✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kiwon kifi ya kawo cikas ga noman albasa a Jigawa

Manoman albasa a Jihar Jigawa sun fuskanci cikas a bara sakamakon karancin irin shuka da kuma ciwon da yanayi ya haifar ga irin albasar. Irin…

Manoman albasa a Jihar Jigawa sun fuskanci cikas a bara sakamakon karancin irin shuka da kuma ciwon da yanayi ya haifar ga irin albasar.

Irin albasar ya yi karanci ne bayan da masu kiwon Kifi suka gano muhimmmancinsa inda suke sayensa suna bai wa kifaye a matsayin abinci.

Wannan yanayi da aka fuskanta ne ya jawo karancin irin, kuma  wadanda suka yi sa’ar samun irin da wuri wani ciwo da ya bayyana ya jawo sun yi asararsa.

Kimanin kashi 40 zuwa 50 cikin 100 na manoma a Karamar Hukumar Birnin Kudu da suka tsunduma harkar rainon irin albasa inda ciwon ya lalatar musu da shi.

Manoman da asarar ta shafa su ne wadanda suka fara rainon irin a tsakanin watan Agustan bara, inda mafi yawancin irin albasar da suke rainon ya rika narkewa saboda maiko ko damshin da kasar take da shi a daidai wancan lokaci. Kadan daga cikin manoman ne suka tsallake wannan annoba bayan sun gano sirrin sanya tafarnuwa a gonakin.

An ce zuba tafarnuwa a gonakin nasu ya taimaka gaya wajen rage maikon da gonakin ke da shi inda hakan ya taimaki wadansu daga cikinsu suka tsallake. Duk da haka wadansu kuma sun cire amfanin nasu ne da wuri saboda tsoron gudun asara lokacin albasar ba ta gama kosawa ba.

Bisa ga wannan yanayi ya sa manoman da ke da ilimin nomanta suka yi jinkirin rainon nasu irin albasar har zuwa watan Janairun bana, bayan albasar lokacin damina da ta lokacin sanyi ta kare.

Bayan wannan yanayi da aka fuskanta na masu kiwon kifi da rashin yanayi mai kyau da ya jawo karancinta farashin albasar ya ninka har sau biyu.

Wadansu manoma da suka fito don neman irin daga yankunan karkara ba su samu ba, sai da suka je makwabciyar Jihar  Kano sannan suka samu.

Da yake zantawa da wakilinmu, daya daga cikin dillalan irin albasa, Malam Haladu Yusuf, kokawa ya yi kan yadda masu kiwon kifi suke bai wa kifayen albasa a matsayin abinci.  Ya ce, ba wani abu ba ne ya jawo  karancin albasar sai yadda irin albasar yake neman maye abincin kifi wanda hakan ya jawo manoman albasa shiga cikin mawuyacin hali.

“Batun gaskiya shi ne manoman kifin ba suna sayen ’ya’yan albasar da yawa ba ne a duk shekarar ne suke nema shi ya sa irin yake tsada,” inji shi.

Malam Haladu Yusuf, ya kara da cewa a lokacin da ake dashen irin albasar rige-rige ake yi a tsakanin manoma da masu kiwon kifi, shi ya sa a wasu lokutan manoman suke shan wahalar samun irin inda ake samu irin kuma yana da tsada.

A cewar Malam Haladu Yusuf, kafin su samu irin albasar yanzu sai sun shiga Jihar Kano, nan ma suna sayensa da tsada.

Ya ce saboda karancinsa da suke fuskanta ya sa a kwanakin baya suna sayen mudu daya a kan Naira 800 ne, amma a yanzu Naira 3000 suke sayensa.

Ya ce ba kudin ne damuwarsu ba, koda mutum yana da kudin sayen sai ya bi ta hannun wani kafin ya iya samu. Ya ce hanya mafi sauki ta noman albasa shi ne mutum ya raini irin sannan daga baya idan ya tsira ya cire ya dasa shi amma a bana rashin kyan yanayi ya jawo musu koma baya.

Haladu ya ce yawan gonakin da ake rainon irin albasar duk sun narke sun lalace idan aka shiga gonakin kamar ba a taba dasa komai a ciki ba, sai ’yan kadan ne suka tsira nan ma sun cire albasar ne da wuri ba tare da ta kai lokacin da ya kamata ta kai na kwana 120 kafin a cire ta ba.

Ya ce cire ta da wurin a wajen manoma shi ne ya fi domin da zarar mutum ya nemi barin ta ta wuce lokacin zai girbi asara.

“ Masu kiwon kifi sun taimaka wajen lalacewar nomanmu, domin sun dogara ne gaba daya a kan irin albasar don ta zama abincin kifi,” inji shi.

Ya ce “Rashin yanayi mai kyau ma bai taimaka ba duk da kasancewar manoman albasar kadan sun ajiye irin, hakan bai sa an samu an yi rainon irin da kyau ba saboda gonakin sun narke.”

Haladu ya ce kadan daga cikin manoman ne Allah Ya taimaka suka tsira daga wannan bala’in ta wajen  sanya tafarnuwa a gonakin duk da wadansu manoman sun cire albasar ce ba tare da ta kosa ba.