✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mahaukacin kare ya ci naman Musulmi a Afirka ta Tsakiya

Wani mutum da ke yi wa kansa lakabi da mahaukacin kare “Mad dog,” ya bayyana cewa yana cin naman Musulmi don daukar fansa, kan kisan…

Mad dog (Mahaukacin kare) mai cin naman MusulmiWani mutum da ke yi wa kansa lakabi da mahaukacin kare “Mad dog,” ya bayyana cewa yana cin naman Musulmi don daukar fansa, kan kisan gillar da suka yi wa matarsa mai ciki a kasar Afirka ta Tsakiya.
Mutumin mai suna Ouandja Magloire, yana daga cikin ’yan dabar Kiristoci da ke kai wa Musulmi hari, a babban birnin kasar Afirka ta Tsakiya, Bangui.
Kafar Labarai ta BBC, ta ruwaito yadda Maglore ya hango wani da tsautsayi ya auka masa, nan take ya bi shi. Kuma yana da mabiya, matasa 20 da ke amfani da karfinsu, wajen tursasa direba ya fito daga motarsa. Sai ’yan dabar su fito da mutum, su yi masa dukan siya, su sassare shi, kafin daga bisani su kona shi da wuta.
Wani hoton bidiyo, ya nuna yadda Maglore ke cin naman kafar mutum. Ya ce daukar fansa yake yi a kan Musulmi da suka kashe masa matarsa mai juna biyu da surukarsa da jaririnsu.
Mutane da dama sun ga wannan hoton bidiyo, amma babu wnad aya yi kokarin ceton wanda aka yi nufin halakawa.
“daya daga cikin mutanen, ya kama kafadar mutumin, sannan ya je, ya sawo bureoi, ya fara cin naman, tare da burodin,” a cewar wani da al’amarin ya auku a gabansa, mai suna Jean-Sylbestre Tchya. “Yanayin abin da ya auku ya sanya mutane da dama sun yi amai, wasu ma har kuka suka yi saboda muni da tashin hankalin wannan al’amari,” inji shi.
Michel Djotodia, Musulmin farko da ya fara mulkin wannan kasa, wadda al’ummar Kiristoci suka fi yawa, ya sauka daga mukaminsa ne, bayan da aka zargi mutanensa, ’yan tawayen Seleka da kai wa kiristoci fararen hula hari, har ta kai ga an kafa kungiyar kariyar kai, mai lakabin garkuwar –balaka “anti-balaka.”