Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Yadda Limamin Ilori ya jagoranci Sallar Idi daga gida

Babban Limamin Ilori, Dokta Muahammad Bashir Imam-Soliu, lokacin da yake gabatar da hudubar Idi

Yadda Limamin Ilori ya jagoranci Sallar Idi daga gida

Ranar juma’a Babban Limamin Ilori, Dokta Muahammad Bashir Imam-Soliu, ya jagoranci raka’a biyu ta Sallar Idin Layya ta bana daga gida.

Da karfe 9.30 na safe daidai Babban Limamin ya tayar da sallar, wadda aka yada a gidan Rediyon Jihar Kwara – a zangon AM da FM – da gidan rediyon Sobi FM, da kuma gidan rediyon Harmony FM.

Jim kadan bayan idar da sallar ne Dokta Soliu ya yanka ragonsa, kamar yadda addinin Musulunci ya karantar.

Da jin wannan yanka da ya yi ne kuma al’ummar yankin suka bi sahu suka yi nasu yankan.

Ranar Litinin ne dai Kwamitin Yaki da Cutar COVID-19, wanda ke karkashin jagorancin Mataimakin Gwamman Jihar, Mista Kayode Alabi, ya soke dukkan wasu bukukuwan Sallah ciki har da sallatar raka’a biyu a Babban Masallacin Idi na birnin Ilori.

Don haka ne Sarkin Ilori kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya umarci al’ummar Masarautarsa da su bibiyi sallar a gidajen rediyo su kuma saurari yankan da Babban Limamin ya yi domin su samu damar koyi.

Wasu jihohin Najeriya dai sun soke bukukuwan Sallah amma sun kyale Musulmi su yi sallar Idi a masallatan Juma’a, da sharadin kiyaye dokokin hana yaduwar coronavirus.