Daily Trust Aminiya - Yadda Kiristoci Hausawa suka gudanar da bikin Kirsimetin ban
Subscribe

Yadda aka gudanar da kasar shan lemu a Unguwar Shuxi, Bakori, Jihar Katsina

Yadda Kiristoci Hausawa suka gudanar da bikin Kirsimetin bana

A makon jiya ne mabiya addinin Kirista suka gudanar da bikin Kirsimeti a fadin duniya, inda Kiristoci Hausawa ma ba a bar su a baya ba, wajen bi sahun ’yan uwansu a sassan duniya wajen gudanar da bikin na Kirsimeti.

Bikin Kirsimetin na bana ya gudana a tsakanin Musulmi da Kiristoci a Jihar Kano, inda suka hadu suka gudanar da bikin cikin farin ciki, lamarin da zai yi wuya ga wanda ya kai ziyara cikinsu ya tantance bambancin da ke tsakanin mabiya addinan biyu.

A Jihar Kano addinin Kirista yana da mabiya masu yawa a kananan hukumomin Garun Malam da Rano da Tudun Wada da Sumaila da Gwarzo da Karaye.

A cikin al’ummomin da ke Garun Malam da Rano, an gudanar da bikin Kirsimeti cikin farin ciki, inda Musulmi da Kiristocin yankin suka gudanar da bikin murnar haihuwar Annabi Isa (AS) a tare.

Wani Musulmi da ake kira Sarkin Kidan Garin Madobi, Malam Umar Chiroma ya nishadantar da Kiristoci a Cocin Nasarawa Baptist a Chiromawa a ranar Kirsimetin.

Wani Kirista mai suna Malam Sabo Jatau, wanda mamba ne a Cocin Nasarawa Baptist ya bayyana cewa yana da tabbacin kasar nan za ta zauna lafiya idan har za a lura da abin da ya faru a baya na cewa ita kasar na da addinai daban-daban.

A cewar Jatau, “Mu a nan ba mu bambancewa a tsakanin bikin Kirsimeti da na Sallah domin muna gudanar da dukkansu. Muna yin abubuwanmu tare da Musulmi idan abin farin ciki ya faru mukan yi murna tare haka ma akasin hakan. Idan suna gudanar da aurensu a masallaci ko gida muna yi tare da su haka, mu ma idan muna yin namu auren ko bikin binne gawa. Kun shaida a yanzu yadda muke bikin tare idan kun duba akwai Musulmi masu yawa a nan wurin (coci) suna taya mu murna. A gaskiya muna zaune lafiya da juna muna kuma mutunta junanmu.”

Wani Shugaban Kiristoci, Malam Garba Waisu ya bayyana cewa kyakkyawar alakar da ke tsakanin Musulmi da Kirista a yankin ta dade kwarai da gaske, “Ko a yau din nan sai da Shugaban Karamar Hukumar Garun Malam ya kira ni ta waya yana taya ni murnar wannan rana ta Kirsimeti. Don haka muna da kyakkyawar alaka a tsakaninmu,” inji shi.

Malam Hassan mai kimanin shekara 75 yana daya daga cikin mutanen da suka rage, wadanda suka karbi addinin Kiristanci a yankin tun shekara 50 da suka gabata. Ya tabo irin tashi-fadin da aka yi wajen gina cocin Nasarawa a farkon lokacin da addinin Kirista ya shigo garin Chiromawa. Ya yi kira ga Kiristoci su yi koyi da Ananbi Isa (AS) ta hanyar ci gaba da zama da junansu lafiya da kuma son makwabtansu.

A garin Kaltungo a Jihar Gombe Kiristoci sun gudanar da bikin Kirsimeti tare da ’yan uwansu Musulmi kamar yadda ya zama al’adar mutanen yankin, inda za ka samu ’yan uwa ciki daya suna bin addinai daban da na juna.

Wakilinmu da ya ziyarci garin ranar Kirsimeti bayan an kammala ibada a coci masu bautar sun koma gida domin su yi nishadi tare da ’yan uwansu Musulmi da Kiristoci.

Da yammacin ranar Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad ya yi bikin Hawan Daba da sauran al’adun mutanen garin, inda suka bi sawun ’yan uwansu Kiristoci don yin bikin na Kirsimeti.

Mai Kaltungo ya gudanar da bikin wanda ya samu halartar Kiristoci da Musulmi masu yawa.

A lokacin da aka gudanar da hudubar Kirsimeti a Cocin ECWA a garin Gombe, Fasto Rolines Buba ’Yangari ya bayyana ranar ta Kirsimeti a matsayin ranar mayar da hankali wajen bautar Allah.

Fasto ’Yangari ya yi kira ga Kiristoci su kwaikwayi irin rayuwar Yesu, ta hanyar nuna soyayya da kirki tare da rarraba kyaututtuka ga mutanen da ke tare da su.

Ya bayyana cewa akwai bukatar masu bin addinin Kirista su dauki dabi’ar ziyartar ’yan uwansu, musamman a lokacin wannan biki.

Haka kuma Rabaran Apollos Hassan na Cocin ECWA Gospel a kan Titin Ashaka ya shawarci Kiristoci su dauki dabi’ar bayarwa da kuma nuna kauna ga juna.Ya nemi Kiristoci su rika yi wa shugabanni addu’a don Allah Ya ba su basira da ilimin tafiyar da mulki kamar yadda Allah Yake so.

Haka  Kiristocin da ke Katsina sun gudanar da bikin Kirsimetin cikin kwanciyar hankali da lumana. Kiristocin da ke Kafur da Malumfashi da Bakori sun gudanar da bikin Kirsimetin cikin jin dadi da nishadi.

Rabaran Ajasi Ayhu na Cocin ECWA a Funtuwa ya ce yawancin Kiristocin yankin manoma ne haka kuma ana gudanar da bikin na Kirsimeti a lokacin kaka, don haka abu ne mai wuya su shiga yanayin rashin kudi a daidai lokacin bikin. “Yawanci muna tara kudi tun kafin lokacin Kirsimeti, wanda muke amfani da shi wajen sayen shanun da muke yankawa don yin abincin Kirsimeti,” inji shi.

Rabaran Ayhu ya ce akwai kyakkyawar alaka a tsakaninsu da abokan zamansu Musulmi, musamman mutanen da ke da ’yan uwa na jini a cikin Musulmi.

Yayin da Aminiya ta ziyarci kananan hukumomin Kafur da Bakori ta ga yadda mata da matasa ke tafiya Unguwar Shudi a cikin garin Bakori. A cewar mazauna yankin bisa al’adar al’ummar yankin a ranar Kirsimeti mutane suna taruwa don yin wasanni iri-iri tare da nishadantar da bakinsu.

Faston Cocin ECWA, Unguwar Shudi, Ishaya Markus ya ce wannan al’ada ta dauki tsawon shekara 20 ana gudanar da ita.

Yawanci mata da matasa a yankin suna gayyato abokansu don su zo su taya su murna. An tanadi abinci da abin sha sun wadata a wannan rana. Ya kuma yaba wa al’ummar Musulmin yankin saboda yadda suke amsa gayyatar ’yan uwansu Kiristoci.

Wani Bafulatani mai suna Muhammad Sani ya ce suna da bambancin addini ne kawai amma suna zaune lafiya da juna. “Rugarmu tana kusa da wannan unguwa ta Shudi, yawancin mutanen da ke wannan wurin Fulani ne, amma muna zaune lafiya da juna shekaru masu yawa. Idan lokacin bikin Sallarmu ko bikin aure ko na suna suka zo, suna halarta muna gudanar da abubuwanmu tare; shi ya sa za ku ga alakarmu tana da karfi sosai,” inji shi.

A Jihar Jigawa, ana fara shiryen-shiryen bikin Kirsimeti ne kwana biyu kafn lokacin. Sauran abin da ya rage na shirye-shiryen ne ake karasawa a ranar Kirsimeti. Akan gama dafa abinci da misalin karfe 10:00 na safe inda ake rarraba shi ga ’yan uwa da abokan arziki.

Garuruwan Roni da Kazaure su ne ke da mafi yawan Kitistoci a Jihar Jigawa. A cewar wani mabiyin addinin Kirista mai suna Haruna Adamu, yawanci sukan gama dafuwar abincin ne da misalin karfe 8:00 na safe saboda bisa al’ada ana daukar abincin zuwa coci, inda ake rarraba shi ga sauran masu ibada da masu gadi.

A cewarsa, akan gudanar da bikin na Kirsimeti bayan an dawo daga ibada, inda mutane ke gudanar da shagulgula iri-iri da suka hada da gasar wasannin motsa jiki da raye-raye da wake-wake.

Wata mata mai suna Binta Fasli, ta ce a lokacin da Mishan ke cikin garin Roni, ana gudanar da bikin Kirsimeti ta hanyar yanka shanu da kuma rabar da taimakon marayu da sauran mabukata.

Shugaban Kingiyar Kiristoci ta Kasa reshen Jihar Jigawa Bishop Markus Yohanna Danbinta, ya ce ana ci gaba da gudanar da bikin Kirsimeti har zuwa sabuwar shekara ta hanyar haddar Littafin Baibul. Haka kuma ana gudanar da gasar wasannin motsa jiki da raye-raye da wake-wake.

texem
More Stories