✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Jihar Filato ta dauki dumi kan kirkiro sabbin masarautu

Jihar Filato ta dauki dumi tun bayan bayyanar wata wasika mai dauke da sa hannun Kwamishinan Kananan Hukumomi da kuma Masarautun Gargajiya na jihar, Dayyabu…

Jihar Filato ta dauki dumi tun bayan bayyanar wata wasika mai dauke da sa hannun Kwamishinan Kananan Hukumomi da kuma Masarautun Gargajiya na jihar, Dayyabu Garga.

Kwamishinan ya rubuta wannan wasikar ne ga shugaban kananan hukumomin Jos ta Arewa da kuma Riyom don gane da sabbin masarautu da aka kirkiro a kananan hukumominsu.

Kafin wasikar dai, sarautar Atar Aten ta Ganawuri da ke Karamar Hukumar Riyom da kuma Ujah ta Anaguta na karkashin Majalisar Masarautun Gargajiya na Jos ta Arewa.

Idan ba a manta ba a watan Agusta na 2018 Gwamna Lalong na jihar ya daga darajar sarautar Ujah na Anaguta da kuma Atar Aten na Ganawuri zuwa sarauta mai daraja ta daya, al’amarin da ya haifar da cece-kuce tun a lokacin.

Sai dai kura ta lafa sakamakon tunkarar zaben 2019 duk da cewa a watan Nuwamba, 2018 Gwamna Lalong ya mika wa Ujah na Anaguta, Pozo Joro Magaji da Atar Aten na Ganawuri, Yakubu Chaimang satifiket dinsu na tabbacin sun zama masu daraja ta daya.

Abin da ya sa a wannan karon jihar ta dauki dumi shi ne, wannan wasika ta kwamishina ta umarci wadannan sarakuna masu daraja ta daya a Riyom da Jos ta Arewa su kafa ma’aikata da kuma mambobin majalisarsu, inda hakan zai sanya ba za su kasance a karkashin Gbong Gwom Da Jacob Buba ba.

Wasikar ta bayyana cewa umarni ne bisa dogaro da sashi na 91 (1) na Kundin Dokokin Karamar Hukuma dangane da masarautu, musamman ma yadda sashi na 91 (3) ya bayyana cewa masu rike da sarautar gargajiya ne za su zama shugabannin majalisar masarautu a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da kuma Riyom.

Wannan wasika dai ta tayar da jijiyar wuya musamman ma da wadansu suke ganin an daga darajar wadannan masarauta ne don a rage wa Gbong Gwom na Jos, Da Jacob Gyang Buba karfi, inda idan hakan ta tabbata, to Gbong Gwom zai koma karkashin Ujah na Anaguta, musamman idan aka yi la’akari da cewa fadar Gbong Gwom tana cikin garin Jos ne, kuma a Jos ba shi ne babban sarki a Karamar Hukumar Jos ta Arewa ba.

Sai dai Gwamna Lalong ya bayyana cewa an kirkiro masarautun da kuma daga darajarsu wadansu ne don a ba kowace al’umma damar cin gashin kanta bisa yarenta da al’adunta, inda hakan zai zama wani ginshiki na fitar da su daban a duniya.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, inda Aminiya samu kwafi, Gwamna Lalong ya ce, “Idan ba ku manta ba a lokacin da na hau mulki na yi alkawarin zan kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye masarautu, gundumomi da kauyuka, sannan na bayyana cewa zan sake fasalin albashin shugabannin gargajiya, hakan ya sa na nada kwamiti, inda kwamitin ya yi aiki ya kuma ba da rahotonsa,

“Mun yanke hukuncin kirkiro da kuma daga darajar masarautu a jihar ne don kara hada kan mutane a karkashin lemar masarautun gargajiya, sakamakon kuma kiraye-kiraye da mutane suke ta yi a kan masarautun gargajiyar.” Inji Lalong.

Lalong ya bayyana cewa tun a shekarar 2006 aka kirkiro sabbi da daga darajar wadansu masarautun, inda majalisar dokokin jihar suka rattaba wa hannu, ta zauna da kafafunta, “amma gwamnatin da ta gabace mu sai ta yi fatali da dokar, hakan ya sa muka dawo da su.”

Wannan hukunci da gwamna Lalong ya yanke ne ya sanya a yanzu masarautu masu daraja ta daya a jihar suka koma sha hudu daga 12.

Masarautun sun hada da Gbong Gwom a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da Agwom Izere a Karamar Hukuma Jos ta Gabas da Ujah na Anaguta – Karamar Hukumar Jos ta Arewa da Atar Aten na Ganawuri (Riyom) da Long Gamai (Shendam) da Ngolong Ngas (Kanke da Pankshin).

Sauran sun hada da Ponzhi Tarok (Langtang ta Kudu da ta Arewa) da Sarkin Wase (Wase) da Sarkin Kanam (Kanam) da Miskaham Maghabul (Mangu) da Utu Ugo Kiche (Bassa)  da Long Pan – (Kuaan Pan) da Saf Ron Kulera (Bokkos) da kuma Long Tehl (Mikang).

Sai dai a wata tattaunawa da Gbong Gwom Jos, Jacob Gyang Buba ya yi da Aminiya, alamomi sun nuna bai gamsu da abin da Gwamna Lalong ya yi dangane da daga darajar wadansu masarautun ba.

Gbong Gwom wanda kabilar Berom ne ya bayyana cewa daga darajar masarautar Ganawuri da kuma ta Anaguta bai dada shi da kasa ba, abin da kawai ba zai lamunta ba shi ne a sauya fasalin iyakar masarautun da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

Ya ce, “Kara daga darajar wadansu masarautu ba abu ne da ya dada ni da kasa ba, batu na gaskiya shi ne, mutanen Naraguta ba su taba zama a karkashin Berom ba, kamar yadda Berom ma ba su taba yin bauta a karkashin Naraguta ba,

“Haka ma dai mutanen Naraguta ba su taba zama a karkashin Berom ba, kamar yadda kabilar Berom ma ba ta taba zama a karkashin Ganawuri ba, abin da za a fi mayar da hankali shi ne rabe-raben kasa kasancewar Berom da Naraguta suna da hakkin mallakar Jos ta Arewa.” Inji shi.

Gbong Gwom ya ce, tun kafin gwamnatin Jihar Filato – a karkashin jagorancin Lalong – ta kirkiro masarautun, ya rubuta wa gwamna wata wasikar tunatarwa, inda a ciki ya nuna masa aikace-aikacen da kwamitocin shari’a na tuntuba suka yi a shekarar 1994 da 2001 da kuma 2009, inda wadannan kwamiti suka bayyana cewa kabilar Afizere da Anaguta da kuma Berom ne suka mallaki kasar Jos.

Ya ce, “A cikin wasikar na bukaci gwamna ya kafa kwamitin da zai ba masu sarautun gargajiya uku da ke Jos damar su zauna da Hukumar Zana Iyakoki ta Jihar Filato don a fitar da iyakokin wadannan kabilu uku da ke Jos, inda har zuwa yanzu gwamnati ba ta ba ni amsa ba.”

Ya ce, ya so tun kafin gwamna ya kara daga darajar wadansu masarautun a fitar da iyakoki tsakanin wadannan kabilu, amma shiru kamar an aiki bawa garinsu.

Mai sharhi a kan al’amuran da suka shafi masarautu a Jihar Filato, Habila Maimako ya bayyana wa Aminiya cewa, daga darajar wadansu masarautu wani kuduri ne daga gwamna Lalong don ya rage wa Gbon Gwom, Da Jacob karfi, inda yake so ya mayar da shi Gbong Gwom na Berom ba wai Gbng Gwom Jos ba.

Ya ce, “Wannan wani kuduri ne daga Gwamna Lalong don ya rage wa Gbong Gwom, Da Jacob karfi, inda yake so ya mayar da shi Gbong Gwom Berom ba wai Gbong Gwom Jos ba, amma a zahirin gaskiya matsayin Gbong Gwom Jos an riga an sanya shi a doka, kuma babu wani abu da za a yi wajen sauya shi.”

Ya bayyana cewa a da Ujah na Anaguta da kuma Atar Aten na Ganawuri suna karbar umarni daga Gbong Gwom Jos ne, amma “a yanzu su ma sarakuna ne masu daraja ta daya, idan za a aiko wa Gbong Gwom wasika daga gwamnatin jihar kan wani abu, to su ma haka za a aiko musu, maimakon a da idan an aiko masa ne sai ya kira su ya sanar da su.”

Garba Sunday Bunu shi ne Shugaban Kungiyar Kabilar Anaguta mai suna Anaguta Debelopment Association (ADA) a lokacin da ya tattauna da Aminiya ya bayyana cewa abin da doka ta tanadar kuma suka yi amanna da shi, shi ne, “Ujah na Anaguta, Pozo Joro Magaji, shi ne mafi daraja dangane da sarautar gargajiya a Jos ta Arewa da kuma Majalisar Sarautar Gargajiya ta Jos ta Arewa.”

Ya ce, “Ya ji ana ta cece-kuce, amma a zahirin gaskiya babu wanda zai ce su baki ne, kuma su ne da garin Jos, don haka abin da muka yi amanna da shi a nan shi ne, Ujah dinmu shi ne gaba da kowa in dai a Karamar Hukumar Jos ta Arewa yake.

“Masu guna-guni a kan Lalong na yi ne kawai don wata manufa tasu, amma Lalong ya yi amfani da doka ne ba wai don son ransa ba.” Inji shi.

Ibrahim Hassan, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya bayyana cewa abin da Lalong ya yi bai saba doka ko kuma son kai ba, domin “tun a shekarar 2006 tsohon Gwamna Joshua Dariye ya kirkiro wadannan masarautu, amma da Dabid Jang ya zo sai ya yi fatali da su, amma da Lalong ya hau mulki sai ya dawo da wadannan masarautu har ma ya kara daga darajar wadansu kamar yadda ya yi alkawarin yin hakan lokacin da yake kamfe.”

Shina Musa Agada, dan kabilar Anaguta da ke zama a Jos ya ce daga darajar masarautarsu abin murna ne, kuma abin da ya dace a yi ne tun ba yanzu ba.

Ya ce,“Kwamitin tuntuba na mulkin soja, Kanal Joshua Madaki ya tabbatar da sarautar Jos ta Anaguta ce, inda ya bayyana hedikwatar mulki ta kasance a Gundumar Gwong, kuma idan za ka iya tunawa Kotun Koli a shekarar 2009 ta yanke shari’a cewa Gwong ta mutanen Anaguta ce, inda a yanzu Gwong ta zama Jos ta Arewa.”

Sai dai Dung Anthony Pam, wani dan kabilar Berom ya bayyana cewa manufa ta siyasa ce ta sa Lalong ya daga darajar wadansu masarautun.

Ya ce, “Idan za ka duba kananan hukumomin da aka daga darajar masarautunsu, masarautu ne da ba na Berom ba, amma suna cikin yankunan da kabilar Berom suke da yawa,

“kuma ka san Berom ba su zabi Buhari da Lalong ba, to muna tsammanin hakan ya taba shi, kuma ka san an rawaito cewa an taba jefansa a yankunan Berom, don haka ya aikata hakan ne don manufar siyasa, kamar za a iya cewa ramukon gayya na abin da Berom suka masa a zaben 2019.”

A yanzu dai abin da jira a gani shi ne yadda al’amarin zai kasance, kasancewar Gwamna Lalong ya babu gudu ba ja da baya don gane da hukuncin da ya yanke na daga darajar wadansu masarautun jihar.