✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda makahon farfesa ya ci gasar motar Naira miliyan 9

Farfesa Jibrin Isa Diso wanda muka bayar da labarinsa kwanakin baya cewa shi ne farfesa makaho na farko a Arewa, ya samu kyautar mota Jihar…

Farfesa Jibrin Isa Diso wanda muka bayar da labarinsa kwanakin baya cewa shi ne farfesa makaho na farko a Arewa, ya samu kyautar mota Jihar Delta. Farfesa Jibrin Diso ya yi wa Aminiya karin haske game da yadda ya samu nasarar cin gasar motar wacce ya bayyana a matsayin rabo daga Allah.

Farfesa Diso ya bayyana cewa ya samu nasarar gasar motar ce dalilin wani taro da ya halarat a Jihar Delta inda ya ce, “Tun farko wata kungiya ce wacc ake kira FAN ta gayyace ni wani taro kan tsara tattalin arzikin kasa wanda kungiyar ta yi hadin gwiwa da Hukumar Bayar da Tallafi ga Kasashe ta Birtaniya (DFID) kuma aka gudanar da taron a Jihar Delta. Bayan an kammala taron na wuni uku sai aka dauke mu domin mu zaga gari don ganin abubuwan da jihar ke da su. A wannan tafiyar ce muka je wani gari da ake kira Inewih, a nan ne muka je wani kamfani da ake hada mota. Bayan mun yi yawo a cikin kamfanin sai shi mai kamfain da ake kira Mista Innocent ya bayar da mota guda daya amma tunda muna da yawa sai ya bayar da shawara a yi kuri’a wanda ya samu nasara sai ya dauki motar.”

Farfesa Diso ya kara da cewa, “Bayan da muka dawo cikin garin Warri ne sai aka yi kuri’a, aka dunkule takardu aka sa mai ‘yes’ guda daya. To sai kowa ya dauka da kowa ya dauka ni kuma ina budewa sai aka ga ‘yes; a jikin tawa. Kin ji yadda aka yi na yi nasarar samun wannan mota kirar SUB IBM wacce aka ce kudinta ya kai Naira miliyan takwas da dubu 800.”

Farfesan ya ce, “Ban yi tsammanin zan samu wannan mota ba kasancewar muna da yawa. Mun kai mu 700. Amma da yake rabo ne daga Allah sai ga shi na samu. Koda yake tun farko na dayanta Allah, na san Shi Mai yin abin da Ya so ne.”

Farfesan ya mika godiya ga Allah inda ya ce, “Ina gode ga Allah (SWT) domin Shi Ya kadarta zan samu wannan mota. Haka kuma ina godiya ga wanda ya ba ni motar. Haka su ma ’yan uwana mahalarta taron. Kin ga duk da muna da yawa a wurin amma lokacin da aka bayyana cewa ni na  lashe gasar, dukkan wadanda muke tare da su a wurin sai suka hau murna da ihu suna cewa Farfesa. Kuma ba su nuna min kabilanci na yare ko addini ba. Wallahi sun taya ni murna kwarai da gaske. Ina mika godiyata gare su. Allah Ya saka wa kowa da alheri.”

A cewar Farfesan yanzu haka yana shirye-shiryen ganawa da Gwamann Jihar Kano don ya nuna masa motar tare da rokon gwamnati ta duba yiyuwar ba wa wancan kamfani izinin bude reshe a Jihar Kano don bunkasar arzikin al’ummar jihar da kasa baki daya.