Search
Subscribe
Yadda makaho, kurma, mai kafa daya ke rayuwa a Sakkwato

Aminu Abubakar

Yadda makaho, kurma, mai kafa daya ke rayuwa a Sakkwato

Rayuwar Aminu Abubakar Alaburwa mai shekara 49 makaho ne kuma kurma mai kafa daya da ke Sakkwato fadar Jihar Sakkwato. Rayuwarsa akwai abin koyi da ban tausayi. A duk safiya yakan fito wajen gidansu ya zauna ya yi bara, idan dare ya yi ya koma gida rike da sandarsa shi kadai idan bai samu jagora ba.

Wakilinmu ya tsaya gabansa bai san ya zo ba ya yi magana bai ji ba, ga shi kuma an guntule masa kafa daya.

Malam Aminu ya rasa jinsa da ganinsa da kafarsa ta dama a mabambanta lokuta a rayuwarsa.

Shi ne da na farko a wajen mahaifiyarsa, na biyu a wajen mahaifinsa, kuma ya zama kurma ne bayan wata biyu da haihuwarsa, ba tare da wani ciwo ba, inda kakarsa ta gano ba ya ji bayan ta fahimci cewa duk wani sauti ba ya ji.

Yayan Aminu, mai suna Lawali Abubakar ya bayyana dan uwansa da mutum mai saukin rayuwa kamar yadda yake tunawa a lokacin suna kanana suna zuwa makarantar Islamiya tare. “Kurma ne a lokacin amma yana motsa bakinsa yana karatun Kur’ani kamar yadda ya ga yara na yi.”

Yana da shekara 10 da haihuwa ne babur ya buge shi, inda kafafuwansa biyu suka karye abin da ya kai ga yanke kafarsa ta dama, kuma ya yi jinya a gida ta shekara biyar.

Yanayin da yake ciki bai hana Aminu ya nemi na kansa ba, ta hanyar yin kananan sana’o’i har da bude karamin shago a kan titin Marafa Danbaba kusa ga gidansu a Unguwar Rungumi a birnin Sakkwato.

Bayan ’yan shekaru ne ya canja kasuwanci ya rika barin gari yana zuwa Maiduguri zuwa kasar Chadi don yin saye da sayar da bandar kifi.

A 1997 ya hadu da ciwon ido wanda ya zama sanadiyar makancewarsa, a nan ne ya dawo gida ya zauna. Yau shekararsa 22 da ciwon makanta.

Lawali ya ce sun yi kokarin nema masa magani, amma ba su samu nasara ba.

Cikin tafiye-tafiyen da ya yi ya auri mace daya lokacin yana da shekara 34 duk da aurensu bai dade ba ya mutu.

Wani makwabcinsu, mai suna Kabiru Aliyu ya tabbatar da abin da Lawali ya fadi, inda ya ce idan Aminu ya samu matsala a kan hanya lokacin da yake tafiya, wansa Lawali kadai ke iya yi masa jagora.

Lawali ya ce duk kokarin da ya kamata su yi na ganin an sanya dan uwan nasu a cikin wadanda gwamnatin Sakkwato ke tallafa mawa da Naira 6,500 duk wata ga masu lalura abin ya faskara.

“Mun je mun samu masu aikin don a sanya sunansa amma ba mu yi nasara ba har muka watsar da lamarin gaba daya,” inji shi.

Ahmad, wani malami ne a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari ya ce Aminu zai iya karatu ya samu ilimi matukar aka hada shi da kwararru. “Lamarin Aminu ba sabon ba ne amma kwararru na iya samar masa da hanyar samun ilimi, ya kamata ya yi amfani da basirarsa ba wai ya tsaya yana bara ba.”

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin