✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda jerin motoci dauke da kwantainoni suka cushe hanyoyi a Kano

Kimanin motoci 400 wadanda ke dakon kwantainonin kayayyakin ’yan kasuwa ne suka cushe manyan hanyoyin cikin birnin Kano sakamakon rashin samun iznin sauke kaya da…

Kimanin motoci 400 wadanda ke dakon kwantainonin kayayyakin ’yan kasuwa ne suka cushe manyan hanyoyin cikin birnin Kano sakamakon rashin samun iznin sauke kaya da suka hadu da shi daga Kamfanin Inland Containers Nigeria Limited (ICNL).

Motocin wadanda suka kafa layi tun daga kan Titin Zariya zuwa Titin Obasanjo da kuma wani bangare na Titin Audu Bako sun shafe tsawon mako shida ba tare da samun izinin sauke kayan a tashar sauke kaya na kasa da ake kira Kamfanin Inland Containers ba.

Yawancin direbobin motocin da suka dauko kwantainonin sun bayyana rashin jin dadinsu game da halin da suka shiga na rashin sauke kayan inda suka dora alhakin faruwar hakan ga dillalan da suka doro musu kayan wadanda ake kira da “Clearing Agents”

A ranar Litinin da ta gabata direbobin sun gudanar da zanga-zanga kan halin da suke ciki, inda suka ajiye motocinsu a tsakiyar titi tare da daddaga ganye don nuna bakin cikinsu kan halin da suke ciki.

Wani direba da ya yi magana a madadin direbobin, Malam Idi Sa’idu ya ce sun gudanr da zanga-zangar ce saboda ba su da abin kaiwa bakin salati. “A yanzu haka abin da ke damunmu shi ne yankewar kudin abinci a hannunmu sakamakon karin kwanaki da muka yi a nan. Su wadanda suka doro mana kayan mun yi kiran wayoyinsu amma ba su dauka. To hakan ya sa muka yi wannan zanga-zanga domin  jama’a sa san halin da muke ciki su kawo mana dauki. Domin a yanzu mu ba maganar sauke kaya muke yi ba, muna maganar abin da za mu sa a cikinmu. Yau fa mun shafe tsawon mako shida amma har yau ba mu sauke kayan da muka dauko ba,” inji shi.

Aminiya ta so jin ta bakin Shugabannin Kamfanin Inland Containers inda babban manaja a kamfanin ya ce ba ya da abin da zai fada wa ’yan jarida a yanzu.

Sashen Hukumar Kwastam ta kasa mai kula da jihohin Kano da Jigawa kuwa a nasa bangaren ya nanata cewa kayayyakin ba za su shiga kasuwanni a jihar ba har sai an bi ka’ida da dokar kasa duk da matsalolin da hakan ka iya haifarwa ga ci gaban kasuwanci a jihar.

A cewar Muhammad Auwal wanda shi ne Mataimakin Kwanturola mai kula da haraji na Hukumar Kwastam din, hukumar ta yi gargadi kafin ta dauki wannan mataki. “Akwai hanyoyin da ake bi na ka’ida na biyan kudin fito. Ya kamata abin da ka rubuta a takardunka a samu shi ne a cikin kwantainanka. Amma matsalar da muke samu ita ce jama’armu a Kano sai a samu biro a cikin kwantaina misali amma a takarda mutum sai ya ce fensir ne domin ya rage kudin da zai biya. Ka san ana biyan kudin fito ne daidai tsadar kayan da mutum ya shigo da shi. Wannan ba daidai ba ne. Tun cikin watan Disamban bara muka bayar da gargadi a kan hakan,” inji shi.

A bangaren Gwamnatin Jihar Kano ta bakin Kwamishinan Harkokin Kasuwanci na Jihar, Alhaji Ahmed Rabi’u ta bayyana cewa tana bakin kokarinta domin lalubo bakin zaren wannan matsala don ceto harkkokin kasuwanci a jihar. “Muna nan muna tattaunawa da Hukumar Kwastam a kan wannan matsala domin a ga yadda za a warware matsalar ba da dadewa ba. Su ma kansu ejan din da ke fitar da kaya muna tattaunawa da su domin ganin su bi ka’idojin da Hukumar Kwastam ta gindaya ta hanyar biyan kudin fito yadda ya kamata sannan su dauki kaya su kai wa mai shi don a samu warwarewar lamurra.”