✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Kasuwar ’Yan kwallo ta Janairu ke ci

A ci gaba da cinikin ’yan wasan kwallon kafa da ka bude a wannan wata, kungiyoyin kwallon kafa na ci gaba da fafutikar saye ko karbar…

A ci gaba da cinikin ’yan wasan kwallon kafa da ka bude a wannan wata, kungiyoyin kwallon kafa na ci gaba da fafutikar saye ko karbar aron ’yan  wasa don cike gurabunsu ko gyara a kungiyoyinsu.

Akwai ’yan wasan da suke neman tafiya wasu kungiyoyi saboda rashin buga wasa a inda suke, akwai wadanda saboda kwarewarsu, wasu kungiyoyi ke nemansu, wanda hakan ya sa suke tsada. Sai kuma wadanda kungiyoyinsu ke neman tura su aro a wasu kungiyoyin domin su kara gogewa.

Aminiya ta rairayo manyan ’yan wasa biyar da aka kammala cininkinsu ko ake neman gamawa a wannan Janairu, kamar haka:

Bruno Fernandes: (Dala miliyan 85)

Kusan an fi maganar Fernandes a duk lokacin da ake maganar saye da sayar da ’yan wasa. Shi dai Fernandez dan wasan kasar Portugal ne da Sporting Lisbon, kuma kwararren dan wasan tsakiya ne da duniyar wasa ke yayi.

Manchester United ce ke kan gaba wajen nemansa, kuma kimarsa ta kai Dala miliyan 85.

Dayot Upamecano: Fam miliyan 68

A ci gaba da kokarin gyara da sabon kocin Arsenal, Mikel Arteta ke yi, kocin yana kokarin sayo dan wasan kungiyar Leipzig na Jamus, Dayot Upamecano a kan Fam miliyan 50. Dan wasan wanda dan kasar Faransa ne, yana cikin masu tsaron gidan kungiyar ta Leipzi da yanzu haka take nuna bajinta a Gasar Bundesliga ta Jamus.

Moussa Dembele: Fam miliyan 40

Moussa Dembele dan wasan gaban Lyon yana cikin matasan ’yan kwallo da taruraronsa ke haskakawa. Ya fara tashe ne a Kungiyar Celtic kafin ya koma Lyon ta Faransa. Yanzu haka Kungiyar Chelsea na nemansa don maye gurbin Olibier Giroud, haka Arsenal da Manchester United na nemansa.

Wilfred Zaha: Fam miliyan 75

Dan wasan gaba na Kungiyar Crystal Palace ana kimanta shi kan Fam miliyan 75, kuma Arsenal da Chelsea ne ke kan gaba wajen neman dan wasan.

Christian Eriksen: Fam miliyan 15

Wani dan wasa da ke tashe shi ne Eriksen, wanda ya nuna a fili cewa yana so ya bar kungiyar Tottenham ta Ingila. Ana kimanta dan wasan a kan Fam miliyan 15, duk da cewa ana tunanin ya yi sauki ne kasancewar saura watanni kadan kwantiraginsa na Tottenham ta kare, dan wasan tsakiya ne da ya kware sosai.

Wadansu ’yan wasan da sauyin zai amfana akwai dan Najeriya Bictor Moses da ya amince zai koma Inter Milan, inda zai sake haduwa da kocin da ya daga shi a Chelsea, Antinio Conte.

Sai kuma Gareth Bale da ya bayyana cewa zai hakura ya zauna a Real Madrid har zuwa karshen kwantiraginsa.