✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mai gidan burodi ya jefa almajiri a magasar burodi

Ana tuhumar wani mai gidan burodi da abokan aikinsa da ke garin Bajoga a Karamar Hukumar Bajoga a Jihar Gombe kan zargin jefa wani almajiri…

Ana tuhumar wani mai gidan burodi da abokan aikinsa da ke garin Bajoga a Karamar Hukumar Bajoga a Jihar Gombe kan zargin jefa wani almajiri a magasar burodi inda suka kona kafafuwansa. Mai gidan burodin mai suna Abubakar Ibrahim da abokan aikinsa sun jefa almajiri dan shekara 14 mai suna Nafi’u Umar, dan asalin garin Kayarda da ke Tafawa Balewa a Jihar Bauchi a magasar burodin ne saboda zarginsa da sace burodin Naira 100.

Da yake zantawa da Aminiya a gadonsa na Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe, Nafi’u Umar ya ce sun je daji ne da ’yan uwansa sai suka bi ta wani gidan borodi domin su sha ruwa. Sai Manajan gidan da wadansu mutum biyu suka ce sun sace musu burodi, ya ce su caje su.

Yaron ya ce ba su ne suka dauki borodin ba, ashe ya fadi ne a kasa. Duk da haka sai Manajan ya ce su je su kira malaminsu.

Nafi’u ya ce ya gaya wa mai gidan burodin cewa malaminsu ba ya nan, ya shiga gari. Shi ne sai Manajan ya sallami sauran yaran, shi kuma suka kama shi da karfi suka tura shi a cikin dakin da suke gasa burodin.

Ya ce da suka ciro shi da farko sai suka ga babu abin da ya same shi, don haka sai suka sake mayar da shi. Da suka fito da shi a karo na biyu kuma sai suka doke shi da itace, suka kuma kwada masa karfe, bayan ya kone a kafafunsa.

Nafi’u ya kara da cewa su uku ne suka doke shi, bayan da suka ga ya kone ne sai suka fara yi masa magani a asibiti da bai yi ba sai wani ya ce su fara na gargajiya saboda kunar wuta sai da itatuwan gargajiya.

Da Aminiya ta tuntubi mahaifin yaron mai suna Malam Umar Adamu dangane da al’amarin, ya danganta al’amari da kaddara.

Malam Umar ya ce lokacin da ya ji labarin abin da ya samu dansa, kawai sai ya dauka kaddara ce. Ya ce domin ko a wajensa yake hakan zai iya faruwa da shi, “Don haka ban dauki  matakin komai ba,” inji shi.

Mahaifin ya ce Nafi’u ne dansa na 20 da ya haifa kuma ba shi kadai yake almajiranci ba, akwai yayyensa, Salisu da Harisu da Musthapha, wadanda yanzu haka sun gama almajiranci sun koma gida Tafawa Balewa.

Ya ce yana sa ’ya’yansa a almajiranci ne “Domin wanda ya yi karatun almajiranci ko kira’arsa ta fi ta wanda bai yi almajiranci ba. Hakan ta sa nake alfahari da ’ya’yana su yi almajiranci, domin ni ma na yi wannan almajiranci a tsangayar Dokoro a yankin Dukku,” inji shi.

“Abin da ya sa na kai ’ya’yana almajiranci wajen wannan malami, shi ne saboda dan uwana ne, kakarsa ma ’yar uwata ce; yana zaman kane ne a wajena,” inji shi.

Malam Umar, ya kara da cewa, idan Nafi’u ya samu sauki zai mayar da shi gida Tafawa Balewa, ya sanya shi a makarantar boko, ya ci gaba da karatunsa a gida, tun da karatun ya yi masa nauyi, har yanzu bai je ko’ina ba.

Ita kuwa mahaifiyar Nafi’u, mai suna Malama Maryam Umar, ba kamar mahafin ba; cewa ta yi ba za ta lamunci danta ya koma almajiranci ba.

Kamar yadda ta bayyana wa wakilinmu, ta ce “Ba zan so dana ya koma almajiranci ba.”

Ta ce a lokacin da aka bugo musu waya aka shaida musu halin da ya shiga, sai da ta yi kusan suma. “Na fadi ina ta kuka, sai da maigidana ya rarrashe ni. Cikin dare kuma na tashi na yi ta nafilfili, na yi ta rokon Allah, sannan na samu sauki,” inji shi.

Malama Maryam ta ce danta Nafi’u shi ne na biyar da ta haifa. Za ta so kuma idan Allah Ya ba shi lafiya, a mayar mata da danta gida. “Yayansa ma da yake karatun allon, shi ma zan sanya a mayar mini da shi, domin almajiranci ba abin yi ba ne. Sai dai idan mijina ya fi karfina a kai, domin kada a samu matsala,” inji ta.

Daga nan sai ta shawarci iyaye kan cewa su daina kai ’ya’yansu almajiranci, musamman bisa la’akari da yadda ake azabtar da su, ake daukar su marasa galihu, bayan kuma almajirai ma ’ya’ya ne kamar kowa.

Da wakilinmu ya tuntubi Kungiyar  mai Kare Hakkin Jama’a ta  CLO, shugabanta a Gombe, Muhammad Aliyu Wayas, wanda ke cikin wadanda suka tsaya wajen kwato hakkin wannan almajiri da aka azabtar, kuma aka ki kula da shi fiye da wata guda; ya ce ba za su bari ba dole doka ta yi aiki a kan wanda ake zargfin.

Ya koka matuka kan yadda maigidan burodi da abokan aikinsa suka azabtar da almajirin, ta hanyar kona shi a gidan gasa burodi.

Muhammad Wayas ya ce sun je har gidan yari, inda ake tsare da Abubakar Ibrahim maigidan burodin, inda aka ce  wai yana da tabin hankali, inda da wannan dalili ne aka sake shi da farko.

Ya ce sun gano cewa lafiyarsa lau, sai dai ya aikata abin ya dawo yake nadama.

Aminiya ta gano cewa wanda ake  zargin, wato Abubakar Ibrahim, yana hidimar kasa ne, bayan da ya kammala karatun digiri a harshen Hausa a Jami’ar Bayero, Kano. An zargin shi da wani mai suna Yerima Adamu da wani karamin yaro (an sakaye sunansa) da ake tsare da shi a gidan kangararrun yara na Gombe ne suka kona Nafi’u a magasar burodi.

Aminiya ta gano da farko an saki maigidan burodin bayan da aka kama shi, amma shigowar Kungiyar CLO cikin maganar ya sa aka tada zancen, har aka gurfanar da su a gaban Kotun Majistare ta Biyu da ke garin Bajoga, inda aka tura su gidan yari, kuma za a ci gaba da shari’ar a ranar 23 ga Janairun nan.

Da wakilinmu ya tuntubi Kwamishinar Ma’aikatar Mata ta Jihar Gombe, Misis Na’omi Joel Awak, don jin matakin da za su dauka, sai ta nemi wakilin namu ya jira ta. Bayan kamar sa’a daya da rabi yana jira, ta fito ta ce ba za ta samu ganinsa ba, tana da aiki a cikin gari, sai dai ya sake jiranta har sai ta je ta kammala ta dawo.

A bangaren ’yan sanda kuwa, Mukaddashin Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, ASP Yusuf Balami, ya ce rahoton da sashin Hausa na rediyon BBC Hausa ya bayar kan labarin a ranar 9 ga Janairu ne, ya ja hankalinsu, inda suka sa aka kama wadanda ake zargi da laifin, wadanda tuni aka gurfanar da su a gaban Kotun Majistare ta Biyu da ke garin Bajoga kuma yanzu haka yaron yana Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya, ana yi masa jinya.

Sannan ya  ce rundunar na ci gaba da bincike don gano masu yada jita-jitar karya kan lamarin, inda suke yada karyar cewa ’yan sanda sun yi wa mai laifin takardar shaida cewa yana da tabin kwakwalwa.