyukan mahaifinsa.