✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kasashe ke dokoki masu tsauri kan shiga da kwaya

A ranar Talata ce Gwamnatin Saudiyya ta sako Zainab Aliyu wacce aka kama bayan isa kasar don gudanar da aikin Umrah. Jami’an tsaron Saudiyya sun…

A ranar Talata ce Gwamnatin Saudiyya ta sako Zainab Aliyu wacce aka kama bayan isa kasar don gudanar da aikin Umrah.

Jami’an tsaron Saudiyya sun kama Zainab Aliyu kan zargin safarar kwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka ga kwayoyin a wata jaka mai dauke da sunanta.

An sake ta ne dai bayan gano cewa ba ta da laifi.

Kimanin ma’aikatan Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano shida hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya ta kama, wadanda ake zargin cewa su ne suka cusa mata kwayoyi a cikin kayanta.

Kwamandan NDLEA a filin jirgin sama na Aminu Kano, Ambrose Umoro shi ne ya shaida wa BBC cewa wadanda aka kama sun dade suna cutar da jama’a.

Al’amarin dai ya haifar da zanga-zanga a Najeriya domin neman ganin an sako Zainab da Saudiyya ta kama.

Hukumomin Saudiyya dai suna zartar wa wadanda suka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar hukuncin kisa ne.

Akwai kasashe da dama da suke da dokoki masu tsauri kan shigar da kwaya a kasashensu, kuma yawancinsu sun fi fuskantar matsalar fataucin kwayoyi a duniya.

Ga jerin kasashe 10 da dokokinsu ke da tsauri kan kwaya a duniya kamar yadda BBC ta rairayo.

Malaysia

A Malaysia, duk wadanda aka kama suna sayar da miyagun kwaya za a yanke masu hukuncin kisa.

Idan aka samu mutum da kwaya, za a iya cin shi tara ko a daure shi ko kuma a kore shi daga kasar.

China

Idan aka kama ka da kwayoyi a China, za a tilasta maka zuwa cibiyar gyara hali ta gwamnati.

Ana kuma zartar da hukuncin kisa idan aka samu mutum da wasu kwayoyi.

Bietnam

A Bietnam, idan aka kama mutum da kwaya ko kuma hodar iblis da ta kai sama da Fam daya, nan take ake zartar da hukuncin kisa.

Iran

Kamar yadda aka san Iran ba ta wasa da manyan laifuka, haka ma laifukan da suka shafi kwayoyi. Idan aka kama mutum da kwaya a Iran, hukunci mafi sauki shi ne a ci shi tara, mafi tsauri kuma shi ne hukuncin kisa.

Thailand

A Thailand, masu fataucin kwayoyi ana zartar masu da hukuncin kisa ne.

Wadanda ke shan kwayoyi kuma ana zartar masu da hukuncin dauri a gidan yari.

Dubai

A Hadaddiyar Daular Larabawa an tsaurara dokar kwaya inda yawancin kwayoyin da aka halatta sha a duniya, a Dubai an haramta su.

Za a iya yanke wa mutum hukuncin daurin shekaru a gidan yari ko kuma a kore shi daga kasar.

Singapore

’Yan sanda a Singapore za su yi tunanin kana sayar da kwaya ne idan har suka kama ka da ita.

Idan har aka same ka da laifin sayar da kwayoyi, to hukuncin kisa ne zai hau kanka.

Indonesia

Dokar kwaya a Indonesia tana da tsauri. Idan aka kama mutum da wiwi ana iya yanke masa hukuncin dauri na shekara 20 a gidan yari.

Laifuka kan wasu kwayoyin sun shafi daurin shekara 12 a gidan yari.

Sayar da kwayoyi kuma a kasar, ya shafi hukuncin kisa ne.

Koriya ta Arewa

‘Yan kasashen waje ba su cika zuwa Koriya ta Arewa ba, amma akwai masu yawon bude ido da ke zuwa kasar. Sai dai kada mutum ya kuskura ya shiga da kwayoyi a kasar domin za a iya yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Philippines

A Philippines, ana yanke wa masu fataucin miyagun kwayoyi hukuncin kisa ne.