✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda magidanci ya yi yunkurin kashe ‘yarsa a Yola

Wani magidanci ya yi yunkurin kashe ‘yarsa mai shekaru 10 inda ya yanke ta a wuya a yunkurinsa na yi mata yankan rago lamarin da…

Wani magidanci ya yi yunkurin kashe ‘yarsa mai shekaru 10 inda ya yanke ta a wuya a yunkurinsa na yi mata yankan rago lamarin da ya abku a yankin Damare inji uku a Karamar Hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa. 

Malam Ibrahim Abubakar Dan jarida ne da ke zaune a Yola ya shaida wa Aminiya cewa, a binciken da ‘yan sandan suka yi wa magidancin mai suna Sa’idu Dan Iya, ko kadan bai nuna nadamar a aika-aikar da ya yi ba, majiyar ta ce mutumin ya dade yana yi wa mahaifiyar yarinyar barazanar kisa.

A cewar mahaifiyar yarinyar malama Fadimatu ta fita aiki ta bar yarinyar mai suna Zahra tare da mahaifinta, “Ina wajen aikin ne makwabta suka rugo suka shaida min halin da Zahra ke cikin, inda ya yi mata mummunar yanka a wuya kamar yadda kuke gani.” In ji ta.

A halin yanzu likitoci na kokarin ceton ran Zahra a cibiyar kula da lafiya ta FMC da ke Yola, inda za a yi mata aikin tiyata a yau alhamis.

Majiyar ta ce, mahaifiyar yarinyar ita ce me kula da iyalin inda take yin aikatau take samun dan abin kula da iyalin.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin wanda ya abku a Lungung Maman manaja da ke Karamar hukumar Yola ta Kudu jihar Adamawa.