✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Kwastam suka haddasa hadarin da ya kashe wakilin Aminiya Bashir Liman da mutum hudu

A’lummar garin Ningi da ke Jihar Bauchi sun zargi jami’an Hukumar Kwastam da ke kan hanyar Babaldu zuwa Kano da cewa su ne suka jawo…

A’lummar garin Ningi da ke Jihar Bauchi sun zargi jami’an Hukumar Kwastam da ke kan hanyar Babaldu zuwa Kano da cewa su ne suka jawo hadarin da ya janyo rasuwar wakilin Jaridar Aminiya Bashir Musa Liman da wadansu mutum hudu a kan hanyarsa zuwa wajen iyayennsa da ke Jama’are a Jihar Bauchi  a ranar jajibarin Babbar Sallah.

Sai dai Hukumar Kwatsam din ta musanta zargin, inda ta ce a bincikenta hadarin ya auku ne sakamakon gudun wuce kima da tukin ganganci daga direban da jami’anta suke bi wanda shi ne ya janyo hadarin.

A bayanan da suka yi wa wakilinmu, mutane da dama a garin Ningi sun ce ranar da wannan tsautsayi ya faru, wadansu jami’an Hukumar Kwastam  da ke Babaldu a Jihar Jigawa ne suka biyo wani direba da ke dauke da shinkafa ’yar kasar waje, suna bin sa yana sheka gudu har zuwa Ningi sai suka harbi tayar motarsa sakamakon harbin tayar motar da suka yi ne sai kan motar ya juya ya doki motar da Bashir Liman ke ciki, daga baya kuma wata mota kirar Starket ta zo ta doki motar sai kuma wasu motocin biyu suka doki motar shinkafar, inda a wajen mutum biyar suka rasu.

’Yan sandan da ke aiki a hanyar ce suka kwashi wadanda suka yi hadarin suka kai su Asibitin Ningi, kuma lokacin da jami’an Kwastam din suka ga cewa hadarin ya faru sai suka juya da gudu suka koma, har mutane sun yi yunkurin a tare su sai suka yi harbi a sama, wanda hakan ya sa suka samu sukunin tserewa.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, Kamal Datti Abubakar, kan lamarin ya ce zai bincika kuma duk bayanin da ya samu zai bayar, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai yi bayanin ba.

Wani dan sanda a Ningi ya shaida wa Aminiya cewa ba laifi ba ne jami’an Hukumar Kwastam su harbi tayar wanda suke bi in sun biyo wanda suke zargi mai amma ya ki tsayawa, sannan duk abin da ya faru direban ne da laifi, kuma Kwastam din ne suka biyo motar a wannan ranar da abin ya faru inda motoci biyar suka kara da juna a wurin da hadarin ya auku.

Kakakin Hukumar Kwastam da ke kula da Shiyya ta Hudu (Zone D) Suleiman Isah a wata sanarwa da ya fitar bayan wakilinmu ya tuntube shi, ya ce hukumar ba ta da hannu a abin da ake zarginta na cewa ita ce ta janyo hadarin.

A cewarsa, “Hukumar ta ji wani sako da ba na gaskiya ba da wani mutumin Ningi ya sanya a shafinsa na Instagram a Intanet inda ya ce jami’an Hukumar Kwastam ne suka janyo hadarin bayan sun biyo wani direba da ke dauke da buhuhunan shinkafa wanda shi ne sanadiyyar hadarin da ya janyo rasuwar mutane da dama.”

Ya ce wannan labari karya ne tsagwaronsa amma a matsayin Hukumar Kwastam tana isar da ta’ziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu kuma suna addu’ar Allah Ya sanya su a Aljanna.

Ya ce ba wani jami’in hukumar da ya yi aiki a wannan hanya, “Bayan karanta wannan sako da mutumin Ningi ya sa a Intanet sai muka shiga bincike don gano abin da ya faru, kuma da yawa daga cikin mutanen da abin ya faru a  kanidonsu ba su danganta Hukumar Kwastam  ko jami’anta da hannu kan faruwar lamarin ba, tunda ba su yi aiki kan hanyar a wannan rana ba. Dukkan mutanen da suka yi mana bayani sun danganta abin da gudun wuce kima da tukin ganganci da yunkurin wuce wanda yake gaba,  kuma bincike ya nuna cewa daya daga cikin motocin da suka yi hadarin tana dauke da buhunan shinkafa  shi ya sa wadansu suke zaton ko Hukumar Kwastam ne ta janyo hadarin.”

Ya ce yana shawartar duk mai son tabbatar da gaskiyar abin da ya faru ya tuntubi hukumomin da suka dace ciki har da rundunar ’yan sanda.