✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kashe Sheikh al-Nimr ta tayar da kura a duniya

A ranar Asabar da ta gabata ce hukumomin Saudiyya suka zartar da hukuncin kisa a kan mutum 47 kan samunsu da aikata ayyukan ta’addanci, cikinsu…

A ranar Asabar da ta gabata ce hukumomin Saudiyya suka zartar da hukuncin kisa a kan mutum 47 kan samunsu da aikata ayyukan ta’addanci, cikinsu har da wani malami dan Shi’a mai suna Sheikh Nimr al-Nimr.
Galibin wadanda aka kashe din Ahlis Sunnah ne da aka same su da hannu a miyagun hare-haren da suka hallaka mutanen kasar da baki a shekarun 2003 da 2004.
Wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Saudiyya ta fitar kuma aka buga a shafin kamfanin dillancin Labaran Gwamnatin kasar (SPA) ta ce mutane 47 din an same su da laifin rungumar muguwar akidar nan ta ‘takfiri’ da shiga ‘kungiyoyin ’yan ta’adda’ da kuma aiwatar da ‘miyagun laifuffuka’ daban-daban. Wannan ne zartar da hukuncin kisa na farko a kasar ta Saudiyya a bana.
Zartar wa Sheikh Nimr hukuncin kisa ya jawo zanga-zanga daga mabiya Shi’a a duniya da kuma wadanda suke adawa da kasar Saudiyya, lamarin da ya jawo kone ofishin Jakandancin Saudiyya a Iran, inda ita kuma ta katse huldar jakadanci da Iran din, sannan wasu kawayenta irin su Sudan da Daular Larabawa da sauransu suka biyo baya, suka yanke huldar jakadancin ko rage jami’an jakadancinsu a Iran din. Dama tun lokacin da aka yanke wa Nimr hukuncin kisa, gwamnatin Shi’a ta kasar Iran ta rika gargadin cewa zartar da hukunci a kan al-Nimr “zai jawo wa Saudiyya babban bala’i.”
Sakamakon yadda kasashen duniya suka yi wa Saudiyya ca, kasar ta nuna rashin jin dadinta kan yadda ake sukarta game da kashe mutum 47 a kasarta, ciki har da Nimr Baker Al Nimr, inda ta ce ta zartar da hukunci ne a kan ’yan ta’adda ba kananan masu aikata miyagun ayyuka ba. Kuma ta ce an kashe su ne saboda gudanar da ayyukan ta’addanci a cikin kasar ba a kan kasancewarsu ’ya’yan wata kungiyar addini ba kamar yadda ake yada jita-jita. Wannan na kunshe ne a wata takardar sanarwar Masarautar Saudiyya da ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Abuja ya aiko wa Aminiya.
Sanarwar ta jero ayyukan ta’addancin da ake zargin mutanen da aikatawa da suka hada da kai hare-haren da suka hallaka mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da lalata dukiya da kai hare-hare tare da hallaka jami’an tsaro, inda aka same su da laifi bayan an gudanar musu da shari’a a gaban kotu cikin adalci kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Wane ne Sheikh Nimr?
An haifi Sheikh Nimr ne a 1959, malamin Shi’a ne da ya fito daga garin al-katif da ke yankin al-Awamiyyah  a Lardin Gabashin Saudiyya.
Ya kasance Shehin Shi’a a al-Awamiyyah tun shekarar 2008 ko kafin haka kadan. Kuma ya kasance limamin Juma’a a garinsu a shekarar 2009 ko kafin haka. Ya yi karatu na shekara 10 a kum da ke kasar Iran kuma ya dan taba karatu a Syria.
Daga farko yana bin Babban Ayatollah Mohammad Hussaini Shirazi  ne amma zuwa shekarar 2008, sai ya koma biyayya ga Babban Ayatollah Mohammad Taki al-Modarresi.
Kuma bayanai sun nuna kafin shekarar 2008, bai tare da kowace daga cikin manyan kungiyoyi biyu na siyasa na ’yan Shi’a da ke Lardin Gabashin Saudiyya wato kungiyar Islahiyyah  (mabiya Shirazis) da Hezbollah Al-Hejaz (Hezbollar Saudiyya).
A watan Fabrairun 2009 an samu matsala a Madina kan wasu bambance-bambancen da ke tsakanin ’yan Shi’a da Ahlis Sunnah a Raudar Annabi (SAW), inda askarawa suka dauki bidiyon mata ’yan Shi’a suna tarzoma a Madina kafin a kame wasu. An kuma kame wasu yara shida a ranakun 4-8 ga Maris kan shiga tarzomar 27 ga Fabrairu a Safwa.
Sheikh Al-Nimr ya caccaki mahukuntan kasar kan matsalar ta auku a Madina a Fabrairu musamman Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, inda ya ce tana danne ’yan Shi’ar Saudiyya.  A wata Huduba da ya gabatar ya ma yi barazanar za su balle daga kasar yana mai cewa: “Ana yi watsi da martabarmu kuma idan ba a dawo mana da ita ba, za mu yi shelar ballewa daga kasar nan… Martabarmu ta fi batun hadin kan ka sar nan.”
Wannan barazana ta sanya aka bayar da sammacin a kamo shi, inda tarzoma ta barke a al-Awamiyyah a ranar 19 ga Maris din 2009. An kama mutum hudu a ciki har da dan uwan al-Nimr mai suna Ali Ahmad al-Farraj mai shekara 16 wanda aka kama a ranar 22 ga Maris.
Daga nan ne ’yan sanda suka fara neman al-Nimr inda suka yi kokarin yin garkuwa da ’ya’yansa. ’Yan sandan sun kuma kafa shingaye a kan hanyoyin shiga al-Awamiyyah kuma zuwa ranar 1 ga Afrilu, 2009 sun kama mutum 35 amma babu al-Nimr a cikinsu.
A ranar 8 ga Yulin shekarar 2012 ne ’yan sanda suka harbi al-Nimr a kafa suka kama shi. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Saudiyya, Mansour al-Turki, ya ce ’yan sanda sun yi kokarin kama al-Nimr da abokansa da suke cikin wata karamar mota, amma sai su al-Nimr suka bude musu wuta da bindigogi, sai ’yan sandan suka mayar da martani, kuma a kokarin su al-Nimr na gujewa ne suka kara motarsu a jikin wata motar ’yan sanda.  Sai dai dan uwansa Mohammed al-Nimr, ya ce an kama Nimr al-Nimr ne “Lokacin da yake dawowa gida a cikin motarsa daga gona a garin al-katif.”
A ranar 19 ga Yulin 2009 iyalan al-Nimr sun ce ya fara yajin cin abinci, kuma lokacin da suka ziyarce shi a ranar 22 ga Yuli sun ce ana musguna masa, domin sun ga alamun an doke shi a kai, kuma yana ci gaba da yajin cin abinci, kuma ya yi yaushi.
Jaridar Saudi Gazzett ta ce Nimr Baker Al-Nimr, wanda shi ne babban mai zuga tayar da kayar baya a Lardin Gabashin Saudiyya ya amince da zarge-zarge 20 da babban mai shigar da kara a kotun manyan laifuffuka ya tuhume su da su, bayan ya ja daga a zaman kotun 17 da aka fara a watan Mayu na 2014, zaman da lauyoyi da ’yan uwansa maza suke halarta. Ya rika kiran alkalan kotun da azzalumai, kuma bai yarda da halaccin kotun ba.
An zargi Nimr da boye ’yan Shi’ar da suka yi ta’asa da ake nema tare da zuga mutanen Saudiyya su yi tawaye wa sarakuna da shugabannin kasar. Sannan an tuhume shi da yawan ganawa da mutum 23 daga cikin mutanen da ake nema kan aikata ta’addanci a lokuta da dama bayan sallolin Juma’a. Sai kuma haddasa tarzomar addini a tsakanin ‘’yan Shi’a da Ahlis Sunnah a katif da kuma zanga-zangar da ta gudana a makabartar Baki’a da ke Madina.